Chapter 7
Wani Sharrin Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Mamy ta dafe ciki tana jin zuciyarta kamar zata fashe, Hajiya ba zata fahimci irin rayuwar da take fuskanta a gidan aurenta ba, kuma ba zata iya faɗa musu halin da take ciki ba, koba komai shiɗin uban ƴaƴanta ne.
Ganin tunanin babu mafita ta fita ta aiki yarinyar dake musu wanke wanke, ta siyo mata PT.
Ba a jima ba ta dawo da aiken da akai mata Mamy ta karɓa ta shiga toilet, tabbas ya nuna mata jan layi, amman bata yarda ba.
Haka ta yini cike da fargaba da tashin hankali, bayan kwana biyu ta shirya ta tafi hospital gwajin farko ciki ya bayyana a jikinta watan shi huɗu, hankali tashe ta dawo gida domin ta san komawarta gidan Abban Yusra ya zama dole.
Tana shiga parlour ta fashe da kuka tana ɗaura kanta a jikin Hajiya, Isma'il babban yayansu ya karɓi takardar hannunta, ita dai Hajiya tana zaune tana murmushi domin ta fahimci dalilin kukan.
Yusra ta shigo parlourn bakinta ɗauke da sallama Mamy tayi saurin share hawayen fuskarta tana murmushin da yafi kuka ciwo, Hajiya ta umarce ta su shiga daga ciki za suyi magana da Isma'il.
Bayan kwana uku da ƙyar Mamy ta koma ɗakinta, Hajiya ta siya mata fridge da keken ɗinki Isma'il ya yi alƙawarin sanja mata kayan ɗaki, a ranar data koma Baba ya tasa Ajwa a gaba ya rakata gidan mijinta, domin ya san in dai ya barta a gidan to wallahi za a samu matsala domin Mamy bata ɗaukar iskanci, akwai lokacin data zagi Mamy ta kamata ta zane ta aka ringa rikici da ƙyar ya shawo kan matsalan.
Daƙyar mahaifiyar Sa'idu ta haƙura shima wallahi saboda ganin idon Baba ne, ko mutuwa na kunyar ɗa da mahaifi, Ajwa ta duƙa ta nemi gafararta kamar yanda ya umarce ta.
Bayan ta bata haƙuri ya tasata har ɗakinta yana rarrashinta, domin Ajwa sai rarrashi bata jin faɗa hasalima idan kayi mata faɗa akan abu gobe sai tayi wanda ya fishi, tayi mishi alƙawarin zaman lafiya da mijinta yaji daɗi sosai yana ta saka mata albarka.
Koda ya bar gidan Ajwa gurin ƴan uwanshi ya nufa ya faɗa musu abin da ya faru har tafiyar Mamy gida, suka ringa mishi faɗa suna nuna mishi kuskuren shi, sun jima suna fira sai da akai sallar magrib da isha'i sannan ya nufo gida.
Ya leƙa bedroom ɗin Inna suna zaune suna cin abinci, ya fita ya leƙa Mamy tana zaune tana karatun Qur'ani Yusra na rubutu Aysar na game, ya shigo ya zauna kusa da yaran suna fira Mamy ta yi addu'o'i ta shafa.
Ba a jima ba yaran su kai bacci ta ɗau Aysar ta shiga dashi Baba ya ɗau Yusra ya bita, bayan sun kwantar dasu Mamy ta zauna tana shafa cream daman wanka ta fito, yana tsaye yana musu addu'a yaji ƙamshi mai daɗi yana ratsa zuciyarsa, ko kafin ya juyo Mamy ta hau gadon ta kwanta a gefen su.
"Banganeba." Ya faɗa cike da mamaki.
Tayi kamar bata ji abin da ya faɗa ba ta janyo blanket ta rufe musu jiki tana addu'ar bacci.
"Dan Allah kar muyi haka dake haba matar kirki, matar aljanna." Sai dai kuma har ya gama magana bata motsa ba, ganin hakan ya nufo hanyar fita daga room ɗin yana cewa.
"Ki dafa mun Lipton yanzu ki kawo mun." Ya faɗa yana fita da sauri, Mamy ta dafe kai cike da takaici ta gyara kwanciya tana ƙara rufe jikinta.
Kamar ba zata tashi ba ta miƙe tana tsaki tana cewa.
" Ni wallahi bana son damu, baccin ma baza a bari mutum ya yi cikin kwanciyar hankali ba."
Ta haɗa Lipton kamar yanda ta san yana buƙata, ta ɗauko hijjab ta ɗaura a saman sleeping dress ɗin jikinta, kofar ta kulle ta nufi room ɗin Baba.
Yana ganin shigowar ta ya karɓi cup ɗin hannunta yana jin ƙaunarta na ƙara ratsa sassan jikin shi, ganin tana shirin juyawa ya riƙo hannunta ya zaunar da ita, ya fara magana cike da rarrashi da kulawa.
