← Book details Wani Sharrin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 8 OF 11

Chapter 8

Wani Sharrin Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Inna tana shigowa ta cakumi hijjab ɗin jikin Mamy tana cewa.
"Wannan wani irin cin amana ne, ranar girkina kin tasa miji a gaba kina bashi abinci, ko gidan ku ba a kaiki islamiyya bane."

"Ai kowa ya kalleni ya kalleki ya san wacece ba taje islamiyya ba a cikin mu, ko kin manta ilimi baya ɓuya a duk inda yake." Mamy ta faɗa tana ƙwace jikinta.

Baba yana zaune yana cin abincin shi.
"Mai dattin hula bai yi karatu ba ballantana mai dattin ɗan kwalli." Inna ta faɗa kamar zata kai mata duka.

"Shi ya sa mai dattin hulan ya ƙare a karen ɗan siyasa." Faɗin Mamy tana shirin barin gurin, Inna jin cin mutuncin data faɗa yasa ta kai mata mari, kafin ta sauke hannu Mamy ta mayar mata da mari biyu.

Baba da ya gama cin abinci da sauri ya miƙe, ya kamo Inna ya fita da ita Mamy tayi tsaki tana rufe ƙofar ɗakin ta.

Inna cike da mamaki take bin shi da kallo har suka shiga ɗakin shi.
"Haba dan Allah Talatu nazo ki bani abinci kin hana, naje an bani abincin kin zo kin fara ɓarnar hali kamar yanda kika saba, wai dan Allah sai yaushe zaki yi hankali.?"

"Sai ranar daka zama na miji mai gaskiya da adalci." Ta faɗa tana fita daga ɗakin.

Baba ya yi shirin bacci ya kwanta ya bar ɗakin a buɗe domin ya san halin Inna komun dare sai ta dawo.

Inna sai da ta gama gayawa yaranta abin da ya faru, sannan ta dawo ɗakin Baba ta kwanta.

Washegari daman kowa tana yin abin karyawane ita da ƴaƴanta, idan ranar girkin tane zata yi da miji.

Yusra da Aysar sun dawo daga hadda suna shigowa, Zainab ta kama su ta zane Yusra Aysar na ganin haka ya zura da gudu har yana cin tuntuɓe, Mamy na toilet tana wanka, taji ihun Yusra ta ɗauko zani ta ɗaura ta fito a daidai Zainab ta kai mata duka a baya taji an riƙe hannun an murɗe, ta saka ihu tana kururuwa.

"Wallahi wallahi duk ranar da hannunki ya ƙara kai wa jikin ƴaƴana sai na yi miki mugun duka." Mamy ta ce tana yarfar da hannun, ta riƙo ƴarta suka nufi ɗaki.


"Wannan wani irin zalunci ne? Ko dan kinga basa ramawa idan kika dake su shi yasa kike yawan kai hannu jikin su." Mamy bata saurari zan cen da Inna take yi ba ta shige ɗaki wankan da bata ƙarasa ba kenan.


Kamar yanda Inna ta faɗa a rama mata kwana bakwai ɗin data ƙara, sai da aka rama mata sannan aka zauna lafiya, Mamy ta samu Baba da maganar tana son ta kira ma'aikata su fitar mata da toilet a cikin bedroom ɗin ta, ya yi shiru bai ce komai ba har ta gama magana ta fita.

Bayan kwana biyu da maganar Baba ya ɗauko ma'aikata, daman gidan akwai fili sosai aka shigo da filin bayan ɗakin Mamy aka fitar mata da toilet, sannan aka gina mata ɗan ƙaramin kitchen.


Bayan an gama itama Inna aka yi mata kamar yanda na Mamy yake, amman bai gina mata da kitchen ba ya ce ta ɗauki na tsakar gidan ta ringa amfani dashi, babu hayaniyya ko tashin hankali Inna ta amince domin kitchen ɗin tsakar gidan babbane.


Bayan wata biyu cikin Mamy ya shiga wata na shida, Inna ta shiga tashin hankali lokacin data yi ido biyu da cikin, kuma tun daga lokacin ta fara neman hanyar da zata illata Mamy.

Ajwa zaman dai Alhamdulillahi ammanfa maganar yawo bata daina ba, duk da cewar ba kullum take fita ba amman wani lokacin yana fita take ficewa, Mama tun tana magana ta kawo ido ta zuba mata, domin tana yin magana akan ɗanta komai yake ƙarewa.


Yau da sassafe Sa'idu ya fita Ajwa data ke jiran fitarshi itama ta fice, bai jima da fita ba ya dawo gida yana dafe kai, yana kallon ƙofar ɗakin yaga alamun ta fita cike da mamaki yake ƙara kallon ƙofar da kyau.

