← Book details Wani Sharrin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 11

Chapter 2

Wani Sharrin Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ko sallama bata yiba ta faɗa chemis tana faɗin.
"Dan Allah ka taimaka mun."

Mai chemis ɗin ya amshi Yusra ya kwantar da ita a saman wani ƙaramin gado, almakashi ya ɗauka ya yage daidai gurin da jinin ya ɓata, wani abune ya yanke ta a gurin kuma yankar ya shiga sosai.

Dressing ɗin gurin ya yi Yusra ta fashe da kuka tana ƙan ƙame Mamy, sannan ya yi mata alluran pain relief ya bata magani, Mamy sai a lokacin hankalinta ya fara dawowa jikinta, ta tambaye shi kuɗin ya faɗa mata.
"Dan Allah idan ba damuwa wannan yaron ya biyo ni, ya karɓi kuɗin." Mamy ta faɗa tana nuna wani matashi da suke zama tare da mai chemis ɗin.

"Ok badamuwa, Hassan kuje ka amso kuɗin dan Allah." Mai chemis ɗin ya faɗa yana kallon shi.

Mamy ta riko hannun Yusra suna tafiya Aysar na bin su a baya, Baba yana zaune a ƙofar gida ya hango Mamy.

Cike da tuhuma yake bin ta da kallo Mamy tayi kamar bata ganshi ba ta shige gida, bata jima da shigaba ta fito ta miƙa wa Hassan dubu biyar sannan ta koma.

Kayan wanke wanken yana gurin a zube Mamy ta je zata kwashe kayan, ta ga jini a jikin ƙaramin wuƙar data yanka albasa.

Cike da tunani ta wanke wuƙar ta kwashe kayan wanke wanken ta shiga ɗaki, Yusra na kwance tana kuka Aysar yana rarrashinta.

"Daga ina kike.?" Baba ya faɗa shigowa ɗakin.

Mamy ta buɗe baki zata yi magana Baba ya ɗaga mata hannu, ya nufi gurin da Yusra ke kwance a two seater tana kuka.
"Garin yaya hakan ta faru.?" Baba ya faɗa yana duba gurin da aka yaga a kai dressing.
"Aunty Z ta tureta shi ne ta faɗi a saman wuƙa taji ciwo." Aysar ya faɗa yana turo baki.

"Subhanallahi ƙila ko bata lura bane." Baba ya faɗa yana shafa kan Yusra.

"Ɗazun ma ta mareni, kuma ta hanani abinci wai ya ƙare." Aysar ya faɗa yana kallon Baba.

"Biyoni parlourna." Baba ya faɗa yana fita a fusace.

Mamy ta harari Aysar ta fita zuwa parlourn Baba, fyalle ɗaya ne sai toilet amman parlourn yana da faɗi sosai, akwai gado drower saitin kujeru masu ruwan zuma da baƙi.

Baba ya yi sallama ya shigo Inna Zainab Khadijah A'isha suna bin shi a baya, Baba ya zauna kusa da Mamy dake zaune a kujera mai zaman mutum uku, Inna ta zauna a kusa dashi suka saka shi a tsakiyyar su.

"Mai ya faru kika hana Aysar abinci.?" Baba ya faɗa yana tsare Inna da ido.

Saboda abincin bai kai ba shi ya sa ban zuba mishi ba, Inna ta faɗa tana tsare shi da ido, Baba ya yi ƙasa da kai yana jin kanshi na sarawa.

"Gaskiya ba zan yarda da horan yunwa a cikin gidan nan ba, daidai gwargwado Allah ya hore mun abin da zan ciyar da iyalai na, dan haka bana son in ƙara jin an hana wani abinci a cikin gidan nan." Baba ya faɗa yana kau da kai. Inna tayi ƙwafa hararan shi.

"Ke kuma na dawo kanki, mai ya haɗaki da Yusra.?" Baba ya faɗa yana tsare Zainab da ido.

"Zagina tayi shi ne na dake ta." Zainab ta faɗa tana turo baki.

"Bayan kin dake ta kuma kika jefar da ita, ta faɗa saman wuƙa koh.?" Baba ya faɗa cike da ɓacin rai.

Zainab ta harari Mamy tana cewa.
"Ni ban ture ta ba, kawai na dake ta ne saboda ta zage ni."

A fusace Baba ya miƙe ya kai mata mari Inna ta tare.

