← Book details Tawa Ta Sameni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 22

Sashe 19

Tawa Ta Sameni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

agogo yake yi na isa gurin shi fuskata babu walwala nace ina kwana?bai amsa ba sai dubana yake yana murmushi yace da raina ya baci domin kin shanya ni amma yanzu kin wanke min zuciyata na dubeshi nace kamar yaya?kinyi dressing irin nawa,na dubi kayan jikinshi kampala green nima haka sai naji tamkar na koma na cire ya dube ni zo muje na saukeki nace ka barshi yace duk da nayi latti sai na kaiki,dole na shiga muna shirin fita yayanmu ya shigo shi da wasu abokanshi cikin kayan training duk da kaninshi ne sai da gabana ya fadi yako tsira mana ido sai ya tsaida motar ya dubeni yace kin mani shara?na dubeshi yayi wani kicin kicin nace a'a yace to fita ki min bai saurari amsata ba yayi gaba na dubi yaya Kabir nace to kaji fa abinda yace,yaya Kabir yace don Allah ki rabu dashi bari mu tafi,nace wai ba haka a tsakaninmu haushi ya kama yaya Kabir yace toko dai yana sonki ne?nace kaji ka da wata magana kaima kasan ko mata sun kare yayanmu ba zai soni ba yace saboda me kikace haka?nace ni nasan bani da kyau kuma gani baka yayi murmushi sannan yace ganinki kenan kina abubuwa masu fizgar hankali so ni dai yanzun ki yarda na fito sai a hada da nasu Mami,haushi yasa na bude motar na fito shima yayanmu na sameshi ya cika dam ina shiga ya dube ni duban wulakanci yace me kika tsaya yi a gunshi?nace ba komai ya nuna ni yace look ba zaki min yawo da hankali ba bani son na kara ganin kin shiga motar Kabir kina jina?ya daka min tsawa nace to,ya fita na shiga gyaran daki ina mamakin wannan ikon Allah.. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Ina cikin goge TV ya shigo yana waya ya zauna kan kujera yanda naji yana amsa wayar ne yasa naji duk bakin ciki ya kamani ko bai fada ba nasan da Mimi yake magana har yana cewa karki damu nima kin manne cikin raina kuma ki saurareni in anjima da sauri na shiga bedroom dinshi har lokacin wayar yakeyi ranar da takaici na yini wata zuciyar tace min kina kishin banza kina wahala bai san ma kinayi ba Kwana biyu ni dasu yaya Abubkr da duk wani mai son ganina in dai saurayi ne sai dai a waya ranar juma'a ina zaune da yamma tsautsayin jin takaici ne yasa nace da mama bari in shiga gun Amira ina isa daidai dakin yayanmu shi kuma yana fitowa tare da abokinshi sun kai su bakwai daya ne naji yana cewa ango ango to Maska wata nawa aka sa yayanmu ne naji ya amsa da cewa sati biyu suka sa da sauri na juyo cikin sa'a muka hada ido shima sai naga yayi wani iri tamkar bai so naji zancan ba wani abu mai nauyi naji ya tokare min wuyana kirjina kuma ya hau zugi da kyar nake janyo numfashina kokari nayi naci gaba da tfy amma bana ganin gabana sosai jirin da naji ya soma dibana shi yasa na juyo na koma gida ikon Allah nema ya kaini kofar dakinmu a nan na zube ban kuma sanin in da kaina yake ba na dai farfado na gani a gadon asibiti Mama tana zaune a kan kujera tana rike da hannu na wanda aka sa min karin ruwa ta min sannu na amsa da kyar a hankali na soma tuno abubuwan da suka faru shi kenan yayanmu ya zama na Anty Mimi ko shakka babu yana mutuwar sonta,na tuno wata rana ina shara a dakin yaynmu har na gama zan fita yace nazo nan na juya na koma nace gani yace baki sa turaren daki ba nace na mance ne,na shiga bedroom din shi idona ya sauka akan wani kyakyawan frame kamar kaida in dai zan shiga uwardakin yayanmu to ba abinda nake fara kallo sai wannan frame din yana da kyau ga dauakar hankali gashi saitin kofa da ka shigo shi zaka fara gani,na manta batun turaren daki na tsaya duban frame rubutun jiki yan kanana shi yasa ban taba karantawa ba amma lokacin sai na hangi rubutun saman kamar hausa akayi nayi mamaki frame mai kyau da shegiyar tsada irin wannan amma da hausa na ce kai yau sai na dauko shi na karanta duk da wane yare ne na duba dakin ko naga abinda zan taka don yayi sama sosai ba wani abu mai tsawo sai tebur karami kuma na glass ne na jawo shi a hankali na taka daya ke nima ina da tsawo na dauko,tabbas da hausa akayi rubutun a saman an rubuta: Zinariyata Zuciyata ta jima tana begenta daga lokacin da idanuna suka fara ganinta,na tsunduma a sonta duk karancin shekarunta duk sanda na dubi idanunta sanyi kasala sha'awa suna gajiyar dani bare in naji kamshinta,a lokacin da nayi nisa da ganinta sai barci ya kaurace ma idanuna sai tunaninta bana jin dadin wani girki sai nata Allah ka azurtani