Sashe 14
Tawa Ta Sameni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kira Iman gata tazo sai ki fda muji ynxu,ta soma magana cikin sababi ni dai Alhj kawai kayi mani tsakani da Habiba da kuma 'ya'yana in kai ta gama da kai to ni da 'ya'yana li'ilafi,,tashanye min yara basa cin girkin kowa sai na 'yarta sannan yanzu shi wannan miskilin dana gani kamar zai zama namiji amma ba haka bane ya tashi sai kashe mata kudi yakeyi harda yi mata anko da matar da zai aura me hakan yake nufi? na dai san rokonshi sukayi don haka ayi mana iyaka dasu ba 'ya'yanta ba nawa,tun da ta soma bata tsaya ba kuma ba a katse ta ba,jin tayi shiru sai na dago kai na dubi kowa kowa dai ita yake kallo sannan na dubi yayanmu wanda kanshi yake kasa Alhj yace to naji naki ke kuma Habiba ya abin yake?Mama ta soma magana cikin sanyin murya lafuzza masu kyau tace ni dai Alhaji a gefena ba wani matsala yarinyar nan dai itace matsalar, da zaka amince min da sai na dauketa na maidata wajen kawunta don inda bata nan gidan da baza ta ga ma 'ya'yan Haj Yaya ba bare su sata aiki sannan muddin tana nan gidan ba zan hanata aiki ma kowa ba har Hajiya Yaya inda zata sata,amma kiyi hakuri Yaya zan maido maki da dukkan abinda Abdulrahim ya sai ma Iman sannan kuma sai kiyi mashi magana ya daina sata aiki a zauna lfy,na dubi Mama hankalinta a kwance tayi maganar sabanin Haj Yaya wadda ke cika tana batsewa. Dakin yayi shiru sai can a Alhj ya soma magana yace Murja! Haj Yaya tace na'am da karfi tana karkada kafa yace ina son kisan cewa 'ya'yan nan nawa ne kuma wancan ma tawa ce don ni da kaina na daukota ko uwarta bata san zan kawo ta sai dai ta ganmu Allah yasan wannan don haka ba zaki raba min kan 'ya'ya ba kinyi kadan,Habiba yarinya ce a kanki amma tafiki hankali da tunani saboda haka kar ki yarda ki amshi duk wani abu da yayi mata kuma aiki duk wanda yayi niyyar sata kar ya fasa don haka na gama wannan maganar sannan ki gargadi laure ta kiyayeni da wasa naji ta taba Habiba ko Iman sai nasa an daureta gara ma ta tabaki zaifi mata sauki,Haj Maska tace yayi daidai hakan,Murja in ka girma to kasan ka girma don haka sai ta soma kuka tana cewa dama namiji ba dan goyo bane nan na dauki kudina na baka ko basu ne silar arzikin naka ba?daban haka ai da har yanxu kana a fakirin ka dole ka min sakamako da mun wulakanci ta nuna ni tace ke kuma zakiga hukuncin da zan yanke a kanki muddin kika kuma ko kallon min 'ya'yane na durkusa da sauri(don har ta mike)nace don son Annabi(SAW) kiyi hakuri bankade ni tayi waje sauran kishiyoyinta suka take mata baya,Alhj ya bisu kallo sannan yace Allah sarki to Allah ya sa ku gane,ya dubi yayanmu yace kaima kayi hakurin dai zan baka cikin sanyin murya yace Alhj kaimin izinin na koma england jibi,yace na maka amma yaushe zaka dawo?kar kaje ka kuma zama yace nan da wata shida ne yace to Allah ya kaimu ya fita na bishi da kallo. Karya ne gane halin da fuskarshi take ciki wato laifinmu yake gani ko na uwarshi,ban taba ganinshi cikin dogayen kaya ba tunda yazo sai yau boyel ne baki amma kanshi ba hula Alhaji ya dubeni yace Allah yayi maki albarka Iman kiyi koyi da halin mahaifiyarki kinji?na daga kai ya cigaba da cewa muddin kikayi halin uwarki to kin dace,sannan mijin da zaki aura ma yadace,su Abdulrahim da Kabir duk yayyanki ne duk abinda suka saki kiyi,sannan in sun maki kyauta ki amsa kice kin gode nace to Alhj na gode,na mike na fita dakinmu na wuce kai tsaye kan gado na fada raina a cunkushe na rasa me ke daga min hankali son da Kabir yace yana min ko matakin da Haj Yay tace zata dauka a kaina ne?wata zuciyar tace duk ba wannan bane tafy yayanku ce wannan amsar da zuciya ta bani itace sanadiyar tashina zaune saboda tashin hankali da naji ni a ciki na mike ina safa da marwa nace a fili ban so akayi wannan rikicin ba ba zanji dadi ba muddin yayanmu ya tafi kai zanje na bashi hakuri in ya tafi na mutu,da sauri na dauki hijabina na fita falo nan nayi turus ganin mama a falon tace ina kuma zaki?karon farko da na soma yi mata karya nace gidansu Amira tace me xakiyi?nace takalmina da gyalena dauko tace ko bari zata aiko maki ko ki aika Jamila kar ki fita ko ina ynxu zo nan kiji,na isa gunta na zauna tace kin dai ga abinda ya faru ko?nace eh tace to ina son kiyi taka tsan tsan da kowa a gidan nan banda yawan shigewa duk wanda ya saki aiki to kiyi masa kamar yadda kikaji Alhaji yace maki,nace to ta kuma duba na tace yanaga kinyi wani sukuku