Sashe 7
Tawa Ta Sameni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tawa Tasameni1-02 Posted by ANaM Dorayi on 01:20 AM, 20-Dec-15 Under: TAWA TASAMENI TAWA TA SAMENI NA HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Ranar lahdi da daddare sai gasu yaya abubakr sunzo nan muka sha fira, ynxu anty faty ta gama mallake babana sai abinda tace gashi har ynxu Allah bai basu haifuwa ba sai karyar bari,na tausaya ma mahaifina kuma na yi alkawarin sa shi a addua insha Allahu zan kuma roki mama ta barni inje na gaida kakata in munyi hutu mun jima dasu sannan sukayi sallama damu suka tafii,muna shirye shiryen soma jarabawa zango na ukku don shiga SS2 aka yaye mu a islamiya inda mukayi walima a gidansu Amira duk gidanmu ni kadai nayi sauka mami kuma sai shekara mai zuwa don tayi wasa da karatun mama da maman su Amira harda Anty yagana duk sun mana bige bigen abubuwa irin su kalanda da robobi,hankici da sauransu,da zamuyi rabon katin walimar har su yaya Abubkr sai dana bawa Amira nayi mata kwatancen taje takai masu kuma sunxo mani da kyautututukan su inda suka bani waya a kwalinta wai inji babana na amsa cikin fargaba na kai dakin kwananmu na boye shima yaya Sulaiman yazo kuma shine ya dinko mana kayan da muka sa ranar walima nashi gudummuwar kenan wata shadda ce galila mai kyau da hijabai. Sai da komai ya natsa sannan na dauko wayar dasu yaya suka bani na kai ma mama na mika mata leda ta amsa ta gami da tambayar menene a ciki?nace su yaya Abubkr ne suka kawo wai inji babana na fada mata cikin tsoro,ta saki ledar daga tsaye tace ke kuma ki ka amsa to ko menene ma a ciki zan maida musu ni,haka kuwa akayi ta kira yaya Abubkr a waya ta bashi gami da yi mishi gargadin karta kuma ganin wani sako daga babana da sunan wai nawa ne tun daga nan suma su yaya Abubkr din ta daina sakar masu fuska.mun shiga SS2 cikin sa'a da nasara ranar wata jumaa mun tashi daga makaranata na tsaya ina amsar sakon wani littafi da zan amsar ma Amira gun wata yar ajinmu Hauwa aminu don yanxu in tana karantawa nakan zauna ta bani lbr ko ta karanta mani na amsa na isa gurin da Musa yake tsayawa wato direbanmu ban sameshi ba na tsaya nayi sororo can na hango wata yar ajinsu mami don yanxu ba aji daya muke dasu ba ni ina A su suna C na isa gunta sai na tambayeta ko taga su Sa'a?don mami bata zo ba tace mani sun tafi abinsu nayi shiru na kuma ce mata motar tazo?tace ba bus din gidanku ba?na daga kai tace to sun dade da tfy,sai da nayi nisa a tfy kasa sannan wani tunani yaxo mani na tsaida mashin na hau sai da muka zo har kofar gate din mu sannan nace bari na shiga na amso maka kudinka ina shiga harabar gidanmu naga matasan layinmu sun cika a kofar dakin yaya Kabir har da wadanda ban taba ganinsu a layinmu ba,nace a raina ko yaya Kabir ya dawo ne?don ynxu yana bautar kasa ce a Bayelsa na shiga gida na sanar da mama abinda ya faru tace to a nawa ya kawoki?nace 40,ta bani 50na kai mashi a hanyar dawowa cikin gida ne nayi karo da Anty Hadiza dasu Anty Mariya suna dauke da manyan tururuka da kuloli a kai,Bilkisu kuma tana dauke da dauke da plates da cokula ga wani kwando mai dauke da kayan shaye shaye na dube au na kauce a hanya,amma duk da haka sai da anty Mariya ta daka min tsawa ke akuya ban hanya,na matsa musu suka wuce,na shiga ina mamakin wane bako ne yaxo ake mashi hidima haka?bayan naci abinci nayi wanka nayi sallah na shirya cikin riga da siket yan kanti ina zaune a tsakar daki ina yin note sai ga mami da gudu ta shigo tana kwala min kira iman! iman!!na tashi da sauri ina fadin gani nan nace menene?don duk na tsorata sai tace min ki tayamu murna yayanmu ne ya dawo ya bamu waya nayi ajiyar zucya na dungure mata kai nace har kinsa duk na tsorata na amshi wayar kirar nokia yar karama mai murfi gsky ta burgeni sosai nayi mata murna tace su dasu Sa'a iri daya ya sai masu don dama ya sai ma su anty Mariya tun tuni,nace kunji dadin wllh tace muje ku gaisa mana ko zai baki kema na dube ta cikin sauri nace ki rufa mani asiri ai ni ynxu ba zan taba yarda ya ganni ba bare da hankalin kaina naje inda yake ta soma dariya gami da fadin kin fiye tsoro me zaiyi maki?daga ganinki sai ya hau dukanki sai kace mahaukaci?tacigaba da dariya na ture littafin gabana na dube ta nace don Allah ki sanar dani wani abu game da yayanmu mana, Tace Abdulrahim sunanshi na gasky wato Abdulrahim mukhtar maska a yanda naji ana cewa tun yana dan karamin shi sam baida yawan fara'a ga miskilanci don zai iya kwana bai damu da yayi ma