← Book details Yaa Sheikh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 12

Sashe 2

Yaa Sheikh Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mamy tace baba nah baci za tai ba kyaleta kawai kar ta Tara mana jama'a , haka take cemai baban ta saboda su nan baban ta abdullahi.

To shikenan mamy bari naje dama ummee ce ta ce azo aduba ko lfa,
yamike zai tafi,

ayko Jidda tace batasan zancen ba ita sai ta bishi don idan yatafi mamy Zane ta za tai,

Itadai mamy da kallo tabi ta don halin Jidda sai addu'a.

Harta rigashi kaiwa zaure tana gaba yana ba ya yaiwa mamy sallama ya fice.

Ta riga shi shiga gidan don haka ya hango ta akan cinyar ummee tana ta zuba ta'barar ta dama halin Jidda ne,

Ummee nah nidai agidan nan zan kwana yau mamy tace saita Zane ni saboda banci tuwo ba,

kai jiddo banda sharrifa inji Abdumajid,

Ayko tahau shure shure ummee nah kinji wannan yaya abdulmajid din yana cemin jiddo ko? Ta karashe maganar tana nuna Abdulmajid da yatsa cike da shagwa'ba da ta'bara,

Abdulmajid banason tsokana wlhy zan sa'ba maka akan tsokanar yata da kake yi,

To nima sai na rama wool bai iya hadda ba tana nai gwalo ,

Ayko takashe bakin abdulmajid yai shiru an ta'bo maganar hadda,

Abdallah bai sa musu bakiba donshi ta'baran jiddan ma mamaki yake bashi , yafara cin abincin shi da tun dazu da aka ajiye mai,

tsilum saiga Jidda agabanshi , yaya Abdallah nah abinci zakaci? Nima zanci, amma nidai a baki zaka bani takarasa maganan kice sa shagwa'ba

Kallon ta kawai ya tsaya yanayi yacigaba da cin abincin sa

Ummee kinga yace wai bazai bani ba

Kafin ummee tai magana ya zuba mata wani razanan nan kallo mai ma'anar ki shiga taitainki fa,

Ayko tsiiit tayi tana kallon sa kuri da ido, candai dataga ba bata zaiyi ba tace don Allah na ci?

"Jeki wanko hannun ki "

Ba musu raje ta wanko hannun ta tadawo

Yabita da kallo azuciyar shi yana tunanin kai yarinta kenan wai mutun yanajin yinwa amma wai yace bazaici tuwoba wai sai abinda ya taza'ba, ummee ce ta katshe mai tunani tana tambayar shi Abdallah kunyi waya da abii kuwa?

Eh ummee munyi ay goben zai dawo ko ko yasake shawara ne?

A'a goben zai dawo dama natambaye Kane ko bai gaya maba,

"Ok ya gayamin ummee Allah y dawo da shi lfa"

"Dukansu suka amsa da amin"

Itako zuwa tai ta zauna jikinta har rawa yake tasa hannu ta fara ci,

Saida suka cinye na fleet dinne yake tambayarta ko ta koshi , tace, a'a yakara mata shikuma ya tashi yaiwa ummee sai da safe ummee tace Allah ya tashe mu lfa.

Yanufi dakinshi dake zaure ,

Ikon Allah kai bakace dakin matashin saurayi bane kamar haka ba ,

Dakin bawani babba bane amma tako ina carpet ne ashinfide da 'Yar durowa ajikin bango mai biyu, sai d'an mirror da turarurruka kala kala amma dai bawasu masu tsada ba , sai katifa dai dai kwanciyar mutun biyu ya lailaye ta da bed shit da wata anger ta rataye kaya, d'akin fes fes dashi sai 'kamshi yake kamar dakin budurwa budurwar ma mai tsafta,lol

Kayansa ya rage ya sa jallabiya sannan ya kuma nufar cikin gida don watsa ruwa da d'auro alwala don haka tsarinsa yake baya konciya sai da alwala ,

koda yashiga har su abdulmalik sun shiga dakinsu ummee ma tadauki Yar rigimarta sunshige, don anan ta bingire bayan tagama tsokanar abdulmajid tai bacci,