dake?nace bani son tashin hankali ne mama shiyasa tace kar ki damu aikin shedan ne kuma ki cigaba da addua sannan daga ynxu zan na tashin ki duk dare in tashi yin nafila sannan zaki dinga yin azumin litinin da alhamis,sai mu dinga tare in kuma an gama bikin nan zanje wurin kawunki na samo mana addu'o'i na tsari mu dukufa,Allah ya ja mana gaba,sauran maganganun da mama takeyi duk banji su ba ina ta tunanin yanda zan ga yayanmu don nasan nice na jawo wannan tashin hankalin gaisuwar da naji mama ta na amsawa shine yasa na juyo Mami ce ta dubeni tace ya dai?na mike muka shiga dakinmu kan gado muka zube na dube ta nace ya dai tace ina gidan walima muna shirya guri sai ga Sa'a wai ana fada da mamanku da su Haj Laure har sunce sai sun zane ku?nayi tsaki nace kan fa kaya ne kin gansu nan jikina yayanmu ya bani ashe irin na Anty mimi ne shi kenan sai tashin hankali gashi yanzu ma yace zai koma jibi,Mami tace ai dama bayan biki da kwana biyu yace zai koma nace to ai gashi ba'a gama bikin ba ni gani nake ma duk laifina ne hawaye suka zubo mani akan kumatu Mami ta tsaya kallona baki bude shi ne harda kuka?kuma ma ina wani laifinki anan? nace nasa kayan tace to baya baki don kisa bane?shi yayanmu in zai ma mutum kyauta ba ruwanshi da wani nuna bambanci nace rakani na bashi hakuri,Mami tace tab ai sai dai kije ke kadai yayanmu ba ya son ai ta faman bashi hakuri musamman in yana cikin tashin hankali gara makin zauna,ke menene naki na damuwa? kina ganin zaki iya hana shi ya tafi ne?nace bani na ja komai ba,tace sannunki da kai ta mike zo muje gidan walima nace ni kaina ma ciwo yake bazan sami zuwa ba ta tafi na koma na kwanta na cigaba da kuka rurus,saidai za'a a tsira ni ko da bindigane ba zan ce ga abinda nake ma kuka ba sai da nayi ya ishe ni sannan ciwon kai ya yomin sallama kafin wayewar gari nayi rigif ko sallar asuba kasa yi nayi sai wurin bakwai na safe yinin ranar nan haka nayi shi, misalin karfe uku Alhj ya shirya da Yaya Abdulrahim yace Habiba danku zai wuce fa,kan Mama tayi magana shima Yayan namu ya shigo ban san lokacin da na mike ba ya zauna a kan kujera yana gaida mama bayan ta amsa sannan ta ce ikon Allah tafiyar ta tashi ne Abdulrahim?na dauka gobe ne?yace eh gobe ne zanje lagos ne na kwana shida na safe jirginmu zai tashi yanzu ma jirgin karfe biyar zanbi zuwa lagos din yana magana niko bakinshi nake kallo da sauraron muryarshi mai dadi tamkar ba namiji ba ne yake magana ba Mama da Alhj suka shiga dakinta ya bisu da kallo sannan ya juyo ya dubeni na dukar da kai gabana sai faduwa yake yi,ga mamakina naji yace Amina nayi sauri na dago kai baki bude ina dubanahi shima ya kafa min idanu na sunkuyar da kai don ba zan iya cigaba da kallon kwayar idonshi ba sai ina ganin wani abu yana fitowa daga idon shi,yana shigowa nawa,murya kasa kasa yace zan tafi kiyi mani addua kaina a kasa nace adawo lfy Allah ya bada sa'a,a lebanshi naga ya amsa,Alhj ne ya fara fitowa yana cewa Abdul walarka nace Mam zata baka?yace no Maman Sagir kar ki damu ba sai kin bani komai ba Mama ta fito da dambun nama dayawa tace to ka tafi da dambun naman nan Iman tayishi shekaran jiya ya dubeni sannan yace to zan amshi wannan sai naji wani sanyi a raina suka fita nima na daga labulen dakinmu ina kallo ga yan biki nan sai a dawo lfy suke mashi harda su Haj Yaya dasu mama aka fita harabar gidan wajen ajiye motoci nima na fito ina daga can baya ina kallonsa har aka shigar mashi da jakunkunan shi cikin boot din motarshi yaya Kabir ne zai jashi,ga wasu abokanshi suma zasu shiga wata motar ya fito daga dakinshi har ya sauya kayansa da jc jajaye masu ratsin fari dogon wando da riga mai dogon hannu sai takalmin kwallo Anty Mimi ma ta fito sai kuka takeyi haushinta ya kamani a ganina nice yafi dacewa inyi kuka ba ita ba ko mai yasa oho zai shiga mota kenan ya hango ni sai naga ya tsaya yana kallona har Anty Mimi ma ta juyo taga wa yake kallo?sai taga ni yake kallo sai naga ta kawar da kai niko sai na kwantar da kaina a jikin bango sannan na daga mashi hannu alamr bye bye sai ya shige mota suka tafi Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Tun daga wannan rana ban kuma wani sukuni ko walwala ba har mamakin kaina nakeyi kullum cikin damuwa bana wani cin abincin kirki gashi kowa ya gane halin da nake ciki a gida da makaranta sai dai kowa ya tambayeni sai nace bani da lfy ne.Azumi da nafilflii kullum cikinsu nake ,ranar da yayanmu yayi kwana biyar da tafy