"Ni dai ban san ta inda zan fara ba, domin na san ni mai laifine a gurinki, dan Allah dan Annabi kiyi haƙuri karki ce komai, kuma in sha Allah daga wannan lokacin hakan ba zai ƙara faruwa ba."
Gaba ɗaya ya riga ya ɗaureta da jijiyoyin jikinta, ba dan ta amince da hakan ba ta nuna mishi komai ya riga ya wuce, Mamy a ɗakin ta kwana.
Bayan sati ɗaya da dawowar Mamy suna zaune lafiya da mijinta, daidai gwargwado tana kawar da kai a lamarin yaran shi kuma hakan ya yi mishi daɗi sosai, sai dai kuma a ranar Inna ta dawo satin ta uku a can.
Yaran sun yi murna sosai ganin mahaifiayarsu, bayan ta huta taci abinci suka fara bata labarin abin da ya faru, tunda suka fara magana take murmushi har suka gama, Mamy tayi sallama ta tsaya daga bakin kofa suka gaisa da Inna tayi mata ya gajiyar hanya, daga haka ta koma ɗakinta Inna ta bita da kallo cike da tuhuma.
Da daddare Baba ya dawo gida cike da farin ciki, amman ganin Inna a tsakar gida yasa yaji gabansa ya faɗi, Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un haka yake ta mai mai tawa har ya samu natsuwa.
Ina tayi dariya tana yi mishi barka da zuwa ta amshi ledar hannunshi ta nufi room ɗin shi, Baba ya saki baki da hanci yana kallon ikon Allah.
Ɗagowar da zai yi suka haɗa ido da Mamy dake fitowa daga toilet, daman akwai hutar nepa, tayi murmushi tana wucewa ta gabanshi, ƙamshin turaren ta ya yi mishi sallama ya lumshe ido cike da muradin matarsa, sai dai kuma ya san hakan ba abu ne wanda zai yiwu ba.
Ganin tsayuwar ba zata fishe shi ba ya nufi room ɗin shi yana waigen Mamy data jima da shiga ɗaki.
Inna tana zaune tana kallo a TV ya yi sallama ya shigo, yana shigowa tayi mishi barka da zuwa sannan ta ce.
"Na haɗa maka zoɓo irin wanda kafi so." Tana gama faɗa ta fita.
Baba ya juye ruwan flask ɗinshi ya yi wanka, har ya gama ya fito Inna bata shigo ba ya samu kaya marasu nauyi yasa ya zauna yana ƙure gudun fanka, lokacin zafi ne kuma baya son zafi ko kaɗan.
Inna tayi sallama ta shigo hannunta ɗauke da plate, ta ajiye cups ne guda biyu a saman plate ɗin Baba yana ganin zoɓob yaji yana sha'awar yasha, Inna ta miƙa mishi guda ɗaya tana shirin zama ya tambayeta abinci.
Ta ɓata rai tana cewa.
"Abinci kuma, koka manta yau na dawo garin.?"
"Tunda baki dafa abincin ba kije ki kiramun wanda take da girki ta bani abinci." Ya faɗa yana ajiye cup ɗin.
Cike da takaici da baƙin ciki Inna ta fara magana.
"Wannan ai cin fuska ne da tozarci, ta yaya zaka ce inje in karɓo maka abinci bayan kuma na karɓi girki."
"Ikon Allah." Baba ya faɗa cike da mamaki.
"Wallahi babu abincin da zanje in karɓo maka, kuma dole a rama mun kwana bakwai ɗin dana ƙara."
"Wai dan Allah Talatu kina da hankali.?"
"A'a ban dashi sai dai ka bani naka." Baba ya fita daga ɗakin Inna tayi ƙwafa tana cewa.
"Wallahi duk inda zaka je zaka dawo ka same ni."
Room ɗin Mamy ya nufa ya ƙwanƙwasa yana faɗin.
"Raliya." Mamy jin muryanshi ta buɗe ƙofar daman tana zaune ne tana karatun Qur'ani.
"Akwai abinci ki bani.?" Baba ya faɗa yana zama a kujera.
"Eh akwai." Ta faɗa tana janyo flask ɗin abincin shi, daman tayi girkin gaba ɗaya na gidane sai bayan ta gama girkin ta fahimci nufin Inna shi ya sa ma bata kai mishi abincin ba.
Ta zuba mishi shinkafa da miya ta buɗe fridge ta ciro jug mai ɗauke da zoɓo, Baba ya yi bismillah yana cika bakin shi da abinci, ya kusa cinyewa suka ji an daki ƙofar da ƙarfi kamar za a karya.
Ta Batulu ce...................... ✍️*WANI SHARRIN*
(Mutum yake nemowa kansa)
Channel 👇
https://whatsapp.com/channel/0029Vb6Kd5SFnSz8T3XpQ22g
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION (J.W.A)*
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA*
Wannan page ɗin sadaukarwa ne ga duk mahaifiyar dake son farin cikin ƴaƴanta.
*ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYADINA MUHAMMAD WASSALIM*
Written by ✍️
Sa'adatu Ta Batulu
(Jagabar Jajirtattu)