Da ya gaji da tsayuwa ya zauna a bakin ƙofa yana sauke numfashi a hankali, Mama data ji motsin shigowar shi ta nufo gurin tana tambayar shi ko lafiya.


Sa'idu ya ɗago jajayen idanunshi ya zuba wa Mama ido, da sauri ta riƙo hannun shi tana tambayar shi bai da lafiya ne Sa'idu ya kasa magana.


Ta taimaka mishi ya miƙe ta nufi part ɗin ta dashi, a saman doguwar kujera ta kwantar dashi ta ɗauko ƙaramin roba da ruwa a ciki, ta samu ɗan kwallin kayanta ta tsoma ta ringa matsa mishi a saman kai, a hankali ya ringa sauke ajiyar zuciya.

Sai da taga ya fara dawowa cikin hayyacin shi, sannan ta zubo mishi faten dankalin turawa ɗan kaɗan yasha ya kau da kai, maganin zazzaɓi ta ɗauko ta bashi yasha bai jima ba ya yi bacci.

Sa'idu sai azahar ya farka lokacin babu zazzaɓin sai dai rashin ƙarfi, a toilet ɗin parlourn ya yi alwala Mama ta shimfiɗa mishi darduma ya yi sallah.

Har bayan sallar magrib Sa'idu yana tare da Mama, kuma sai a lokacin Ajwa ta dawo shima dan tana tsoran Sa'idu ya riga ta dawowa ne.


Kuskus ta dafa daman tana da miya tayi wanka ta zauna tana jiran Sa'idu, har bayan sallar isha'i bai dawo ba cike da mamaki take duba lokaci domin ta san bai saba kaiwa dare a waje ba.

Data ga ƙarfe goma daidai ta miƙe ta nufi part ɗin Mama cike da tunanin yanda zata kasance tsakanin su.

Da takalmin Sa'idu ta fara cin karo a bakin ƙofa, Ajwa ta lallaɓa ta cire takalmi ta leƙa window ɗin parlourn Sa'idu yana kwance yana bacci a saman kujera Inna tana zaune a saman darduma tana lazumi.

Tayi ƙwafa tana fita daga part ɗin tana shiga ɗaki ta kulle tayi kwanciyar ta, Sa'idu bai farka ba sai sha biyu saura ya miƙe yana salati.


"Ya kake jin kan naka yanzu.?" Inna dake zaune saman darduma ta faɗa.

Sa'idu ya ce.
"Da sauƙi sosai."

"Ka tafi part ɗin ku idan Allah ya kaimu inada magana da kai." Mama ta ce tana mayar da hankalinta gurin Qur'anin dake gefenta.

"Allah ya tashe mu lafiya." Sa'idu ya faɗa yana fita daga ɗakin.

Sa'idu ya jima a bakin ƙofa yana ƙwanƙwasawa amman shiru, ya kira wayarta yaji a kashe kuma yana tsoran ya buga da ƙarfi kar Mama taji, ganin babu mafita yasa ya fara kiran sunan Ajwa, tana jinshi tayi banza dashi sai da ya kusa yin awa ɗaya a tsaye sannan yaji maganarta tana cewa.
"Dan Allah baku ji kunyar kanku ba, ace mutum da matarsa amman kin hana shi zuwa wajenta, saboda shegen sa ido da gulma."

Sa'idu ya ce.
"Ajwa na rantse da Allah idan baki bar wannan maganar ba na shigo sai ranki ya yi mugun ɓaci." Ya faɗa yana jin kamar ya kamata ya yi mata mugun duka.

"Ƙofa dai ba zan buɗe ba, wallahi sai dai ka koma ka kwanta a can." Ta faɗa tana komawa bedroom.


Sa'idu ya dafe kai cike da takaici, da sauri ya dafa aljihun shi makullayen shagon shi ya ciro daman akwai na ɗakin a ciki, kuma yaga alamun ta kulle da key ne ta ciki.


Yana gwadawa ƙofar ta buɗe ya faɗa ɗakin a fusace.


Free pages sun kusa ƙarewa.

Ta Batulu ce ✍️.................*WANI SHARRIN*
(Mutum ke nemowa kansa)


Channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029Vb6Kd5SFnSz8T3XpQ22g


*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION (J.W.A)*


*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA*


*ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYADINA MUHAMMAD WASSALIM*


Written by ✍️
Sa'adatu Ta Batulu
(Jagabar Jajirtattu)


Bismillahir Rahamanir Raheem.
Chapter 8 · 0% Book details