← Book details Yaa Sheikh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 12

Sashe 7

Yaa Sheikh Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A b'an garan Nana har tafi Jiddah Farin ciki da jin wannan labarin sai dai ita Nana acikin satin nan za a kaita Saboda angama mata komai, Nana bata so haka ba amma Jiddah ta kwantar mata da hankali cewar ai itama ba dad'ewa za taiba an kusa gama mata nata shirin.

Figo baiji dad'in Nisan da masoyiyarsa Jiddah zatai ba amma acewar sa ba wani abun damuwa bane Tunda tana tare da Nana mai yi masa ban ruwa a soyayyar tasa. lol😂

Haka akayi kuwa Nana ta tafi a satin, inda kuma Yaa Sheikh yaketa yima Jiddah nata shirin don yace bayason ta buk'aci wani abu.

A kwana goma da Nana Tayi a makaranta ba Wanda bai santaba Saboda bak'in rashin ji da rashin kunya, hatta malamai sun gane ta.

A yanzu Nana bata da wani buri da ya wuce taga k'awarta ta a makarantar Saboda kowa yak'i k'awance da ita gudun kar a Shafa mai bak'in fenti.

Yau ta Kama ranar Monday kuma yau ne Yaa Sheikh ya d'au niyyar kai Jiddah makaranta.

Keep flowing
Khairaty😘✍🏻
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*Yaa Sheikh*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*BY:U. K. Y. For real*😘

🌈 *kainuwa writers asso*✍🏻

*Dedicated to Mmn khairy*🤝🏻 😘

*55to60*

An gama saka komai a boat din moton Abii Jiddah kawai Yaa Sheikh yake jira cos shima ya gama shirin shi.

A cikin gida kuwa Jiddah ce keta sharb'an kuka harda majina, gaba d'aya jikin ta yayi sanyi zata rabu da Mamyn ta da kuma Ummen ta suyi fad'a su shirya.

Nasiha Umme Tayi mata sosai sannan ta kwantar mata da hankali.

Ita kuwa Mamy cewa tai ba ruwanta Tunda Jiddah itace tace taji ta gani don haka Tayi mata shuru, to amma abunka da d'a da uwa cikin ranta tausayin Jiddahn ne ya bai baye ta, basu tab'a rabuwa ba koda na Kwana daya ba don ko Borno tare suke zuwa amma sai gashi yanzu Jiddahn ta zab'i makarantar kwana.

Mamy ta kalle ta tace "Kid'au jakar ki kije yana jiranki fa kin sani sarai kinzo kin tsaya"

Ta d'auki Jakarta Umme ta taya ta da wasu sauran kayan da ba'asa a moto ba suka nufi waje Jiddah sai shasshk'ar kuka take Ummy nata bata hak'uri.

"Allah ya kiyaye ya kuma tsare kuma ki maida hankalin ki kiyi karatu" wannan shine abinda Mamy ta iya cewa, ta koma cikin d'aki don baza ta iya ganin tafiyar tilon "yarta-taba.

Yaa Sheikh yana tsaye yanata kallon agogo don baison suyi rana Saboda makarantar ba a cikin gari take ba, ya shirya tsaf cikin farar jallabiya kana gani basai an gayama kud'in taba kasan mai tsadace Tayi cif da jikin sa gashi ta karb'i kalan fatar sa, wani bak'in sau ciki ne a k'afarsa shima yayi matuk'ar kyau ak'afar tasa, sanna ya kawo bakar hula irin ta larabawa yasaka sumar kanshi tasha gyara ga wani bak'in agogo daya haska hannun shi,kai gaskiya yaa Sheikh kyakkyawane gakyau ga gayu ga tsafta ga iya soyayya uwa uba ilimin addini Dana zamani, a tak'aice Yaa Sheikh ya had'u matuk'a.

Yana tsayenne Umme tafito rik'e da hannun Jiddah suka k'arasa jikin motar.