"Wallahi ba zan ɗauki wannan iskancin ba,  idan mutum zai gyara to, idan kuma ba zai gyara ba zan ɗauki mummunar mataki." Baba ya faɗa yana fita a parlourn.

Ɗaya bayan ɗaya suka fice yaran Inna ta kalli Mamy tayi murmushi ta ce.
"Duk wanda ya ci tuwo dani, wallahi miya yasha." Daga haka Inna ta fita.

Kamar yanda Baba ya faɗa haka ya faru, Inna sai da tayi sati biyu tana girki sannan ta tafi garinsu, da Zainab ta tafi A'isha Khadijah ta bar su a gida domin su ɗauko mata rahotanni abin da yake faruwa.

Bayan kwana biyu da tafiyar Inna Mamy na zaune a kitchen ɗin su tana girki, Khadijah ta shigo zata ɗauki cup ta taka ƙafar Mamy da zata fita ma ta ƙara taka ƙafar.

Mamy ta riƙo hannun Khadijah ta juyo cike da rashin kunya zata yi magana Mamy, ta zabga mata mari sannan ta yi magana cike da gargaɗi da kashedi.
"Wallahi duk ranar da kika ƙara gigin aikata, makamancin wannan abin sai na zane ki a gidan nan, babu wanda zai ƙwaceki, idan kun yiwa yara wannan bai dame ni ba domin na san akwai ko lokacin da baza ku iya taɓa su ba, amman taɓa ni shi ne babban kuskuren da zaki yi a cikin rayuwarki." Daga haka Mamy ta koma gurin da take zaune, ta bar Khadijah buɗe da baki.

Baba ya yi sallama ya shigo Khadijah ta fashe da kuka tana cewa.
"Wallahi ban lura bane, amman dan Allah ki yi haƙuri."

"Mai ya faru." Baba ya faɗa yana ƙarasawa gurin.

"Na taka tane ban lura ba, shi ne ta mareni duk da na bata haƙuri." Khadijah ta faɗa hawaye na zubowa.

"Dan Allah ki ringa haƙuri da yara, tun da ta baki haƙuri to ba sai ki haƙura ba." Baba ya faɗa yana jin haushin Mamy.

"Wannan ne kake cewa yarinya.?" Mamy ta faɗa cike da jin haushin mijin nasu.

"To ba yarinyar bane.?" Baba ya faɗa yana zabura kamar zai kai duka.

"Yarinyar da ko yau akai mata aure zata zauna, ita kake kira da yarinya.?" Mamy ta faɗa tana sauke girkin data ji ya fara kamawa.

"Daman an jima ana gaya mun kin tsani yara na ban yarda ba ashe da gaske ne, wallahi ba zan lamunci wannan zaluncin ba." Ya faɗa yana shiga parlourn shi.

Khadijah tayi murmushi tana cewa.
"Allah ya ƙarawa Baba lafiya da nisan kwana."

Daga haka tayi gaba tana juya jiki, Mamy dariya abin ya bata, domin lamarin mijin nasu da ƴaƴanshi ba yau ta saba gani ba, amman kullum sabon abu take gani a cikin gidan.


Mamy ta aiki Aysar ya ya karɓo kwanon abinci, Aysar ya dawo yana kuka fuska duk shedar mari.

Mamy bata ce komai ba ta zaunar dashi, ta rarrashe shi.

Ta ɗau plas mai ɗan girma a kwandon Inna ta raba abincin kamar yanda aka saba, ta ɗau plas ɗinta dana Baba ta shiga ɗaki, bayan ta ajiye kayan abincin ta fito ta tsaya a bakin ƙofar ɗakin Inna ta ce.
"Khadijah kizo ki ɗau abincin ku." Mamy taji shiru kuma gashi tana jin firan su, sau biyu tana magana jin basu amsa ba ta tafi abin ta, domin bata jure rainin wayyau.


Bayan sallar azahar Baba ya dawo gida, A'isha da Khadijah suna zaune a tsakar gida.
"Kunci abinci.?" Baba ya faɗa yana shiga ɗaki.

Khadijah tabi bayan shi.


Ta Batulu ce.........✍️*WANI SHARRIN*
Mutum ke nemowa kansa


Channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029Vb6Kd5SFnSz8T3XpQ22g


*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
*(J.W.A)*


*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA*


Written by
Jagabar Jajirtattu

Allahumma salli ala sayyadina Muhammad wassalim.
Chapter 2 · 0% Book details