Sashe 16
Tawa Ta Sameni Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
sai dai ni bata dameni ba don haka ko lambar ban rike ba in Nana tazo taje maka da lambar yace ai bazaki min ko flashn bane tunda kinsan tawa nace to na maka na shige daki ina jinshi yana fadin barakiya? Sannu a hankali zuciya da gangar jiki suka tsananta da so kauna da kuma begen wanda bazasu samu ba sannan ni naki yarda da cewa sonshi nake ban yarda da nayi nutso a kogin sayayya ba sai da na samu kaina da rashin barci,sannan na kama karatun littatafai na soyayya,kallace kallace da basu dameni ba yanzun nakan zauna nayi duk saurayin da aka nuno sai naga bai kai yayanmu komai ba ni fa gani nake ba wani namiji wanda ya amsa sunan namiji in ba yayanmu ba,yauma kwance nake akan gado yar karamar Rediyon da nike yin karatu ce na manna a kunnena kaset na wakar fim din kugiya na sa wakar na ratsani Idona a lumshe sai nakejin kamar nice nakeyin wakar, duka naji an dada min da sauri na tashi ganin Amira da Mami shine yasa nayi ajiyar zuciya nace kin dau alhakina Amira ta cire wayar kunnena sai ta dauke Radion ta sa a kunnenta dajin wakar sai naga ta cire da sauri tace Mami ji wannan kaset din Mami ta sa taji sai naga sun dubi juna sukayi dariya nace wai menene?suka zauna suna cewa zancenmu gasky ne nace kamar yaya zancenku gsky ne?Amira ta dauke fuska tace Iman mun gamsu nace me na muku?Mami tace akwai abinda yake damunki amma kin kasa sanar damu,Amira ta amshe damu ne da munhau gaya maki nayi shiru ina tunanin me zan ce masu can dai nace Amira,Mami kunsan yayyena Abubkr,Ibrahim da Sulaiman?suka ce sosai ma kuwa nace dukansu sunce suna sona ni kuma bani son ko daya sannan yaya Kabir shima yace wai sona yake na mike tsaye don girmama maganar da zanyi na cigaba da cewa ni kuma zuciyata da gangar jikina sun nutse a son wanda bai san inayi ba kuma koda ya sani ba zai soni ba don yana da wacce ta fini kyau da ilimi da kuma shekaru,hawaye suka soma zubo min na juyo da sauri na rike kafadun Mami da karfiina cewa ku bani shawara kawayena ku taimaka min da maganin da zan daina sonshi don kukan ku da zaku san ko wanene da kunce lallai zuciyata tayi wauta,suka kamani suka zaunar dani tsakiyarsu suka yi shiru dakin ya yi tsit daga ajiyar zuciata da nakeyi sai karan fanka can Amira tace a ina yake?kuma yaya sunanshi?nace kuyi hakuri wata rana zan gaya muku don ba anan yake ba Mami tace dakin gaya mana ai da mun san yanda zamu bullowa abin nace no ko zan mutu bazan taba tunkarar wani da namiji da sunansa ba yanzu ku bani shawara yaya zanyi na daina tunaninshi suka yi shiru can Mami tace rokon Allah zakiyi muma zamu taya ki nace sai dai mukara don kullum yi nake amma ba sauki sai dai abinda ya karu nan dai suka lallashe ni gami da bani shawarwari. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Haka naci gaba da rayuwa cikin kunci,wata safiya misalin karfe takwas Mama tana dakin Alhaji ta kai masa abin kari ni kuma ina ta faman gyaran dakinmu na gama na koma dakin Mama ina cikin aiki naji wayar Mama tana ringin na dauka sai ga lambobin rakwacam na dauka nace Assalamu alaikum sai naji ance Wa'alaikummussalam,jin muryar da ta amsa nan da nan na gane yayanmu ne farin ciki da na ji baya misaltuwa ina wannan tunanin ne naji yace Naman Sagir ina yini? nace ba ita bace ni ce Mama tana dakin Alhaji yace ok! nace ina kwana?yace lafiya amma mu nan rana ce kuna lfy?nace lfy lau yace to kice da Maman Sagir ina gaishe ta dama don mu gaisa ne na kira kafin nace to har ya kashe ranar nayi walwala har yamma don jin muryar abin sona. Share