← Book details Yaa Sheikh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 12

Sashe 10

Yaa Sheikh Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abby yace "Ina amsawa, Ya shirye shiryen tafiyan naka? Gobe ne koh?"

Kai ya gyad'a, Abby ya masa Addu'a sosai sannan suka cigaba da hira. Sai bayan la'asar yaje yad'anyi siyaiya ya dawo. A daran ya shiga Yama Mamy sallama ya fito dan da asubah zai bar gida. Addua tamai sosai sannan ya fito.

Da Asubah ana fitowa a masallaci Abby yakaisa Airport da rakiyan su AbdulMalik. K'arfe Shidda jirginsu ya d'aga zuwa k'asar saudi Arabia.

K'arfe Sha biyu na dare wanda a k'asar Nigeria yake goma na dare ya sauka a Prince Muhammad bin Abdulaziz Airport dake Madina.

Taxi ya nema yahau zuwa masaukin shi........

Long lasting friendship, my in low. Ummy Abdul 😍khairaty ✍🏻
[7/4, 7:50 AM] ‪+234 903 274 9200‬: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
*Yaa Sheikh*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*U. K. Y. For Real*😍

*Dedicated to Mmn Khairy*🤝🏻

*76 to 80*

Ikon Allah ne kawai ya kaisa gida, yana parking aka soma kiran Sallan Magrib, yana fitowa ya shiga gida. Ummy dasu Abdulmajid yasamu a tsakar gida suna Alwala.

Da d'an sakin fuska ya k'arasa cikin gidan, Ummy ta d'ago da fara'a tana cewa

"Sannu da zuwa Abdallah"

Da murmushi ya amsa, su Abdulmajid suma suka masa Sannu da zuwa sannan suka fita dan zuwa masallaci. Bokiti ya d'auka ya d'ebi ruwa ya shiga wanka, dan yanda Jiddah ta rud'asa dazu yasa dole yayi wanka.

A gurguje ya gama ya fito ya sauya kaya ya nufi masallaci. Ana idarwa ya dawo gida, D'akin Ummy ya shiga da Sallama ya zauna tare da fad'in

"Wash!"

Ummy tad'an kallesa cike da kulawa

"Yaya dai? Ya kasamu 'Yar tawa"

Da wani k'ayataccen Murmushi jin ta ambato Masoyiyar tasa yace

"Tana nan Lafiya lau Ummy, kinga kuwa yanda ta k'ara natsuwa"

Ummy tayi dariya tana girgiza kai. Mik'ewa tayi ta d'auko mai abincinsa ta aje tana cewa

"Nasan kanajin Yunwa"

Yayi saurin Jan Food flask din ya bude ya soma ci yana lumshe ido, Hira ya soma mata kamar bashi bah duk hiran rabi na Jiddah neh.

Kallansa kawai take cikin ranta ko kawai mamaki me na ganin yadda yaa Sheikh yake kokarin maida kansa wawa.

"Alhandulilahi ala kulli halin, wannan abuncin naki da dad'i yake Ummi ta"yafad'a yana aje Food flask d'in a gefe.

Murmushi ummy tayi, suka cigaba da hira.

AbdulMalik da AbdulMajid ne suka shigo a tare da sallama, Ummy da Yaa Sheikh suka amsa masu suka zazzauna tareda musu sannu. AbdulMalik yace

"Ya Abdallah Ya Jiddo nasan tana nan tana cigaba da rashin ji da lalaci kamar yanda aka saba to wai yanzu ma wa zataiwa wannan shagwa'bar tatane? "
Ya k'arasa maganar suna kwashewa da dariya shida Abdul majid.

Yaa Sheikh yabud'e baki neman zaiyi magana abbulmajid ya karb'e

"Kai kake tunanin wannan ma kamata yayi ka tambaya acen wane yake dafa mata indomei mai yaji , yarinya sai kafurin kwadayi wai ita bazataci tuwo ba, hala madai ba a yin tuwo a makarantar nasu"

Ya maida dubansa ga Ya Abdallah

"Ya Abdallah Halan An baka Complain d'inta a makarantar? "

Kasa magana Abdallah yayi saboda takaici, so dayawa su Abdulmajid na shirmansu da Jiddah na tsokana amma bai
Taba jin haushi kamar nayau bah, mik'ewa yayi fuskansa ba walwala yace

"Ummy barin shiga wajan Mamy"

