← Book details Yaa Sheikh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 12

Sashe 1

Yaa Sheikh Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read


Compiled By Umar Dalha Funtua.

Copied By Shooly

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*_YAA SHEK_*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

🌈 *kainuwa writers asso*🤝🏻

*_BY : U.K.Y for real_*

*_Dedicated to Mmn khaery_*

```Assalamu Alaikum yan uwa musulmi wannan littafin nawa nayishine ba Don wata ko waniba ko Don cin zarafin wani ba aa kawai sai Don nishadi ,fadakarwa da kuma wa'azin tarwa ina fatan yadda na fara lafiya na gama lafiya```

1⃣to5⃣

Tashin kira'ar Yaa shek ne ke tashi tun kafin ka karyo kwanar islamiyar mai suna Sahsib kasancewar Allah y hore mai murya gaza'ki ga balaga, kowanna harafi yana fitarwa bisa ka ida

d'alibai ne a zaune cikin wani aji, matasa ne maza d mata jikin su sanye da uniform maroon color suna zazzaune kowa d al'quran a hannun sa sun nutsu suna sauraran karatun

shikuwa malamin nasu wato Yaa shek yana kan wani benci yana ta rero karatun cikin kwanciyar hankali da nutsuwa idon shi alumshe saboda shauki, da ka yake karatun kasan cewar shi hafizin al qur'ani,

sanye yake da wani hadaddan yadi milk color yasha guga, da wata hula brawn,kasan cewar aykin dake jikin kayan ma brown ne, kannan yasha gyara sumar nan baka kirin tayi luf luf da ita takalmin ma brown ne yasha mai sai kyalli yake wandon nan a d'age kai daka gani kasan sunna ta ratsashi ga wani gemu mai ban sha'awa yazauna das dashi sai 'kamshi yake kanagani kasan cikakken mai tsaftane,

Yana kaiwa karshe wata aya yace sadakallahul aziim kafin ya 'Dan nisa yadago kyawawan manyan idanun shi yana kallon yan ajin d'aya bayan d'aya yai gyaran murya yace lokacin fitasalla yayi karfe hud'u da minti biyar duk Wanda bai shigoba to kuwa bazai shigoba yana kaiwa nan ya mike yafita

Ayko yana fita mazan da matan suka hau shewa suna cewa yaaaa sheeek d'aya daka cikin yan matan ce tai magana tana cewa kunga kutashi muyi sauri mu dawo Don ni wlhy dana rasa lecture din yaa shek gara nai zazzabin wuni Don nasan idan na rasa dolene sai nayi

Caraf wata tace ayke zazzabi ma kikace da sauki wata tace nidai wlhy idan namakara zama zanyi naita kuka har sai yace nashigo, ayko kinsan yaa shek ba cewa zai yi kishigoba Don haka kunga tafiya ta ayko gaba daya yan ajin suka rufa mata baya,

suna zuwa wajen sallah wasu yan mata biyar sukawo Kansu d'aya daga cikin yan matan nan tace wayyo kunji dadin Ku yau yaa shek a ajin Ku yake wata takuma cewa kai kugayama na yau wani kalar wanka yayi d'aya tasake cewa nima abinda nakeson ji kenan d'aya daga cikin wayanda yaa shek yafito daga ajinsu tace wai saurin mekuke? nagadai zaku ganshi sai kujira yafito daga office naga kuma Idan a ajin Ku yake bakwa gaya mana Don haka kujira suna cikin haka kuwa saiga yaa shek yafito daga office,
yana takawa cike da kasaita d gayu yana goge fiskandhi da wani Brown hankacif da alama alwala yayi ayko suka bishi da ido

Afilin makarantar d'aluban sukeyin sallah Don haka tako ina dalubai ne suna jira atayar da sallah

