← Book details Yaa Sheikh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 12

Sashe 6

Yaa Sheikh Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yeeeee naji da'di Ya Abdallah"

"Toh Jiddah bari na 'karasa shiryawa ko?..... sai anjima Zan sake kira Kafin mu tashi"

Da haka sukai sallama.

9:00pm jirgin su Ya Sheikh ya 'daga sai Nigeria 🇳🇬

I love ❤️ u all my fans🤝🏻

Khairaty 😍😘
[21/04, 10:00 a.m.] Shooly: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*Yaa Sheikh*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*BY:U. K. Y. For real*😘

🌈 *kainuwa writers asso*✍🏻

*Dedicated to Mmn kheiry*🤝🏻

*Note*: *naji sa'kon ku masoya na cewar bakwa so Jiddah taje boding school to amma Idan kunyi ha'kuri na d'an lokaci ne kucigaba da bina kudai kawai*🤝🏻😍

*45to50*

_Wannan page din nakune abokan arzik'i 😍 *Yaa Sheikh fans* 😍_

'Tun safe Jiddah take zaman jiran Yaa Sheikh amma shuru kakeji, harkusan magarib bashi ba labarin sa.

Kallon ta Mamy tai tace "tashi ki shiga gidan Ummy ki tambaye ta kiji ko baban nawa ya kira ta?nasan dai yanzu kam sun iso".

Jiddah kamar mai jiran hakan, ta mi'ki da sauri ta sa hijab ta fita sai gidan Ummy,

Tana shiga ta tarar da Ummy itama tana zaune ta cab'a ado na tarbar d'an ta.

Bayan ta gaishe da Ummynne take tambayar ta
"Wai Ummy Ya Abdallahn bazai dawo bane kodai dama bai taho Ba? "

Ta k'arasa maganar kamar zatai kuka Don har idon ta ya kawo kwalla.

"Au kuka zakiyi saboda bakya raina abin kuka? To Abii ya tafi d'akko shi yanzunnan zaki gansu, Dan Tun d'azu Abii ya tafi d'aukan shi "

Sai a sannan taji dad'i ta saki ranta ta hau yiwa Ummy hira.

Suna cikin hirar ne su kaji tsayuwar motar Abii, Jiddah kawai k'urawa k'ofa ido tai tana jiran taga shigowar Ya Abdallahn ta.

Da sallama suka shigo,....... Ido hud'u sukai da junan su ay kuwa Jiddah ta wani zabura tai kan Ya Sheikh, bai Ankara sai ji yayi Jiddah ta rungume she,

" *YA SALAM*"

Shine abin da ya iya furtawa saboda yadda yaji tsigar jikin shi ya tashi ga wani jiri da ya d'ebe shi, taga-taga ya fara kamar zai fad'i, Ummy da ta Ankara da halin da Ya Sheikh ya shiga tai saurin cewa "kai Jiddah bakisan kin girma Ba yanzu ay saiki kada yayan naki",

Da Wannan damar Ya Sheikh yai k'ok'arin tattaro nutsuwar shi sannan ya zame jikin shi daga na Jiddah.

Abii ne yace" to ay sai ku samu guri ku zauna ko? "

Dukan su zama sukai sannan Ya Sheikh ya gaishe da Ummy zuciyar shi cike da murnar ganin shi a gida.

"Lafiya kalau Abdallah ya hanya ya karatu to Allah ya sa angama a sa'".

"Amin ya Allah, Ummy na"

haka dai sukaita gashe-gaishen su da hirar yaushe gamo, Abii yana ta tambayar shi game da aykin da madina suka bashi, kafin daga bisani Abii ya tashi ya shiga d'akin shi.

Ya Sheikh sai satar kallon Jiddah yake yana mamakin girman da ta k'arayi, ga wani iyayi da take kamar wata cikakkiyar budurwa, Ummy ce takatse mai tunanin da yake tace,"Abdallah akawo ma abinci KO? "

"A'a Ummy bari dai na fara wanka"

Bayan yayi wankane ya fito cikin shirin sa, sanye yake da wata black jallabiya, kannan a gyare sai zuba k'amshi yake Idan kagan shi kamar balarabe duk dade hasken shi Ba irin na larabawa bane irin na yan sudanne ne amma Ba k'aramin kyau yayi ba.