wani magana ba in ana son aga fara'arshi to a bashi kwallo sannan kwallonshi ta samo asali ne tun yana makarantar primary inda yayi ta cin gasar da aka sha hada su da wasu makarantun,haka yacigaba har secondary,bayan kammala yaso a barshi yaci gaba da kwallonshi amma sai babanmu ya kiya sam dole yaje ABU zaria inda ya karanci politics har ya samu degree bayan ya gama sai ya shawo kan babanmu da kyar yayi wasanni da dama a nan gida nigeria kafin ya fita england inda wani coach yayi mishi hanya, Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Na dakatar da ita nace ke ni ban tambayeki lbr kwallo ba,kunce yana dukanku ko?mami tace Allah yana duka sosai ma,amma sai ka mashi ba daidaiba,na dubeta nace kamar yaya ba daidaiba?tace baya son ya saka abu kaki ko kai shirme,bai son kazanta kuma in ka ganshi yana son ka gaisheshi amma baison yawan gaisuwa ,kana ce mashi ina kwana is ok,yana da cin abinci kinsan yan kwallo gashi da tsafta yana son kamshi ke gadai abubuwa nan,in har kin kiyaye komai babu abinda zai faru tsakaninku ko ynxu ki tashi muje ki gaishe shi mana,nace a'a mami gaisa wata rana nace to ynxu ya dawo kenan?tace aah bai dawo ba kenan,zai koma wannan zuwan ma in gaya maki haj yaya ce ta matsa yazo don su gana da yar gidan haj laure,anty mimi nace ita zai aura kenan?mami tace kuma abinda baki sani ba yana matukar bin maganar iyayenshi don ko wuta suka ce ya shiga zai iya shiga musamman haj yaya bai hada ta da kowa ba yana matukar jin maganarta,na dube ta cikin tsoro nace kinji ko?tana ce mishi ya koreni zai koreni ko dai ma in tafi ne?mami sai dariya take yi min,Kamal ne ya shigo ya sanar da mami mamansu na kiranta.Bayan kwana biyu ya raba tsaraba har su jamila da sagir ya basu,mama ma ta samu less da shadda da takalmi sagir din ma harda Jc shi da kamal,su mami english wax ya kawo masu ni dai banje ba kuma bai sani dani ba don ban yarda ya gani ba,ran da ya yi kwana ukku da dawowa mama ta amshi girki da rana ina tayata aikin burabisko mami ta same mu a kicin tace yaya yace a kai mishi abinci,nace yana cin birabisko ne?tace oho nace to inbazaki laifi ba kije ki ce mishi burabosko ne don kar a yi mishi laifi,tayi musrmushi sannan ta fita,anty yagana tayi sallama ta shigo na fito daga kicin na amsa,sannan na gaisheta gami da tambsyarta saudat tace tana gida sannan ta wuce ciki tana ce min maman naki na ciki? nace eh,mami ta dawo tace yace akai ma abokanshi shi kuma a dafa mashi indomie amma ke zaki dafa ko? tace eh nace to don kar inyi kuskure mami tayi dariya tace kai ke kam kin cika tsoro,sababin kuloli mama ta bani na zuba masu birabisko da miyar kaji yaji curry sai kamshi yake,na dauka na tafi nayi sallama a kofar dakinshi aka amsa mani cikin faduwar gaba na shiga nace sannunku mutum uku suka amsa kaina a kasa ban kalli kowa ba nace a ina zan ajiye?cikin dauriya nake magana gabana sai faduwa yake wani daga cikinsu yace maska tana magana,da sauri na dan dubi wanda aka kira maska yana ta faman danne danne waya tamkar ba dashi ake magana ba,dayan yace ke ajiye kan wancan table din,na dubi table din sai naga akai yayanmu ya dora kafarshi ,na dubi mai maganar nace ai yasa kafa a kai yayi murmuahi sannan yace ajiye ko ina kinsan halin yayan naku sai hakuri na ajiye a gabansa don mami tace dama su ne zasu ci na juya zan tafi sai naji murya mai sanyi amma cikin fada akace ke haka ake bada abinci a gidanku ko?na juyo da sauri ga mamakina yana danne danne wayarshi kamar yanda na sameshi,sai a lokacin ne ma na dan kalli fuskarshi, kykkyawa ne na ban mamaki don duk gidan yafisu kyau sak kamarshi daya da hajiya yaya,tsawa naji in ba zaki zuba musu ba dauki ki tafi,da sauri na duka jikina na kyarma na zuba musu nan dakin ya bude da kamshin miyar kajin na mika wa kowa sannan na mike dayan yace dan bamu ruwa nace to zan fita dayan kuma yace ga fridge nan na nufi gun fridge ina tunanin yanda zan bude dan ban taba ganin irinshi ba cikin sa'a ina dafa shi sa i naji na latsa wani abu sai ko ya bude kayan shaye shaye ne kala kala na rasa wanda zan dauko musu sai na dauko musu ruwa a babban gora na dauko five alive na aje masu da na duba saman fridge din sai naga kofuna irin na wajen na dauko tiran kofunan gaba daya na aje a gabansu,ina kokarin mikewa ne mami tayi sallama suka amsa har da yayanmu ta shigo dauke da kula da plate da cokali na fita na dan tsaya a kofar dakin ina jiran mami labarin abinda yayanmu yayi mani sai na jiyo itama tana shan nata fadan,muryar yayanmu ne yana