Bayan ya gama ne yakoma d'akinshi ya cire jallabitar ya fesa body spree yasa wayanshi a chage yai addu'a yakwanta hadida addu'ar Allah y sa kar yayi mafar kin nasa na jaraba,

shi yana mamakin wannan Abu ace rana d'aid'ai ne ba zaiyi mafarkin yana Tarawa da mace ba shidai yasan bawai yasa son mata aransa bane kuma yana azumi litinin da alhamis kuma yana kokarin kauda idon sa ga duk abinda zai sashi jin shaawa don kare addimin sa da imanin sa don gudun sabawa mahaliccin sa

Eh bazaice baya son kasan cewar mace a kusa da shiba saboda yasan shi lafiyayyan namiji ne,

amma yasan ba abu ne mai yiwuwa ba kasancewar bashida ayki kuma albashin sa na Sahsib islamiyya bawani mai yawa bane,

kuma abii ma ba wani karfe ne dashi ba sai dai rufin ashiri duk da yasan abii mutum ne mai kokarin yaga yarufawa iyalin asiri,

ga iyalan 'kanin shi baffa usman wato mamy da jadda duk shi yake dawainiya dasu duk da dai tasu dawainiyar ba mai yawa bace saboda mamy tana Yar sana'arta don itama taga tarufawa kanta asiri amma duk da haka bazai iya bijiro da zancen aure ba shiyasa yake kai zuciyar shi nesa.

Da ire iren wannan tunani bacci yayi gaba dashi....
[21/04, 9:59 a.m.] Shooly: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
*YAA SHEK!!*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*BY:U.K.Y. for real*😘

🌈 *kainuwa writers asso*🤝🏻

*dedicated to mmn khaery*🤝🏻

1⃣0⃣to1⃣5⃣

Koda ya farka karfe hud'u dai dai duk da cewa ya makara tashi sallan dare, amma fa aykin gama yariga ya gama, abun dai da bayaso shi yagani,

Ya Allah wannan wace irin jaraba ce abinda ya furta kenan,

Nifa bansan ma nayi mafarkin ba amma dai gashi alamu sun nuna, duk shi kadai yake wannan zancen kamar wani zautacce,

Goge jikinsa yayi yana nai addu'ar kar Allah y sa ummee ta ganshi idan zai shiga wanka don kusan kullum sai ta ganshi kuma ba karamar kunya ce take kamashi ba, don yasan duk Wanda yaganshi yayi wanka da asuba to kuwa yasan me ya faru d shi,don ma dai Abii ba mazauni bane da kunyar sai tafi haka ,

Futowa yayi yana sand'a kamar 'barawo bakin shi d'auke da addu'a,

ya samu yai wuf yafada toilet sannan yasauke nannauyar ajiyan zuciya saboda ummee bata ganshi ba,

Saidai baisan shine bai gantaba amma ita ta ganshi, don tazo d'akinsu Abdul Malik taga ko sun tashi, tana fitowa ne ta ganshi yana sand'a,

ta koma d'aki zuciyar ta cike da tunanin wai meke damun abdallah,

kusan kullum sai yayi wanka,to komadai meke damun shi saidai yasama ranshi hakuri don aure ba yanzu ba, shida bashi da ayki.

Bayan yafito agurguje ya shirya yanufi masallaci,

"Abdul Malik wai bazaku fito Ku karya bane lokaci yana kurewa? Inji umme

" ummee gamu nan zuwa"

To Ke kuma Jidda aydai yanzu kin bushe ko saikizo nashafa miki mai,

Turo baki tai tana ma'ke kafad'a "nidai nizan shafa da kaina, wankan mafa na iya kika ce saikin yi min"

Naji to jeki shafa kifito ki karya inji ummee,

Suna karyawa ya shigo sai lokacin yadawo saga masallaci, ya nemi guri kusa da ummee ya zauna yana gaishe ta,

Fuskan ta dauke d fara'a tace lafiya klau abdalah,

kana azumin kuwa yau alhamis?

