← Book details Yaa Sheikh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 12

Sashe 12

Yaa Sheikh Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Cike da ladabi ya amsa tare da d'an duk'ar dakai ya gaida shi kamar yana gabansa, Abby ya amsa yana tambayansa ya jarabawa, cikin natsuwa ya soma masa bayanin tun zuwansa har zuwa yau dazasu duba sakamakon jarabawan tasu.

Lokaci lokaci Nu'aym kan juyo yana kallan Abdallahn da d'an murmushi ganin yanda ya natsu yana wayar duk yanda akayi wanda suke wayan yanada matuk'ar muhimmanci da kuma girma a wajansa.

Addu'a sosai Abby ya masa na samun nasara sannan ya mik'ama Ummy wayan suka gaisa itama ta masa addu'a sosai sannan sukayi sallama ya kashe yana murmushi cike da annashuwa.

Har Nu'aym ya bud'e baki zai masa magana sai kuma ya fasa ya cigaba da driving d'insa hankali kwance. Cikin k'ankanin lokaci suka isa makarantar tasu, Direct notice board suka nufa, sun samu d'alibai da dama suna duba result d'insu hakan yasa suka koma gefe har saida aka d'an ragu.

Abdallah ne ya soma ganin masa, ya samu points sosai har yayi yawa, Shima Nu'aym yaga nasa shima yayi nasara dan ya samu abinda yakeso. Hannu suka mik'a ma juna sukayi musabaha saboda murna, A take ya sake kiran Abby ya sanar dashi, sunyi farinciki sosai tare da yi masa Addu'a.

Sai da yanma sannan aka samu attending d'insu, batare da wani b'ata lokaci ba aka basu takardar d'aukansu aiki, a matsayin Malaman Jami'a sai dai Jami'ar da zasu koyar ba d'aya baneh anma yana kusa da juna.

Murna wajan Nu'aym da Abdallah ba'a magana. Murnan su sam yak'i b'oyuwa. Jiddahn shi ce ta fad'o masa a rai, ya saki murmushi a ransa yana ayyana Jiddansa ta kusa zama nasa san don son zata zama tashi cos dama jiran ayki yake.

To dama haka rayuwa take wasu suyi nasara wasu kuma akasin hakan don da dama wasu basuyi nasara ba.

Khairaty😍
[7/13, 5:49 AM] 0mmer Farouk: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
*Yaa Sheikh*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*U. K. Y. For Real*😍

*Dedicated to Mmn Khairy*🤝🏻

*96 to 100*

Sai da suka fito daga office din sannan suka bubud'e lettern dan karanta abinda ya k'unsa

Bayan Abdallah ya karanta nasa ya d'ago yana kallan Nu'aym wanda shima ya maida hankali kan takardar hannunsa

"Alfaisal University Riyadh zanyi aiki"

Nu'aym ya sake kallan nasa sannan yace

"Ni kuma a Prince Sultan University, Its ok ai duka Riyadh din neh"

Suka mik'a ma juna hannu sukayi musabaha cike da jindad'i. Motan Nu'aym suka nufa suka nufi gida cike da murna. Saida suka isa sannan Abdallah ya Kira Abby ya fad'a masa abinda ke faruwa.

Abby dasu Ummy sunyi matuk'ar farinciki, d'aya d'aya Abby ya mik'a ma su Ummy wayan suka masa murna harda Mamyn Jiddah dan ta shigo gidan. Sun masa fatan Alheri sosai.

A cikin Satin sukayi bikin murnar Kammala makarantar, taro ne wanda ya amsa taro, daga Abdallah har Nu'aym sakin baki sukayi ganin manyan mutane wanda suke gani a tv. Sarkin Saudi Arabia wato Sarki Salman shima ba'a barshi a baya bah tare da tawagarsa harda babban d'ansa dayake matuk'ar ji dashi.

Anyi taro lafiya, Abdallah har kyauta ya samu na First Class daya samu. Hakan yasa tauraronsa ya haska a taron. Anyi an gama kowa ya koma gidansa lafiya. Saboda tsananin gajiya a Apartment d'in Nu'aym suka kwana, washe gari suka soma shirya kayansu dan zuwa Riyadh, Bayan sun isa Masaukin Abdallah Nu'aym ya fara saukeshi dan kowa an basa gidansa kusada makarantar dayake.

Abdallah ya masa godiya sannan shima ya wuce nasa masaukin. Ya samu ya huta asabar da lahadi, Ranar monday k'arfe bakwai a Alfaisal University Riyadh ya masa. Ba tare da b'ata lokaci ba ya nufi department d'inda xai koyar.

Tafiya yake cikin sanyinsa kamar yanda ya saba, yana sanye da Brown Jallabiya da Bak'ar hula, sosai kayan suka amshesa, duk inda ya wulga sai an kallesa har abin na basa mamaki. direct reporting yayi sannan ya aje jakansa a office d'in da aka basa ya wuce Lecture hall dan an sanar dashi yanada Class da safiyar ranar.

Tunda ya shiga ajin wasu mata su biyu dake zaune a gaba suke kallansa kamar zasu cinyesa. Guntun tsaki yaja a hankali sannan yayi musu sallama tare da gabatar da kansa, sunyi murna sosai da kasancewarshi malamin su.

Bai d'au wani lokaci ba ya soma musu darasi. Cikin kwanciyar hankali yake musu karatun, da tsantsar larafci, tunda ya fara daya d'aga kai sai su had'a ido da D'aya daga cikin 'yan matan dake gaban, a haka har ya gama musu tare da tambayansu ko sun gane, duk suka amsa da na'am. Ba b'ata lokaci ya musu sallama ya fita.

