← Book details Wani Sharrin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 4 OF 11

Chapter 4

Wani Sharrin Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Akwai motoci guda uku ajiye a rumfar, Mamy ƙaramin part ɗin ta nufa ta ƙwanƙwasa, ta jima tana ƙwanƙwasa ƙofar sannan taji alamun tafiya.

Kyakkyawar dattijiya ce ta buɗe ƙofar tana tambayar waye, tana buɗe ƙofar taci karo da Mamy tsaye da akwati.

Mamy ta rungume mahaifiyarta  tana share hawayen daya zubo mata.

Dattijiyar ta riƙo hannun ta suka shiga ciki Mamy na janye da akwatin kaya, a parlour suka zauna.

Mamy ta ɗaura kanta a jikin mahaifiyarta tana cewa.
"Hajiya dan Allah karki tambayeni komai."

Ruwa ta ɗauko mai sanyi ta miƙa wa Mamy ta ce.
"Sha ruwa kije bedroom ki kwanta."

Mamy ta shanye ruwan ta nufi ɗaya daga cikin bedrooms ɗin dake parlourn.

Bayan kwana biyu da tafiyar Mamy Yusra da Aysar, sun zama marayun ƙarfi da yaji duk wani aikin gidan yaran ke yi, gashi sun hana su zuwa makaranta, Baba kuma baya zama a gidan sai dare yake dawowa, kuskure kaɗan duka.

Gidan Ajwa Sa'idu ya dawo daga kasuwa ya samu bata nan, ya shiga part ɗin mahaifiyarshi ya ajiye ledoji guda biyu ya ce ta ɗau ɗaya ta ajiye wa Ajwa ɗaya, har zai fita mahaifiyarshi ta kira shi.
"Kaci abinci.?" Mahaifiyar shi da suke kira da Mama ta faɗa tana tsare shi da ido.

Sa'idu ya yi shiru bai ce komai ba daman magana bata dame shi ba, ganin ya yi mata shiru bai bata amsa ba yasa ta sanja tambayar ta hanyar cewa.
"Ina matar taka take."

"Daman daman." Mama ta ɗaga mishi hannu ta ce.
"Zauna in zuba maka abinci kaci."
Sa'idu ya zauna daman yunwa yake ji, Mama ta zuba mishi abinci yana ci suna fira.

Sa'idu bai tashi ba sai da aka kira sallar magrib ya yi alwala ya tafi masallaci, kuma har lokacin Ajwa bata shigo gida ba, sai da akai sallar isha'i ya shigo gidan kai tsaye ya wuce part ɗin Mama, tana zaune tana lazumi Sa'idu ya yi mata sallama ya ɗau ledar daya shigo dashi guda ɗaya ya fita.

Ajwa na zaune tana lissafin kaya Sa'idu ya yi sallama ya shigo, tayi mishi barka da zuwa tana ɗauko ruwa ta ajiye a kusa dashi.
" In zuba maka abinci.?" Ta faɗa hankalinta na gurin kayan ta.

" A'a na ƙoshi." Sa'idu ya faɗa yana ajiye mata ledar da ya shigo dashi.

"Bangane ka ƙoshi ba." Ajwa ta faɗa cike da tuhuma.

"Saboda naci abinci a gurin Mama kuma na ƙoshi, sai dai ki dafa mun Lipton domin na san babu a plask."  Sa'idu ya faɗa yana kwanciyya a saman kujera.

"Kaje Mama ta dafa maka, tunda har ta iya baka abinci to Lipton ɗin ma sai dai ta dafa maka." Ajwa ta faɗa cike da masifa.

Sa'idu ya ɗauko waya yana dannawa Ajwa haushi kamar ya kashe ta, Sa'idu yana lura da ita amman ya shareta.

Sai da suka zo kwanciyya bacci Sa'idu ya riƙo hannun Ajwa yana cewa.
"Ɗazun na dawo gida bakya nan, kuma baki gaya mun zaki fita ba."

Cike da rashin kunya ta ɗago zata fara masifa, suka haɗa ido da Sa'idu ta kau da kai tana faɗin.
"Kasuwa naje sarin kayan siyarwa, domin na gaji da zaman banza babu sana'a."

"Shi ne bani da arziki da zaki gaya mun zaki je kasuwa, sai dai ki tafi ba tare dana sani ba."
Sa'idu ya faɗa yana matse hannunta dake cikin nashi.

"Uhm nifa bana son ƙorafi wallahi." Ta faɗa tana ƙoƙarin ƙwace hannunta daga cikin nashi, ammman yaƙi bata damar hakan.

"Sau biyu kina fita ba tare da izinina ba, kuma kin san hakan babban kuskurene mace ta fita ba tare da izinin mijinta ba." Sa'idu ya faɗa yana sakin hannunta.

"Shike nan ba zan fita ba idan ya kama, sai ka dawo ka fara ƙorafi, kafi son in zauna a gida sai ka ce wata akuya." Ajwa ta faɗa tana hararan shi.

"Ajwa Ajwa Akwai sau nawa na kira sunanki.?" Sa'idu ya faɗa a hassale.

"Sau uku." Ta faɗa tana tura baki.

"Wallahi idan kika ƙara fita gidan nan bada izinina ba sai na ɓata miki rai, domin ba zan lamunci wannan gantalin ba." Yana gama faɗa ya shige bedroom ya barta zaune tana ƙananun maganganu.