Zama yayi sannan yace"yawwa to yanzu Kinga sai naci abincin ko Ummy na? "

Murmushi Ummy tayi sannan face"to Abdallah bari na d'auko ma"

Tana fad'in haka ta nufi kitchen .

Jiddah itama mik'ewa tayi da niyyar taje ta taya Ummy d'auko abincin, da sauri Ya Sheikh ya ruk'o hannuta ya maida ta ta zauna suna kallon juna sannan yace

"Jiddah na baki ce nayi kyau ba kodai banyi ba ne? Don kefa nai wannan wankan"

Ya k'arashe maganar yana kurawa k'wayar idonta kallo, kamar mai jin bacci.

Kallon shi itama tai sannan tace

"kayi kyau mana ka ganka kuwa kamar balarabe"

"Toh Jiddah nah nagode, yanzu to kice kina sona"

Ta kyalkyale da dariya tace"kai Ya Abdallah nace fa Ina sonka kuma kaima kace kana sona ba shikenan ba"

Zuwan Ummy ne ya hanashi sake cewa komai, Don haka kawai ya fara cin abincin da ta kawo mai.

Bayan ya gama yace

"Ummy bari na shiga na gaishe da Mamy naga dare yana yi"

Haka kuwa akai suka tashi shi da Jiddah, Jiddah mata yiwa Ummy saida safe.

Mamy tayi Farin ciki sosai da ganin Ya Sheikh, sun d'an tab'a hira Karin Ya Sheikh yayi mata saida safe, Jiddah tanajin haka tabi Bayan sa, a zaure suka tsaya Jiddah tayi k'asa-k'asa da murya tace" Ya Abdallah karfa ka manta nace maka zan gaya maka wata magana amma sai da safe"

"Toh Jiddah Allah ya kaimu"

Sallama sukai ya nifi gida,.... yana shiga -yayi wa Ummy da Abii saida safe, yashige d'aki yayi shinrin kwanciya Bayan ya gama duk abubuwan da ya sabayi.

Yana kwanciya tunani yace salamualaikum, haka yaita tunani,................ Tab wai Jiddah ce ta k'aragirma haka, amma daga nayi magana Ummy tace wai nayiwa Jiddah girma baza ta iya dani ba, to ay in ita bazata iya Dani Ba ni zan iya da ita.

Da irin wad'annan tunanin bacci yayi awangaba da shi.

Khairaty😘🤝🏻
[21/04, 10:00 a.m.] Shooly: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*Yaa Sheikh*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*BY:U. K. Y. For real*😘

🌈 *kainuwa writers asso*✍🏻

*Dedicated to Mmn khairy*🤝🏻 😘

Surah Al-Araf, Verse 27:
يَا بَنِي آدَمَ لَا يَفْتِنَنَّكُمُ الشَّيْطَانُ كَمَا أَخْرَجَ أَبَوَيْكُم مِّنَ الْجَنَّةِ يَنزِعُ عَنْهُمَا لِبَاسَهُمَا لِيُرِيَهُمَا سَوْآتِهِمَا إِنَّهُ يَرَاكُمْ هُوَ وَقَبِيلُهُ مِنْ حَيْثُ لَا تَرَوْنَهُمْ إِنَّا جَعَلْنَا الشَّيَاطِينَ أَوْلِيَاءَ لِلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ

O children of Adam! let not the Shaitan cause you to fall into affliction as he expelled your parents from the garden, pulling off from them both their clothing that he might show them their evil inclinations, he surely sees you, he as well as his host, from whence you cannot see them; surely We have made the Shaitans to be the guardians of those who do not believe.
(English - Shakir)

via iQuran juma a Mubarak

*masoyana ina godiya da kulawar da kuke bani, wad'anda suka kirani da Wanda suka bini pc duk ina godiya kuma ina k'ara baku hak'uri abu buwa ne sukai min yawa*

*50to55*

'Dumin abinda ya fitar daga jikin sane ya farkar dashi daga mafarkin da yake, gaba d'aya ya had'a gumi afili ya furta "hasbunallahu wa ni'emal wa kil, why!? Me yasa haka ne?"

Duk shi kad'ai yake surutan sa kafin daga bisani ya kalli agogon dake mak'ale a jikin bangon d'akin nasa, k'arfe 3:00 dai-dai don haka ya tashi ya nufi toilet.