Bashi yabar makarantar ba sai K'arfe biyar na yanma, a gajiye ya tari Taxi ya nufi gida tare da kudurin siyan moto saboda irin hakan.

*Bayan Wata Biyu*

Meenarh ce ta shigo class tana yatsine Fuska tana kallan wata d'aliba dake zaune a kan kujeranta da alama sabuwar d'aliba ce. Cikin k'asaita ta k'arasa ta rik'e k'ugu tana jujjuya ido

"Ke! Uban wa yace ki zauna min a kujera"

Cike da tsoro yarinyan tace

"English teacher ce tace na zauna"

Jiddah da Nana suka shigo a tare, Fiddy na biye dasu a baya, a tare suka k'arasa wajan Jiddah ta kalli yarinyan tace

"Ina kuma muka samu wannan"

Meenarh tace

"Wai new student ce, kuma dan iskanci a seat d'ina"

Nana ta galla ma yarinyar harara

"Ke tashi dan ubanki"

Ganin yanda suka zazzare mata ido yasa ta mik'e dasauri ta canza kujera tana kallansu a tsorace.

Jiddah ta fashe da dariya suka tafa itada Meenarh

"Kuna Burgeni wallahi" cewar Jiddah tana cigaba da dariya

"Stay were uh are!"

Abinda sukaji kenan daga bayansu
Ko ba'a fad'aba sun san Social studies teacher neh, a daidai inda suke suka k'ame. Teachern ya shigo yana kallansu, cikin harshen turanci yace

"Dama nasani ku hud'u nan neh tsaye, Come forward and knell down"

Meenarh ta chuno baki tana gaba suna biye da ita har gaban ajin sukayi Knell down sai turo baki suke.

Malamin mai suna Ahmad Yusuf ya kalli Jiddah yana girgiza kai

"Hauwa'u Usman sanda kikazo makarantar nan uh are Calm, why do uh change?"

Jiddah Ta sake tura baki ta kauda kai tana wani jujuya ido, baice komai ba sai girgiza kai dayayi ya cigaba da koyarwa.

A haka suka tsaya har ya gama sannan yace suje su zauna, Fiddy tayi gaba tana wani turo k'irji tana b'ata fuska, baice komai ba ya fita ya koma staff room. Yana fita Nana tace

"Nifah Mr Ahmad Yusuf d'in nan ya takura mana Wallahi"

Meenarh taja tsaki

"Tsiyar Boarding school kenan"

Fiddy tayi saurin cewa

"Wallahi kuwa"

Jiddah ta amshe da cewa

"Ai yafi ma samin ido, baki maji sunana ya kiraba"

Nana tace

"Dallah kyallesu, mu chanza topic dan bansan jin wannan maganar mah"

*******

Salati yayi ya mik'e zaune yana mik'a tare da duba Jikinsa, Gani yayi gaba d'aya ya jik'e. Ya rik'e kansa da hannu biyu yana d'an girgiza kai

Harga Allah yana matuk'ar buk'atar mace a kusa dashi, kuma ba kowa ba sai Jiddah. Kwanakin nan mafarkan dayake yana making love da Jiddah ya soma yawa.

Ya lumshe ido ya bud'e yana d'an murmushi, he really enjoy the moment he had with her on his Dream. A hankali ya furta

"Da dad'i... Balle kuma reality"

Ya saki murmushi mai sauti

"I can't wait"

Dole ya mik'e ya shiga toilet yayi wanka tare da wanke boxern ya fito.

K'arfe Takwas ya Shiga school direct Office d'inshi ya wuce ya bud'e ya shiga. Ya zauna kenan akayi knocking, ya bada izinin shigowa. Yarinyan nan Student d'inshi ce ta shigo cikin b'akar jallabiya har k'asa tayi rolling da farin veil. Tana sanye da Butterfly eye glasses.

Tsaki yaji kad'an, gaba d'aya yarinyar ta soma takura masa, sam baya ra'ayinta shi ko sunanta ma bai saniba.

Cikin harshen larabci tace

"Zan iya zama?"

"Idan kinaso"

Tad'anyi murmushi sannan ta samu guri ta zauna. Agogon azurfan hannunsa ya duba K'arfe takwas da kwata yasan yanzu a nigeria shidda da kwata kenan na safe.

Wayansa ya d'auka ya soma neman layin Abby, bugu biyu ya d'auka tare da masa sallama, Abby ya amsa, cikin ladabi suka gaisa ya tambayi su Abdul ya amsa da lafiya lau.

Jimmm yayi har saida Abby yace

"Akwai wani abu neh?"

Ya sosa k'eya kamar yana ganinsa yace

"Dama yau ne Visiting d'insu Jiddah, Ummm... Shine...Umm"

Abby yad'anyi dariya yace

"Abdallah kenan! Kanadai ji da k'anwar nan taka".

Yad'anyi murmushi, Abby yace

"Ai Ummynku na nan nata shiri gaba d'aya zamu rankaya mu tafi zuwa anjima"

Dad'i ne ya lullub'esa yace

"To Abby, a gaida su mamy"

Abby ya masa sallama ya kashe kiran. Had'a girar sama data k'asa yayi ya maida dubansa ga Yarinyar dake Office d'insa

"How may i help uh"

Khairaty😍
Chapter 12 · 0% Book details