← Book details Tawa Ta Sameni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 22

Sashe 5

Tawa Ta Sameni Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

rage yaki dole na amsa nayi godiya.Amira wacce tayi shiru tun da na soma magana kamar ruwa ya cita sai da nayi shiru sannan tace gsky iman ke yar gata ce to amma sai nan gaba zaki sani in Allah ya kawo karshen muguwar matar babanki,nace Allah yasa,Amira ta gyara zama sannan tace anty faty matar babanki ta haihu?nace kai har yanzu Allah bai basu ba tace to ina yayyenki Abubakar da Ibrahim kuma?yanzu basa zuwa nan?nayi murmushi nace kin cika tambaya Amira zaki yi kyau da yar aikin da nake ra'ayi wato yar jarida Amira ta basar da abunda nace tace baki amsa mani ba nace basu san nan gidan ba don kwanaki baba uwa tace masu mama tayi aure,sai kuma ta kuma cewa to ina yayansu mami abdul wa ma kika ce mani?nace abdulrahim sunanshi mami tace yana england shi dan wasan kwallo ne nima ban sanshi ba amma ya sha masu aike nima na gani,shi kuma kabir aikinsa shi dai amira tace haba nasan shi mana ba shi ne yake karatu a kano ba,tace ai shi naga ba ruwanshi don naga yana maki wasa nace gsky shi kam ba ruwan shi ko zai zo hutune ya kanzo da yar tsaraba su sweet biskit da yan kayan lashe lashe ya ba kannenshi tonima yanda ya basu haka yake bani don haka nima nake sonshi a raina ganin shi nake kamar yaya abubakar duk da bai tsokanata irin na yaya abubakar din amma kinga yayan nasu da ke waje ina tsoron ranar da zai dawo,ta dube ni don mi kika ce haka?nace don ina jin yanda suke lbr shi wai ya cika masifa ga duka sannan nasha jin yanda suke bada lbr irin son da yake ma hajiya yaya,sunce yana son mamarsa kamar ransa don bai hada ta da kowa ba yanda mami take bada lbr sai kinyi mamaki sosai abin kamar ba gaske ba to kuwa ai kinsan dole ne ya kuma ki duk abunda taki gami da tsanar shi tunda sunce komi tace mashi yayi,don haka ina jin ance yau zai dawo zan hada ya nawa yanawa na kama gabana na koma can gidan kawu na malam,Amira ta dinga man dariya wai na cika shegen tsoro nace ai ke dariya ma nabaki?lallai Amira, tana dariya tace dole ne nai maki dariya ma naga dai komai son uwar shi sai kin mata abu sannan zata sanar dashi sannan in baki sani ba su maza ba yawancinsu basu da daukar zance na tsegumi haka wannan sai mata sai ko sakaran namiji ina jin wannan ba zai maki haka ba don shi dan boko ne nayi shiru ina nazarin maganarta can nace wannan gasky ne to Allah yasa dai kar ya kulani,Amira tace amin,mun kaure munata zuba lbr sai kawai ganin yaya Ahmed mukayi nace a'a yayanmu ustazi ba sallama ne?yace ku dai bakujin sallamar to mama tace a tashi ayi sallah dama masallaci zani,yasa kai ya yi waje na mike nace bari na wuce gida kawai,Amira tace ai baki isa ba sai kinyi sallah kinci abinci sannan zaki bar gidan nan,na kwace daga riko da tai min nayi waje ina dariya nace yaushe rabon da ki shigo gidanmu,ta biyo tana kira na gudu gashi nayi sa'a mamansu tana daki tana sallah a gidanmu ma mamanmu sallah na sameta tanayinima sai na shige dakinmu naga jamila tana barci na tashe ta muka yi alwala muna idar da sallah nima na kishingide. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
Chapter 5 · 0% Book details