A kunyace yace
"Eh ummee inayi"

To da kyau madalla Allah ya muku al barka,
"Suka amsa da amin"

Su Abdul Mali suka gaishe shi shima ya amsa yana mai cewa kuyi Sauri kun kusa makara fa,

Kafin suyi magana sukaji sallama, mamy ce tashigo hannun ta dauke da uniform din Jidda,

suka amsa mata, tazauna suna gaisawa da ummee , suma duk suka gaisheta ta amsa cikin fara'a ta Dora da cewa amma dai waccan Yar rigimar ita tashafa wannan man? tai maganar tana kallon inda jidda ke zaune da daurin kirji Wanda tayi da 'Dan kwalin ummee,

Ayko su Abdul Malik suka kyalkyale da dariya, ganin yadda fuskan jiddan take maiko

Sukuwa manyan yara wato Jidda Yar aji daya a primary an sha Vasilin a fuska sai maiko take , kuma ko ahikin ta,

ta dago ta kalle yaa shek Wanda tunda ya gaishe da mamy yamai da hankalin shi kan wayarshi, tace

" yaya abdallah batajira amsar shiba tadora da cewa gaskiya nidai yau Kaine zaka kaini makaran ta, idan muka tafi dasu yaya Abdul malik dukana sukeyi suce wai bana sauri,kuma basa Shiga dani makaranta a bakin layi suke barina, ta'karasa maganar har da 'Yar kwallar ta.

'Dago kai yayi yana kallon su rannan abace yace mai yasa kuke dukan ta?

Wlhy 'karya takeyi yaya idan muka tafi da ita bata sauri , taita bata mana lokaci,yaya don Allah kawai tunda makaran tarsu banisa tadinga tafiya ita kadai, tunda idan yawanta yatashi har gaba da makarantar tasuma tana zuwa,

Many tace aykuwa dai ingun gama kuringa tafiyar ku, zanje ay gurin auntyn taku nace taringa zaneki idan kin makara,
Karbi uniform dinki ni kisaka,

ta karba tana bubbuga 'kafa,

Ummee tace 'karfa Ku takurawa auta ta, zonan na sakamiki kinji,

Takarba tasaka mata tace abdallah zo kakai ta tunda tace kai zaka kaita ,

Bamusu yatashi ya rike mata hannu suka fita, suma su Abdul majid suka kama hanya,

Ahanya ne tasa mai kuka wai itasaiya d'auketa, bayadda ya iya haka ya d'auketa,

saboda shi fa duk 'kan 'kartar Jidda idan tana wannan shagwa'bar ta ta sai yaji wani iri kuma hankalinsa yana tashi matuka.

Asalin su Jidda da Yaa shek!...
[21/04, 10:00 a.m.] Shooly: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*YAA SHEIKH!!*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*BY:U.K.Y. for real*😘

🌈 *kainuwa writers asso*✍🏻

*dedicated to mmn khaery*🤝🏻

_Note: masoyana ina mai ba Ku ha'kuri don zakuga spelling d'in rubuta sunan littafin nan ya sauya daga Yaa Shek zuwa Yaa Sheikh,amma hakan ne ya kamata ya zama ,ina godiya gaduk kan masoyana, nima aylobiyu Lodi lodi_.🤣

*Special tanx to*:

Ummy Abduol,Ummu farheen and Aunty Fauziyya.

1⃣5⃣to2⃣0⃣

Malam Gaddafi da wato Abii mahaifin Yaa sheikh, da kuma malam Usman mahaifin Jadda, 'yan uwan juna ne uwa d'aya uba d'aya suke.

Mahaifiyar su Hajiya Laila Shuwa ce ita 'Yar garin Borno, shi kuwa mahaifinsu Alhaji Mahi d'an 'kasar Sudan ne.

Kasancewar ba inda aure baya kai mutum ne yasa ya kai Hajiya Laila kasar Sudan ,bayan auran ne Allah ya azurta su da yara biyu wato Gaddafi da Usman, Gaddafi shine babba sannan Usman.

Usman yana da shekara d'aya Allah yayiwa mahaifin su wato Alhaji Mahi rasuwa, k'warai rasuwar ta jijjaga Hajiya Laila da 'yan uwan Mahi.

Bayan ta gama takaba ne ta shaidawa 'yan uwan Mahi Zata koma kasar su Borno,basuji dad'i ba matu'ka, amma ba yadda suka iya dole ne ta tafi tunda dama ba 'Yar 'kasar Sudan ba ce.
Chapter 2 · 0% Book details