Yaa shek matashi ne mai shekaru ashirin da bakwai 'Dan gayu ga tsafta uwa uba ilimin addini da na boko masanin hadisai da littafan addinin islama ya gama degree dinshi a usman dan fodiyo university sokoto ya karanci 'bankaran hadisai da zamantakewar aura tayya hakan ne yasa hukumar makarantar suka bukaci yadinga yima d'aluban da zasuyi sauka lecture duba da yadda aure yake mutuwa da wuri a wannan zamani Don haka d'aluban keson ya shiga ajinsu saboda yadda Yaa shek yake warware musu zare da abawa ga daukar wanka,
wasu daga cikin daluban sonshi suke wasu kuma burgesu yake ajin yan sauka guda biyu ne Don haka yau idan yashiga daya gobe sai ya shiga daya cikakken sunan sa kuwa Abdallah Gaddafi a makaranta ne d'alubai ke ce mai Yaa shek batun aykin gwamnati kuwa yana nema saidai har yanzu shiru,

Sauri sauri suke saboda su koma bayan kowa ya hallara saiga Yaa shek yashiko yana shikowa duk suka nutsu sabada sun san bayason hayaniya kuma yana iya korar mutun

Bayan yadai daita zaman shi ne a kan bench din ne yace kundai San dokokina ko?kuma kunsan hukuncin Wanda yasaba min Don haka ba bukatar na mai mai ta suka hada baki wazen fadi na'am yaa shek

ya nisa ya cigaba da bayani daga inda ya tsaya jiya.

Baki iya hiraba baki iya kwalliya ba baki iya shagwa'ba ba baki iya komai ba kuma kina korafi wai lado baya dawowa gida da wuri to taya zai dawo d wuri bayan in ya dawo d'in ma yasan kayan haushi zai gani,
kuna kallo a tb an nuno wani dan wasan kince wai ke wannan gayan yana burgeki duk a gaban lado yo ba lado ba ko ni ne sai na shanbe ki ina mijinki kice wani yana burgeki agabana ta yaya kuke tunanin aure bazai mutuba?

duk yana maganane yana kallon gurin d 'yan matan ke zaune Don dasu yake, kafin ya dawo da kallonsa gurin mazan yana mai cewa

"kai kuma lado baka iya siyan brush ba baka iya shiyan acuci maza ba baka iya siyan kayan kwalliyaba inzaka shigo gida kazo rannan abace, kana tsamin daud'a kashige gansan gansan ba fara'a,tayi tayi da kai kayi wanka kace kai baza kaiba sannan kuma kazo kana mata Yar murya idan dare ya tsala"

ayko duk d'aluban dariya suka sa kasa kasa Don kar yajisu,
haka tsarinsa yake yayin lecture idan zai bada misali akan namiji sai yace lado idan mace ce sai yace kande ,

shikuwa ko ajikin sa da irin wannan Jan hankali da nasihohi lokacin tashi yayi yayi musu addu'a ya fita sannan d'aluban kowa ya watse,
saida yashiga office y dauki littattafan sa sannan ya kama hanya yayi gida.
[21/04, 9:59 a.m.] Shooly: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*_YAA SHEK!!_*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*BY:U.K.Y. for real*😘

🌈 *kainuwa writers asso*🤝🏻

*_dedicated TO mmn khaery_*🤝🏻

5⃣to1⃣0⃣

Z,aune suke a tsakar gidan nasu, ummee da abdulmalik da abdul majid suna kan tabarma,

Shi kuwa yaa shek yana gefen su akan wata katuwar sallaya, waya ce a hannun shi yanajin wa'azin Dr Zakir Naik,

Ummee ce ta kalleshi tace Abdallah wai baza kaci abincin bane?

Nace a kawo ma abinci kayi shiru,

ummee nah zanci mana,

ay nazata baza kaci bane da naji kayi shiru, abdulmalik jeka ka dauko mai abincin shi ya nanan a flas sai ka dauko cokali d flet,

Kawo masa abincin yai gaban sa ya ajiye ya koma ya zauna,