"Ka gaisheta" cewar Ummy

Toh kawai yace yasa takalmansa ya fita. Da sallama ya shiga gidan Mamy, kan sallaya ya sameta tana lazumi, zama yayi kusa da ita harta gama sannan ta juyo garesa

"Aa An dawo ne baba na"

Duk'ar dakai yayi k'asa tare da gaisheta, ta amsa fuska a sake tare da tambayansa ya hanya, ya amsa da lafiya lau. Shiru ne ya biyo baya chan tace

"Ya Jiddan? Nasan tana nan tana abinda ta saba musamman da yanzu babu mai saka mata ido"

"Aa Mamy! Jiddah yanzu ta chanza ba yanda kika santa bah, tayi Hankali sosai"

"Kaiya Babana, nasan fa halin Jiddah"

Yayi saurin kauda zanchan da cewa

"Mamy Addu'a kawai zaki cigaba da mata, Allah ya bata sa'a a karatunta"

Ta sauke ajiyar zuciya tace

"Addu'a kullum ina muku ba ita kad'ai ba, Allah ya shiryeku gaba d'aya ya shige muku gaba a duk alamuran ku"

"Ameen Mamy mun gode"

*****

Da kuka ta k'arasa gurin Nana ta zauna tana cigaba da sharan hawaye

"Ke wai yaneh haka mene kike ma mutane kuka? "

Tad'an d'ago kanta chab'e chab'e da hawaye

"Yaa Abdallah neh! Ni gida nakeso na koma"

Nana taja dogon tsaki tare da tureta

"Nifah na tsani Yaa Sayyadi yake ko Yaaa Sheikh? Ban gane wannan bibiyan da yake miki bah faa"

Jiddah ta sake d'ago jajayen idanunta tace

"Duk cikin yayye na babu mai sona kamarshi ya Abdallah yana matuk'ar sona koda nake da k'arancin shekaru Nasan da haka ya Abdallah bai barni nayi kukan maraici ba, kuma kema shaida ce tunda gashi kina gani inayin makaranta mai kyau kamar yadda kema me uba araye kikeyi"

Nana ta dungureta tana turo baki

"Dallah chan kedai banza ce, wani so bayan ko 'yar tsarabar d'an makaranta bai miki bah"

Maganganun Nana ne ya soma bata haushi ta d'ago tana goge hawayen fuskanta

"Ke tsaraban yan makaranta ya dama"

Ta fita ta barta nan baki bud'e cike da Mamakin yau ita Jiddah ke yab'ama magana.

Class ta koma gaba d'aya jikinta a sanyaye saboda kewar gida, ko inda Nana take bata kalla bah har aka tashi, sai da yamma sannan ta samu ta amso kayan da Yaa Abdallah ya kawo mata. Ba kunya Nana ta matso tana duba ledojin

"Haba k'awaliya romon kaza, ai nidake ba haka. Me Yaa Sheikh din ya kawo mana neh"

Jiddah dai batace mata komai bah dan Ciwon Maranta ne taji yana neman tashin mata. Tana kallo Nana ta jida abinda takeso tayi tafiyarta tana zagin Yaa Abdallah.

Bayan sun koma hostel ne Mara yace Bismillah, kuka kawai Jiddah take tana juye juye rik'e da maranta, Gaba d'aya d'akin ya rude, d'aya daga Cikin Mummys d'in makarantan neh ta shigo, da taimakonta Jiddah ta mik'e sai yarfe hannu take tana kuka tare da turo baki gefe guda kuma tana kiran Mamy da Ummy.

Clinic suka wuce dan Kallo d'aya ta mata ta gane abinda ke damunta.

A firgice ya farka tare da dafe k'irjinshi yana kiran sunan Allah, Idanunsa ne suka ciko da kwalla murya a raunane yace

"Allah kasa Mafarkin nan ba gaskiya baneh, Allah kasa Jiddah tah na cikin koshin Lafiya"

Ya sake dafe kirjinshi sbda yanda zuciyarsa ke bugawa da sauri. Ba shiri ya fashe da kuka duk da taurin zuciya irin ta maza, kuka yake yana dafe da kirjinsa yana karanto duk addu'ar datazo bakinsa.