"Kukan me takeyi kuma? Kefa kikace kina so, zakiyi shuru ki shiga mota kosaina sab'a miki? "

Umme ce ta kalleshi tace"Aa Abdallah kabita a hankali banason wata magana, Jiddah ki shiga mota kutafi karku yi rana"

Jiddah najin haka ta kuma fashewa da kuka "yaya don Allah kayi hakuri Wallahi na fasa bana so"ta k'arasa maganar tana k'arasawa gun shi da gudu ta fad'a jikin shi ta rungume shi.

Sosai yaji tausayin ta amma bakin alk'alami yariga ya bushe dole ya kaita.

"Kiyi shuru kinji Jiddah na ki daina kuka, kece fa kikace kina so, ba komai kiyi hakuri zan dinga zuwa duba ki kinji "yan mata na? "

Da haka dai ya samu ya lallab'a ta, Umme tana tsaye Tana kallon ikon Allah.

Da haka yaja moton suka d'au hanya Jiddah tana ta d'agawa Umme hannu.

Zallan so Yaa Sheikh yake nunawa Jiddah amma da yake ita a nata tunanin 'yan uwan taka ne kwata kwata bata kawo komai a ranta ba.

"Jiddah na tafiya zakiyi ki barni? Zanyi kewar ki Jiddah, Allah ya nuna min ranar da bazaki kuma yin nisa dani ba ranar da zan zama ke, ke ki zama ni, Jiddah zan shar dake dad'in da baki tab'a jinshi ba a duniya , yanda ko ance kiyi nisa dani ma bazaki iya ba, Jiddah na kice kina sona please "

Jiddah da tai kasak'e Tana kallon bakin Yaa Sheikh da yake matuk'ar burge ta yadda yake motsa shi kamar bai son yin maganar, a ranta cewa take dama nata ne da sai itama ta ringa yin yanga. Lol

"Jiddah na bazaki ce kina son nawaba "ya fad'a kamar zaiyi kuka.

Da sauri ta d'ago tace"aa yaya zan fad'a ina son ka mana, kasan wani abuma yaya Wallahi ina son wannan bakin naka"ta fad'a tana kai hannu zata tab'a yayi sauri ya rik'o hannun nata saboda yasan saukar hannunta kan bakinsa ba k'aramar fitina zai haifar ba amma duk da haka rik'e hannunta da yayi saida yanayinsa ya sauya.

"Jiddah kalleni"ya bata umarni ba musu Tayi yanda yace ta kalle shi suna kallon juna amma hanunsa rik'e da sitiyari.

"Jiddah kika ce bakina yana burge ki? "

"Eh Wallahi yaya, bakaga ba har wani iyayi kakeyi dashi"

Dariya ta bashi sosai saida yayi mai isar shi sannan ya kuma kallon ta yad'ora da cewa "Jiddah na Inama dai inada damar nuna miki wannan bakin nawa da yake burge ki mallakin ki ne, Allah ka nunamin wannan lokacin"

Batare da ta gane me yake nufiba tace "amin"

*********************"""***********************"
Sai a wannan lokacin suka iso cikin matarantar babu b'ata lokaci Yaa Sheikh yashiga bin duk wata ka'ida da zata tabbatar da Jiddah ta zama cikakkiyar 'yar makaranta, ansha artabu sosai Kafin Jaddah ta cika Yaa Sheikh ya tafi saida malamai sukayi mata jan ido tukunna.

Yaa Sheikh yabar Jiddah zuciyar sa cike da tausayin ta.

Khairaty😘✍🏻
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*Yaa Sheikh*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*BY:U. K. Y. For real*😘

🌈 *kainuwa writers asso*✍🏻

*Dedicated to Mmn khairy*🤝🏻 😘

*60 to 65*

*Alhamdullah ala kulli halin am back, am really really appreciate your support and cares, prayers, calls, messages.... I will use this ofacunity to great all my family and friends......*
*BARKA DA SALLAH*

Wani malami ne daga cikin malaman gurin ya daka mata tsawar don yaga da alama Jiddan shagwa'babbiya ce.

"Ke! "

Ay kuwa a razane ta d'ago jikin ta na rawa tace "na'am"

Sake hade rai malamin yayi yace "ki fara d'aukar kayanki one after the other kina kaiwa bakin bishiyar can kafin students su tashi daga class saiki samu mate d'inki su taya ki d'auka"

Ya k'arasa maganar yana mata nuni da bishiyar.