dago kai yayi ya kalli k'annan nasa wato su abdulmajid,sannan yace "wai kuwa ma kunyi hadda ne kukazo kuka zauna kuna wa muta ne surutu?"

Nidai nayi inji Abdulmalik, shi kuwa abdulmajid cewa yayi ni saida asuba zanyi yaya Abdallah wlhy idan nayi yanzu ba zai zauna ba,

umme ce tace bazai zaunaba?! dama bakaso yazauna ba ne. sai asuban tayi Ay ta tashinka kaki tashi makaryaci, wai saida asuba kamar da gaske,

Shidai Abdul majid bai sake cewa komai ba don bayaso a ja zancen da yawa ga ya Abdallah agurin, yasan Zane mai jiki zaiyi don ya Dade da fuskantar ya abdallah 'kyaleshi kawai yakeyi amma yasan sarai ba kararun yakeba.

Acikin su ukun Abdul majid ne yake da wasa ba shida maida kai a karatu, amma alamu sun nuna Abdul malik zai biyo hali irin na yayan nashi wato Yaa shek.

Shima Abdallah shiruyayi da kudurin zai gyarawa yaron nan zama a zuciyar shi,

Suna zau nan ne kowa yayi shiru suka jiyo kuka a ma'ko tansu, da suke Katanga d'aya da su, wato gidan kanin babansu baffa usman mai rasuwa

ihu take tana kiran yayyo ummee nah wayyo yaya Abdallah nah kuzo kutai makeni nidai wlhy bazan ci ba,

Ummee ce ta ce ikon Allah waye kuma yake dukan min yarinya a cikin daran nan?

Abdul majid ne yana dariya. yace wlhy ba wani duka in kin bibiya ma'kiyin ta akace taci wato tuwo shine take wannan ihun
kamar ana yankata, sai kace bakusan halin *Jidda* ntaku ba,

Wlhy kuwa inji Abdul malik yana 'kyal,kyala dariya shima

To ay sai a 'kyalemin yarinya ko a dafa mata indomie din nata data keso ko? Yariyar nan da gaske take batason tuwon nan tunda idan tacima sai tayi aman sa don haka sai a kyale ta, kai Abdul malik jeka ka gani mene ne idan tuwan ne baza taci ba ka kawo min ita ga abincin yayan kunan tunda bai ciba sai a d'iba mata,

Yaa shek da tunda yajiyo ihun Jidda ya kasa kunne yanaso ya gane me take cewa don yasan dalilin kukan nata don in akan cin tuwo ne bazai sa baki ba ace yarin ya wai baza taci tuwo ba sai kace ba mace ba ay halin rayuwa ake gudu idan babu halin a dafa mata abinda ranta yakeso to ayi yaya kenan?

amma duk da haka bazai iya jure jin kukan nata ba saboda bai son kuka balle ma kuma kukan Jidda Yar rigima,

Kai abdulmalik zo kazauna bari na dubo ummee, yawwa Abdallah zeka kaji.

Yana fita ya fad'a gidan yayi sallama sai da aka amsa akai mai izini sannan ya shiga, (abunka da masu koyi da koyar war annabi Muhammad wato sunnah)

Kafin ya gama shigowa Jidda tayi maza tayi gunsa tana shashshe'kar kuka tana ajiyar zuciya kamar wadda akaiwa dukan kawo wu'ka,

A'a baba na Kaine kunjiyo kukan wannan ja'irar ko?

Samu guri kazauna tana nunamai tabarma, zama yayi sannan ya gaishe ta,

Kaga baba nah wlhy ko yatsa ban d'ora a kantaba kawai tuwo na bata nace ta ci shine take wannan ihun tafiso idan na dafa tuwan na dinga bi makota ina asanmin abincin na bawa Jidda ko kuma in nemo mata wani abun, duk da ita yarinya ce amma ay kullum girma take kuma koba dad'e ko ba jima. gidan wani zata.

Hakane mamy kiyi hakuri sai a hankali zata ci ne, yadaga kai ya kalli Jidda da ta make kafad'a ta cuno baki Dan bakin nan mitsil dashi alamun ba
ranar da zata ci tuwan ,

yace ke, to sami guri kizau na, ayko ta bare mai baki zata Dora a inda ta tsaya,
Chapter 1 · 0% Book details