Ummy Abdul/
khairaty ✍🏻
[7/4, 9:12 AM] ‪+234 903 274 9200‬: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
*Yaa Sheikh*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*U. K. Y. For Real*😍

*Dedicated to Mmn Khairy*🤝🏻

*81 to 85*

Ganin kukan bazai fisheshi ba yasa ya mik'e ya saka jallabiya ya fito, Alwala yayi ya koma d'aki ya tada sallah, bai zauna ba saida yaji kiraye kirayen Sallahn Asubah.

Mik'ewa yayi dak'yar sbda yanda kansa ke masa wani irin mugun ciwo, D'akinsu Abdulmajid ya buga kamar yanda ya saba duk Asubah idan yaba gida. Yana tashin su ya wuce Masallaci.

Bashi ya shigo gidan ba sai karfe goma na safe, cikin gida ya shiga ya samu Ummy tana gyaran kayan miya, har k'asa ya tsugunna yace

"Ina kwana Ummy"

Ta d'ago suka had'a ido, ganin yanayin Idanunsa yasa ta juyo garesa dakyau tana cewa

"Lafiya Lau Abdallah, meya sameka naga idanunka haka?"

Yad'an dukar dakai k'asa yace

"Kaina ke ciwo tun jiya amma nasha magani"

"Allah ya baka Lafiya, tashi ka shiga ciki abin karinka na nan, nima sauri nake na gama Aiki dan Abby na hanya yau"

Murya a raunane yace

"Eh munyi waya jiya, Allah ya kawosa Lafiya"

Ta amsa da "Ameen"

Ya mik'e yace

"Ummy barin d'an watsa ruwa na kwanta tukun zanci abincin Anjima"

"Toh" tace dan bataso ta tsawaita magana saboda yanda ta lura da yanayinsa.

*******

Da kuka suka isa Clinic, sun samu Nurse mai Night Duty ta amshi Jiddah, kuka kawai take harda majina. Mummyn tace

"Kedai Wannan yarinya da shagwab'a kike, kiyi shiru mana ai girma ne ya sameki"

Cikin kuka ta turo baki tace

"Wallahi banasan girman na yafe"

Ta k'are maganan da sakin wani sabon kukan tana rik'e da Maran. Abu taji na gangaro mata daga k'asanta tasa hannu ganin jini yasa ta saki k'ara da karfi ta soma tsalle

"Wayyo Allah na shiga uku Jini na fitomin a gabana, na shiga uku Mamy zan mutu"

Nurse d'in ta daka mata tsawa

"Dallah yima mutane shiru"

Nan da nan ta shanye kukan ganin ba wasa a idon Nurse d'in gata K'atuwa bak'akirin da ita.

Allurah ta zuk'a a syringe Jiddah na ganin haka ta soma aniyan arcewa Mummy ta dank'ota, Nurse d'in ta mata alluran ta saki k'ara tana kuka sosai.

Nurse din ce ta d'auko Pad da sabon Pant ta nuna mata yanda ake anfani dashi sannan tace ta shiga Toilet tayi wanka sai tasa. Ba musu ta shiga dan mugun tsoron Nurse din takeji yanzu. Tana shiga Nurse din tace Mummy ta samo mata wasu kaya ta chanza, ba musu ta koma Hostel dinsu.

Nana ta samu ta zafga tagumi, ta tambayeta inda kayan Jiddan suke ta nuna mata, kaya ta d'aukan mata ta fita, koda ta koma har ta gama wankan kayan kawai take jira.

Cikin minti kad'an ta kimtsa amma har lokacin bata daina hawaye da turo baki bah. Drip nurse din tasa mata bayan ansha artabu da ita. Nan ta kwana juye juye tana kuka sai gaf da asubah ta samu Ya saketa sannan ta samu bacci.

K'arfe Sha biyu da rabi Yaa Sheikh ya farka da Addu'an tashi daga bacci, Hiransu Abdulmajid da Abby yaji Hakan ya tabbatar masa da ya dawo.

Da sauri ya mik'e dan ciwon kan ya sakesa yanzu sai jikinsa daba k'wari, A tsakar gida ya samesu suna shan iska ya k'arasa ya zauna kan tabarma kusada Abby ya gaida shi da fara'a, Abby ya amsa yana cewa

"Ya jikin Ummyn ku kecemin bakajin dad'i"

Yad'an duk'ar dakai yace

"Dasauk'i Abby"

Abby yace

"Ya Jiddah tah? Ance kaje dubata jiya"

Nan da nan ya saki lallausan Murmushi
Chapter 10 · 0% Book details