da aurenta domin na samu ni'imarta har ka azurtani da 'ya'ya masu albarka daga gareta (A)amin. jikina yayi sanyi sai dai abin daya bani mamaki shine yanda (A)a cikin (A)tamkar irin na zoben da yayanmu ya bani a cikin kayan tsaraba nace kai kilan ma ba (A)guda biyu ba ne wani tambarin ne na wani camfanin a can England din,na dubi fulawoyin dake jikin frame din da tsuntsaye masu ban sha'awa ina cikin juya shi ina cewa nasan Mimi yake nufi,shine Mami tace min baya sonta ashe ma ya jima yana sonta gashi yace tun tana karama,ina cikin tunani naji yayanmu daga falo yace baki ga turaran bane?nan jikina ya soma rawa ina kokarin maida wa ne tsautsayi yasa na goce,frame din ya fado sai kan tebur din glass ji kake tats,jikina ya hau bari na soma tsuma tamkar mazari,na dauki frame din baiyi komai ba teburin ne ya fashe naga an daga labule da sauri na dubi kofar yayanmu ne tsaye nayi duba zuwa ga fuskarshi ya wani daure fuska me ya kai ki gurin frame kina ganin sirrina ko?hawaye ya soma zarya a kan kumatuna nace a'a zan goge ne yayi kura ya daka mani tsawa yi min shiru kuma sai kin biya dukkan abinda kika fasa min,na durkusa kan gwiwoyina na soma cewa don Allah kayi hakuri yace ai zaneki zanyi yanzun nan muryata tana rawa nace please yayanmu ya dubeni cikin wani yanayi mai wuyar fahimta sannan yace gyara min wirin ki wuce,ban san kan kwalba nasa gwiwata ba sai da na gama gyra dakin sannan naji zafi na duba.kamshin turaren da naji shi ya dawo dani cikin hayyacina ko ba'a fada ba nasan yayanmu ne ya shigo Asibitin nan ban gama tunani ba ya kwankwasa kofa ya shigo dama fuska ta kofa take kallo don haka yana shigo dani muka soma hada ido sai naga tamkar an kara mashi wani kyau.... Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Na lumshe ido sai naji wasu hawaye sun zubo min ina jinshi suna gaisawa da mama ya tambayeta jikina tace da sauki ban ma san har na kwana ba sai da naji yace tun jiya bata tashi ba?mama tace dazun nan ta farka ina mata magana banji ta amsa ba nayi mata sannu ta amsa bata kuma magana ba sai hawaye da ke zuba daga idonta shiru yayi na dan lokaci sannan yace bari inga likitan mama tace yanzun nan babanku ya tafi gurinshi tun jiya ma yace ciwon zuciya ne yake son kamata ni na rasa mai yarinyar nan ta nema ta rasa da har ta sa kanta cikin tunani,muryar yayanmu naji cikin sanyin shin nan yace ai maman Sagir cututtuka sunyi yawa ba sai mutum yana wani tunani ba Allah dai ya sauwake ya juya zai fita sai ga a Alhj ya turo kofa yayanmu ya matsa Alhj ya shigo yana ma mama bayani sun tabbatar da zuciyata na son ta harbu sannan yace su tuhumeni ko akwai wanda takeso ne ko abinda ya shafi haka yayanmu yace Alhj bari nima na ganshi likitan sukace to lokacin Alhj yasa an tashe ni zaune ni kaina nasan na rame sosai cikin kwana daya yayanmu ya dubeni yace sorry Iman na dubeshi yaune na fara jin ya kirani da Iman na daga kai alamar amsawa,yace maman Sagir me taci?mama tace bata ci komi ba yanzu ne dai zan hada mata to amma tace sai tayi sallah tukunna,ya dubeni zaki iya yin sallar ne?nace eh tare da taimakon mama nayi alwala muna fitowa daga bayi yayanmu yayi mana sallama yace da daddare zai dawo haka na cigaba da jinya har tsawon kwana uku kullum yan dubiya suna zuwa,Amira da Mami nan suke yini haka yayanmu da yaya Kabir nan sau uku suke zuwa sai dai duk lokacin da yayanmu yaga yaya Kabir haushinshi yake ji, gudun fadan alhj yasa kishiyoyin mama suka zo sau daya kuma basu kawo mana abinci sai dai anty Yagana da maman su Amira kayan ciye ciye kam yayanmu ya kashe kudi har Anty Mimi ya kawo ta gaisheni nasan dai dole tazo ba don son ranta ba,niko ban ma ji wani dadin zuwanta ba don ma kadan ya rage ciwona ya dawo musamman ma da naga sun sa anko yellow kampala sun man kyau sai dai kishi da ya sani gaba,ban san yanda akayi su yaya Abubkr sukaji ba sai dai ganinsu nayi yaya Ibrahim ne yake ce min babana yana nan zuwa,yace a gaisheni naji dadi har ina tambayarshi yaushe zaizo?yace kilan yau ko gobe nace kilan a sallame ni yau ai a ranar aka sallameni kafin sati na dan girgije,yan skull dinmu na comp ma sun zo duba ni randa na cika kwana goma ranar na koma zuwa makaranta lokacin saura kwana hudu bikin yayanmu su Mimi duk sun damu da bikin sai rawar kai suke yi har Mami na cewa da ban warke ba bikin ba zai mata dadi ba sannan suna son kudi gun yayanmu nice ma zan amsar musu nace ke Mami ki rabu dani ba wani kudin da zan tambaya a raina nace in baku
Chapter 19 · 0% Book details