Bayan ya tsarkake jikin sane ya fara gabatar da nafilfilu yana adduar Allah ya kawo masa mafita don shi kansa wani lokacin Yana gasgata maganar Umme cewar Jiddah ta mai k'ank'anta ya nemi wata,

To amma fa shi bashi da wani interest Akan wata mace Bayan Jiddah da ya kwallafa ranshi a kanta, don haka dole ne ya rok'i Allah mafita, ahaka har lokaci shiga sallar asuba yayi, don haka ya feshe jikin shi da turare ya nufi masallaci ba tare da ya shiga cikin gidan nasu ba.

Da misalin karfe 8:00 na safe Jiddah har ansha wanka za'aje rok'ar al farman tafiya boarding school gurin Yaa Sheikh sai addua take Allah yasa ya yarda, fitowa Tayi ta iske Mamy a falo, kame kame ta fara kafin ta nemo abun fad'a.

"Umm Mamy zanje gun Umme na gaishe ta"

Mamy tace "hmmm Jiddah kenan zadai kije gurin babana ay ba hanaki zanyi ba sai kin dawo".

Aykuwa sim-sim ta fice ta nufi gidan Umme,
Tana shiga bata tsaya ko ina ba sai d'akin Yaa Sheikh a cewar ta koma ina yake ai zai shigo d'akin sa, tai zamanta, Aikuwa tana cikin tunanin nan Yaa Sheikh din ya shigo, dawowar sa kenan daga masallaci don Tun fitar sa sallan asuba bai dawo ba sai yanzu.

Tashi tai da gudu zata rungume shi Aikuwa k'irjjn shi har dukan uku-uku yake Saboda shi yasan wani irin yanayi ya shiga jiya da ta rungume shi gashi yau yana azumi don haka yayi sauri durk'usawa ya dafe cikin sa Yana cewa"Asssshhhhh"

A tsorace ta dago tana kallon sa "yaya mene? "Ta tambaye shi.

"Cikina "yabata amsa

"To sannu yaya muje ka kwanta"

Haka ta tusa shi gaba kamar k'aramin yaro, saida taga ya zau na Sannan ta sake yimai sannu.

Shidai a cikin ran sa Allah yake wa godiya da bata tabashi ba sannan yana tunanin ya rayuwar sa zata kasance a gaba, ba zaiyiwu ace kullum zai dinga k'arya Saboda Jiddah kar ta tab'a shi ba, kuma ya fuskanci kamar bata da ranar daina rungumar sa, " tab akwai aiki"ya fad'a a zuciyar sa.

"Sannu yaya kasha magani ko zai daina "

"Toh Jiddah zan sha sai anjima, yanzu dai ki fadamin abinda kika ce zaki fad'a min"
Ya k'arasa maganar yana kallon ta.

Ita kuma ta sunkuyar da kai tana jin tsoron abinda zai biyo baya idan ta fad'a mai ko zai yarda ko bazai yarda ba.

Cikin k'ink'ina ta fara magana"umm emm... Dama yaya so nake a kaini boarding ni banason day Saboda a boarding anfi karatu kuma inason boarding school nidai yaya "ta k'are maganar tana zuba mai shagwa'ba.

A rud'e ya d'ago yana kallon ta duk Yabi ya susuce" kiyi shiru mana, badai kince kina so ba, kuma zaki iya? "

"Eh yaya inaso"

"To shike nan ki bari Zanyi shawara "

"To yaya amma kar kayi shawaran da Mamy kaji"

"To naji tashi kije "

Ba musu ta fita ranta fari k'al, don ga dukkan alamu zatai nasara.

Shi kuwa Yaa Sheikh wata ajiyar zuciya ya sauka had'i da furzar da wata zazzafar iska.

"banida wani zab'i da ya wuce na bar Jiddah ta dafi school nima zan samu sauk'in abinda nake ji idan bana ganin ta, indan yaso in Zan koma madina sai nai mata transfer don har ga Allah banason makarantar kwana ko don karatun islamiyyar ta" shi kad'ai yake maganarsa kamar zau tacce.

**************

Three weeks ago

Komai ya kammala Mame ta amince da maganar zuwan Jiddah makaranta, haka, Abii da Umme duk sun yarda kasan cewar sunga yadda Jiddah ke so taje makarantar kwanan.
Chapter 6 · 0% Book details