← Book details Wani Sharrin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 5 OF 11

Chapter 5

Wani Sharrin Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ajwa tana shigowa a daidai Aysar ya miƙe zai ɗibo ruwa, ta ture shi ya faɗi  a kai rashin saa ya faɗi akan hannunshi, hannun sai da ya yi ƙara.

Da sauri Yusra ta miƙe tana kuka ta zura da gudu zuwa room ɗin Baba.

Ajwa tayi tsaki ta shiga room ɗin Inna ko sallama, Baba ya fito Yusra na bin bayan shi.

Aysar na kwance yana kuka Baba ya ɗaga shi, ƙarshe dai sai da aka kai Aysar gurin mai ɗaurin karaya.

Aysar sai da ya suma saboda azaba Yusra sai kuka take yi, bayan an gama ɗaurin hannun Baba ya dawo dashi gida.

Baba ya tambayi Yusra garin yaya hakan ta faru.
"Aunty AJ ne ta ture shi ya faɗi." Yusra ta faɗa a tsorace.

Baba ya tashi rai a ɓace ya nufi ɗakin Inna, yana sallama ya fara faɗa kamar zai haɗa su ya dake su.
"Wannan zaluncin har ina, daga zuwanki gida kin kama yaro kin karya shi saboda mugunta." Baba ya faɗa cike da takaici.
Dukanninsu babu wanda ya motsa ballantana ya yi magana.

"Kuma kizo ki gaya mun abin da ya kawo ki gida, bayan ko wata ɗaya ba kiyi a gidan miji ba." Cewar Baba yana fita daga ɗakin.

Ajwa durƙushe a gaban Baba tana kuka.
"Wallahi idan baki gaya mun abin da ya haɗaki da mijinki ba, sai na ɓata miki rai a gidan nan, mutum ya girma amman har yanzu babu hankali, daga zuwanki gidan ma sai da ya san kin dawo saboda masifarki." Baba ya faɗa yana jin kamar ya rufe ta da duka.

Ajwa ta buɗe baki zata yi magana Baba ya ɗaga mata hannu yana faɗin.
"Ki tabbata duk abin da zaki faɗa babu ƙarya a ciki, domin kin sanni kamar yunwar cikin."

Ajwa ta faɗa mishi yanda suka yi da Sa'idu sannan ta ce.
"Mahaifiyarsa take zuga shi duk abin da yake yi, kuma bata son a faɗi laifinsa."

"Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un." Abin da Baba yake ta maimaita wa kenan, domin yama rasa abin da zai ce mata.

Baba ya yi mata nuni da ƙofar fita yana shiga toilet, shi wallahi masifar Ajwa ta fara isar shi, yarinya kamar rainon sheɗan.

Washegari Baba yaje ya samu ƴan uwanshi da maganar Ajwa, domin suje gidansu Sa'idu biko, sun ajiye magana zasu je bayan sallar la'asar Baba daga nan gidansu Mamy ya wuce.

Mai gadi ya shigar dashi parlourn gidan bisa umarnin Hajiya,  Baba yana zaune kamar munafuki ya nata raba ido.

Mamy tayi sallama ta shigo Baba ya zuba mata ido cike da kewarta, Mamy ta gaishe shi bayan ta zauna ta ɗaure fuska.

"Dan Allah ki manta da abin da ya faru ki dawo ɗakin ki, ko domin yaranki." Baba ya faɗa yana yin fuskar tausayi.

"Daman da yara kowa yake fakewa domin ya cutar da kai, to wallahi ni har cikin zuciyata na haƙura da zaman aure dakai, yara kuma Allah zai raya su a gidan ubansu." Mamy ta faɗa tana shirin barin parlourn.

Baba ya yi saurin cewa.
" Wallahi idan babu ke yaran nan ba za su iya rayuwa ba, dan Allah kar ki yanke musu jin daɗi."

"Wallahi sai dai su mutu ko kuma ni in mutu, akan dai in koma gidanka in cigaba da rayuwa, dan Allah ka tashi ka tafi kawai domin babu sasanci a tsakanin mu, zaman aure ya haɗa mu da kai kuma yanzu babu wannan auren, to ka bari muyi rabuwar mutunci." Mamy ta faɗa tana barin parlourn.

" Yanzu haka Aysar ya karye a hannu, Yusra kuma ba zata iya jinyar karaya ba." Baba ya faɗa cike da yaƙinin Mamy zata sauko, amman sai yaji tana faɗin.
"Ka kawo mun shi, in yi jinyarsa a nan idan ya warke sai ya koma gida." Mamy ta shige bedroom tana fashewa da kuka, tayi kewar yaranta kuma tana muradin ganinsu, amman bata buƙatar cigaba da zaman aure da ubansu.

"Ki zauna kiyi tunani akan goben ƴaƴanki." Hajiya ta faɗa tana miƙa mata ruwa mai sanyi.

"Tsawon lokacin nan ban taɓa zuwa na gaya muku, halin da nake ciki ba Hajiya dan Allah karku ce dole sai na koma gidan shi." Mamy ta faɗa tana dafe kai.

"Wallahi ba zan taɓa yi miki dole ba, amman ina son ki zauna da kanki kiyi tunanin makomar rayuwar ƴaƴanki, kafin ki yanke hukunci kiyi tunanin yanda goben yaran zata kasance." Hajiya ta faɗa tana fita daga room ɗin.

Baba ya koma cike da damuwa domin bai taɓa tunanin Mamy zata ƙi amincewa ba, amman ya yi alƙawarin wallahi duk inda zasu je sai dai suje amman ba zai taɓa sakin taba.

Yana shiga gidan ya ƙara cin karo da wani sabon tashin hankalin, Ajwa ne take ta dukan Yusra ƴan uwanta na ƙara zuga ta.

Ganin basu lura da tsayuwar shi ba kuma tana cigaba da dukanta, ya yi gyaran murya.

    Da sauri ta yar da bulalar tana sosa kai Baba ya miƙar da Yusra yana share mata jikinta, Baba ya kalli bakin Yusra da ya fashe yana jini, ruwa ya ɗauka ya wanke mata bakin suka nufi ɗakin Mamy.

Aysar na ganin Yusra ya fashe da kuka yana faɗin.
"Ni dai ki kaini gurin Mamy na."

Baba ya zauna a tsakiyar su yana rarrashin su, shima lamarin gidan nan wallahi ya fara isar shi, mafita kawai yake nema domin ya gaji.

Sai da ya tabbatar da sunyi shiru sannan ya tambaye su ko sunci abinci, Yusra ta faɗa mishi basu ci komai ba tun safe.

   Baba yaji damuwar shi ta ƙara zama sabuwa, domin shi bai da labarin duk abin da yake faruwa.

Cike da dubara ya ringa tambayar yaran duk abin da ke faruwa a gidan, Aysar ya faɗa mishi komai, Baba jin irin abubuwan da yaran ke fuskanta yasa shi jin ƙwarin gwiwar mayar da Mamy ɗakin ta, ko ba dan komai yaran suna buƙatar kulawarta.

Baba ya fita ɗakin ya tsaya a tsakar gida yana kiran yaran gaba ɗaya.


Ta Batulu ce✍️............................ 08138098887 WhatsApp only*WANI SHARRIN*
(Mutum ke nemowa kansa)


Channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029Vb6Kd5SFnSz8T3XpQ22g


*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION (J.W.A)*


*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA*


Written by ✍️
Sa'adatu Ta Batulu
(Jagabar Jajirtattu)


*ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYADINA MUHAMMAD WASSALIM*
Chapter 5 · 0% Book details