Ba musu ta fara d'aukar kayan nata, tana dana sanin zuwan ta boarding a zuciyarta......

Nana kuwa a lissafin ta yau ne sahibar ta ta zata zo don haka take allah allah a tashi daga class...

Yaa Sheikh tuk'i kawai kake yanajin kamar bai kyautama Jiddahn shiba dama bai biye taba dama bai amince da zuwanta boarding school ba amma aykin gama ya Riga da ya gama saidai yasan sai ya dage wajen yak'i da zuciyar shi don tun daga yanzu ya fara jin missing din Jiddahn, ..."fuuhhh! "Wata zazzafar iska ya furzar yana karawa da cewa....

" ohhh Allah help me out,... son 'yar k'aramar yarinya zai kashe Abdallah"

Duk shi kad'ai yake maganarsa.

(Ayya Abdallah abun tausayi )

Adaddafe ya cigaba da driving din zuciyarsa cike da tunani....

Ba karamin dad'i Nana taji ba saboda ganin aminiyar ta don haka bakin ta yaki rufuwa......

"Ke wai dagaske kece Jaddah? "

A salib'e Jiddah ta kalli Nana kafin tace"to da wacece"?

Ay kuwa sai Nana ta kwashe da dariya sannan tace "ke kinga fiskanki fa kinga yadda kike wani gwab'a fuska kamar kina gaban wannan mai jallabiyar da tashi kafiya naci? To bari kiji in fad'a miki garama ki zama jan ido idan ba hakaba a raina ki"
......... Ta karashe maganar tana d'aga kirji sama, duk wani iskanci na yan makaranta Nana ta haddace su, kai harda karin nata ma Saboda Nana ba baya bace.

Jiddah datai sak'are tana kallon ta, zunbura baki tai tace "daga zuwa na zamu fara ko ?... to Dabadan shi mai jallabiyar ba da baki ganni anan ba yar rainin wayo "

"Kedai kika sani... Bari yan jss 1 suzo wucewa su d'aukar maki kayan"

"Gaskiya Nana ke yar rainin hankali ce kina mate dinsu kice su d'aukar miki kaya? Ko dama ana haka? "

Wata dariya Nana ta yi tace "baki da maths, to Dalla cen ay sababbin zuwa nake samu wanda basu sanni yar jss 1 bace saina had'e rai na kirasu na ayke su kuma suje ba musu, sai su zata ni senior ce kinsan wawaye ne"

Kafin Jiddah tayi magana saiga yan jss 1 nan sun taho don da ka gansu zaka gane sabbabbine kuma yan jss 1 saboda sababbin uniform din jikin su.

Ay kuwa ba bata lokaci Nana ta raba musu kayan tace sukai mata blue hostel kasancewar nan aka bawa Jiddah ita kuma nana a green hostel take, amma hakan bai wa Nana dad'i ba amma ba yadda zatai.

Koda suka shiga cikin hostel Jiddah saroro tai kuma zuciyarta cike da tsoro take bin students da kallo ganin su da tai daga mai mini skat sai mai skin tied sai mai half beast ga Uban acuci maza Akan kowacce.

"Tab" shine abunda Jiddah ta iya cewa.

"Ke kema sabuwar zuwa ce"?

Wata free Fed ta tambaye su

"Eh sabuwar zuwa ce kuma nan blue aka kawo ta"

"Ok to zoki hau layi kafin a raba muku gado"....

Saida Nana ta shiryawa Jiddah komai sannan tace mata "to kizo muje hostel dimu na baki ruwa kiyi wanka na ara miki kaya kafin a baku naku"

Ita dai Jiddah ba uhm ba uhm-uhm Saboda mamakin Nana take Saboda yadda take magana tana d'aga kirji.

A haka Jiddah tai wata d'aya zuwa wannan lokacin ta goge ta gane kan komai duk wani iskancin yan makaranta itama ta iya wani girgije girgijen k'irjji ta iya dama ga abubuwa sun fara bayya na.

"Babyn Figgo kije ki karbo mana abinci"
Chapter 7 · 0% Book details