Haka suka kwanta kowa ya juya wa ɗan uwanshi baya.

Washegari Sa'idu ya bayar da kuɗin cefane ya fita, Mama tayi sallama ta shigo daman jiran Sa'idu ya fita take yi.

Ajwa ta amsa sallamar ciki ciki tana hararan ta, Mama tayi kamar bata ganta ba ta samu guri ta zauna ta fara magana kamar haka.
"A matsayina na uwa wacce ta haifa ta san zafin haihuwa, zan baki shawaran da zata amfaneki." Ajwa tayi shiru tana kallon ta, Mama taci gaba da magana.
"Dan Allah ki daina fita ba tare da izinin mijinki ba, domin Sa'idu mutum ne mai tsananin kishi akan abin da yake so."

"Ƙarata kenan ya kawo gurinki!." Ajwa ta faɗa cike da mamaki.

"Ni ban san abin da ya faru tsakanin ku ba, kawai ina lura da abubuwa da suke faruwa ne, kuma bana jin daɗin hakan shi yasa na ce zan sameki idan ya fita muyi magana dake." Mama ta faɗa tana kallon Ajwa data buɗe baki tana kallon ta.

"Uhm Allah ya raba mu da munafurci." Ajwa ta faɗa tana shigewa ɗaki.

"Lallai yarinyar nan baki da kunya daga faɗa miki gaskiya shi ne zaki kirani da munafuka, to a gurin Talatu na koyi munafurcin mara mutunci wanda bata san arziki ba, wallahi sai na sa Sa'idu ya yi mun maganinki." Mama ta faɗa tana miƙe wa.


"Dan Allah idan ya dawo kisa shi ya rubuta mun takardar saki, ƙarshen dai abin da zaki sashi kenan." Ajwa ta faɗa daga cikin ɗakinta.

Mama tayi ƙwafa tana fita daga part ɗin cike da haushin abin da Ajwa tayi mata.


Da rana Sa'idu ya dawo cin abinci daman kullum a gida yake cin abincin rana, Ajwa na zaune a tsakar gida tana wanke wanke.

Sa'idu ya yi sallama ya shigo Ajwa ta amsa ta cigaba da wanke wanken da take yi, ɗaki ya shiga ya zauna yana jiranta amman shiru babu Ajwa babu labarinta, da ya gaji da zaman sai ya fita tsakar gidan harta gama wanke wanken tana zaune tana danna waya.

"Inata jiranki kizo ki bani abinci amman baki shigo ba." Sa'idu ya faɗa yana ƙare mata kallo

"Baka da labarin yanzu na daina dafa maka abinci a cikin gidan nan.?" Ajwa ta faɗa cike da rainin wayyau.


"Banganeba.?" Sa'idu ya faɗa fuska ɗauke da mamaki.

"Abin da kunnenka ya jiyo maka shi na faɗa." Ajwa ta faɗa tana shiga ɗaki.

Sa'idu zai bita Mama data ke sauraron duk abin da ya faru ta ce.
"Zo muje in zuba maka abincin kaci."

Cike da ɓacin rai Sa'idu yabi bayan Mama kamar yanda ta faɗa, shinkafa da miya ta zuba mishi.

Sa'idu ya kasa cin abincin sai juya spoon kawai yake, domin shi lamarin Ajwa abin tsoro yake bashi.

Mama data fahimci damuwa na son yin tasiri a cikin ranshi ta ringa kawo mishi labarin mahaifin shi, da kuma sauran ƴan uwanshi, a hankali Sa'idu ya cinye abincin duka ba tare da ya lura ba, kawai shafa plate ya yi yaji babu abinci Mama tana ta dariya.

"Tun da an raba girki, saura kuma a raba kwana." Ajwa da tun ɗazun ta shigo ta faɗa.

"Bangane a raba kwana ba mai kike nufi.?" Sa'idu ya faɗa yana jin kanshi na sarawa.

"Jiya ta fanshe ni ta girka maka abinci yauma ta ƙara girka maka abincin, mai ya yi saura da ya wuce a raba kwanan girki a tsakanin mu." Ajwa na gama faɗar hakan Sa'idu ya wanke ta da mari guda uku, yana shirin ƙarawa Mama ta riƙo shi tana yi mishi tsawa.

Ajwa ta fashe da kuka ta fita tana cewa.
"Wallahi tun da ka mareni to ka mari aurenka, domin wallahi na gama zaman aure dakai."

Ajwa ta janyo babban akwati ta haɗa kaya ta nufo gidansu, lokacin Yusra da Aysar na wanke wanke a tsakar gidan.


Ta Batulu ce ✍️..............*WANI SHARRIN*
(Mutum ke nemowa kansa)


Channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029Vb6Kd5SFnSz8T3XpQ22g


Group 👇

https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT


*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION (J.W.A)*


*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA*


*S REZA DATA JOY 30DAYS VALIDITY*

*MTM📶*
1GB-600
2GB_1,200
3GB-1,800
5GB-2,300

*AITEL 📶*
1GB-850
2GB-1,600
3GB-2,440

*GLO📶*
1GB-455
2GB-900
3GB-1,350


Chat 08100785178


Written by ✍️
Sa'adatu Ta Batulu
(Jagabar Jajirtattu)

Allahumma salli ala sayyadina Muhammad wassalim.
Chapter 4 · 0% Book details