Sashe 13
Tawa Ta Sameni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tawa Tasameni 1-03 Posted by ANaM Dorayi on 02:31 AM, 29-Dec-15 Under: TAWA TASAMENI __________NA HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Garama ni ubana yana nan, haka danginshi, nayi nisa cikin tunani na ji horn ba karewa na juya can wajen da ake horn din bakin gate sai naga ashe su yayanmu ne zasu tafi ban fahimci wai ni suke ma horn ba sai da anty Mimi ta bude gaban mota tace ke na dubeta na dafa kirjina nace ni?eh da Allah zo nan ana maki horn kinyi banza da mutane, na nufi gunsu ina zuwa naga yayanmu ya sako hannu ya bude baya yace shiga,gabana na faduwa na shiga motar don nasan ba wanda ya taba shigarta a yan gidanmu sai yaya Kabir na zauna sannan na rufe sanyi da kamshi sune suka ziyarceni tamkar wata munafuka haka na zauna a motar kaina a kasa, suko suna ta labari bana jin dai muryar yayanmu sai ta anty .Mun yi nisa sannan na dago idona sai kawai muka hada ido da yayanmu ta madubi nayi sauri na sunkuyar da kaina kasa har mukaje ban tanka ba,ban kuma daga idona ba,sai da naji an tsaya sannan na dubi gurin yan mata ne cike na buda zan fita sai naji yayanmu yace karba,na juyo sai naga yana bani kudi ne sababbi yan naira hamsin na amsa nace Allah ya saka da alkhairi,anty Mimi ta shaka sosai da na kalli fuskarta ni dai nayi ciki ko zan ga Mami, ana cikin hidima shalele suka kira don haka gun ya cika da karan kidan police band Sa'a tazo tace kije ana kira gabana yana faduwa nace inji wa?ta harareni dole sai kinji? ki zo mana na bita can baya mukaje ganin Anty Mimi da Amare da kuma kawayensu yasa wata faduwar gaba ta sameni na dai daure na isa wurin,Anty Mimi ta kai mani rankwashi akai tace ina jakarki?nace tana gun Mami tace nawa yayanmu ya baki?nace ban kirga ba nan ta shiga zayyane masu wai wannan wace irin yarinyace,Anty Hadiza tace ai wannan daga ita har uwarta annoba ce,Anty Mimi ta cigaba da cewa kunga jiya a gabana ya bata waya irin tawa ce sak koda ganin kwalin sannan yau zamu taho nan ta zo ta rabe ya dauko mu tare kunji biyu,cikon na uku kuma sai gashi ya raba mana kudi kilan ma daidai ya raba tamkar wasu kishiyoy,nan suka taru a kaina wannan ya kai mani bugu kowa dai na fadin albarkacin bakinshi, Mami ta iso daidai lokacin da wasu kawayen Anty Mimi suke cewa asiri tayi mishi daga gani,in ba haka ba me zaiyi da wannan mummunar yarinyar gara ma ki dauki mataki tun da wuri akan abin, Mami tazo tana cewa Anty Mariya kuzo anguna sunzo fa ana ta nemanku,kan suyi magana Anty Mimi tace Mami muga jakar wannan jakar,sai sannan Mami ta ganni ina kuka tace Iman menene?Bilki tace ba'a sani ba ke dai ki bada jaka a kace Mami tace bazan bayar ba nace Mami bata ta mika mata sai da suka kirga kudi daidai da nata dubu ashirin da biyu ne dama ban kirga ba,saura sukace kar ki bata ko sisi Mami tace wllh sai naga ya wa yayanmu in har kika dauki kudin nan,Anty Mimi ta watso kudin da jakar a jikina sannan tace ki jira abinda zai biyo baya ta wuce sauran suka bi bayanta aka bar daga ni sai Mami inata kuka,Mami ta kwashe tana tambayata abinda ke faruwa na zayyane mata komai itama na kula ta dan yi mamakin kudin da ya bani tace Iman yayanmu yana ji dake fa nace Nami ku kula da wani abu daya yayanmu nice nake mashi aiki,shiyasa yake mani alheri amma wai suna zargin wai yana sona ne ni nasan ko mata sun kare yayanmu ba zai taba cewa yan sona ba ke kinsani balle yana da kamar Anty Mimi,Mami tace ai itama anty Mimin ba wani kyau ne da ita ba uban gashi ne kamar jirgi ya daso tasha kuma a tsaye take ba wani diri kirji kamar na bera ba wasu nonuwan kirki nace to shi dai tayi mashi Mami tace ke zo muje ba wani yi mashin da tayi kawai saboda mamansu zai aure ta. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 TAWA TA SAMENI,haka na fada ranar daurin auren anty mariya ba wani abu yasa na fada ba sai ganin munsa less iri daya da Anty Mimi wato wanda yayanmu ya bani nasa daya daga ciki me ruwan lemun tsami takalmi da jaka iri daya itama ni take kallo ta zauna kofar dakin yayanmu a fararen kujerunshi ranta yayi matuka gun baci naga ta yi cikin gida ni kuma sai na nufi gidan su Amira,dama dazun ta aiko Faruq wai ta dawo dama jiya ne ta tafi unguwar dosa gun kanwar mamansu da suka dawo kwanan nan shine taje kwana,ta fito wanka na sameta nan nake zayyane mata abin dake faruwa ta dinga mamakin karfin halin irin na nasu Aunty Mimi dan yayanmu ya min kyauta ta kara da cewa komai ya sai maki ba zai biyaki ba irin dawainiyar da kike mishi ba nace suna zargin fa wai sona yake yi,Amira tace haba dai nasan ma ba zai fara ba domin kin......na katse Amira nace ni ba ajinshi bane nasan da haka kuma ko mata sun kare ba zai so ni ba Amira tace ba nufi na kenan ba ina nufin matsalar dake tsakanin mahaifiyarki da tasa ai yasan da wannan matsalar ba zaima ce yana sonki ba.Nace ato su sai hauka suke yanzun nan na hadu da anty Mimin shine ta ganni da kayan nan har jakar to tayi cikin gida ban san me zai faru ba,dama bikin nan sai yan tsegungumi sukeyi dangin Haj Yaya naci gaba da cewa kinsan abin da ya faru ne da babansu Mami ya tambayi Haj Yaya game da kayan da za'a siya don yayanmu ya riga ya sai masu sai yace to suyi mashi list din kudin sukayi mashi hauka to hauka mana wai fa miliyan daya da rabi suka rubuta shiko ya kira mama tayi mashi lissafin kayan dakin mata mata har da na jere da na kicin duk ta sanar dashi naji ya bata kudi sukaje ita da Anty Yagana suka sawo mashi komi don Mama cewa tayi sai da tayi ciko suka kawo ya dinga sa mata albarka itama ta bashi nata gudummuwar na zannuwan gado to wannan abin shi yayi matukar tada hankalinsu Haj Yaya da har sunce sam kayan nan bai masu ba shine baban yace yayi in baiyi masu ba to su sai nasu da kudinsu kafin Amira tayi magana sai ga Jamila kanwata da kukanta wai ana fada da Mama nace mama da wa tace Mama da mutane yan biki nace yau mun shiga uku ko takalma bansa ba na nufi gida Amira ta biyoni,tun a harabar gidan nake jin hayaniya yaya Kabir na gani ya fito daga cikin gidan ranshi a bace da ganina ya nufoni yace kar ki shiga zo nan,na soma kuka ina cewa ni dai na shiga uku ya ja min hannu zo muje karki shiga,nace ina kuka yaya Kabir barni naje naga Mama yace Mamanki tana dakin Alhajinmu zo muje ya jani dakinshi ya zaunar dani kan kujera sannan ya tsugunna gabana yace kiyi shiru zan tambayeki ne,nayi shiru ina share hawayena yace yaya Abdulrahim yace yana sonki? nace aah yayi ajiyar zuciya sannan yace alhmdll yayi shiru zuwa can yace a gaskiya Iman na dade ina sonki shiyasa ma har yau na kasa kula duk wata ya mace da sunan so na mike tsaye na ce Kabir tun ina ganinka da gashi kar ka yarda na kuma jin wannan zancen kana ganin balain da muke shiga kullum a gidan nan sannan zakace wai kan sona ni dai ba ruwana,ya zaro mani ido gami da tasowa kamar zai bugeni yace sai kin soni kuma ni da ruwana ba abinda ya dameni da fadan iyayenmu,na mike zan fita yace kar ki yarda ki fita su Haj Laure zasu dake ki muddin kika shiga,jin maganar duka ni uwar yan tsoro na dawo na zauna na sanyaya muryata nace sun doki Mama ne?yace suna hauka ne?ita ko kulasu ma batayi ba shine yar Alhajinmu da tazo daga maska tace ta shuga dakin Alhajin tasa na mashi waya yanzun nan yana zuwa shiyasa nace kar kije,na cigaba da kukana yaya Kabir yana lallashina har nayi shiru ya dinga shigar dakan shi a guna yana ce min in na yarda yasan Akhajinsu zai tsaya man kuma zai nemi canjin gun aiki mu bar kaduna haka ya yi ta cusa min raayi har na soma yarda,sai dai ina tunanin mama ba zata amince ba na dai yanke shawarar zan ci gaba da addua. wayar yaya kabir tayi kara yace in dauka don nafi kusa da wayar,na dauka sai naga sunan yayanmu sai na mika masa yace ya baki dauka ba?nace yayanmu ne ban san mai yake ce mazhi ba na dai ji yace gata nan sai na kuma jin yace dakina sai gabana ya fadi,sai naji yace to gata nan zuwa,ya dubeni yace alhaji yazo yana dakinshi an ce kije,nace yayanmu na gurin ne?yace shi ne yayi min waya wai Jamila tace nine na tare ki ina kike yanxu sai shine nace gaki nan ki tafi ko na raka kine?nayi saurin cewa a'a don kar agan mu tare,cikin dar dar na shiga gidan yan biki sai ni suke kallo gashi ko takalmi babu a kafata na shiga ciki nayi sallama a kofar falon Alhaji na shiga Alhaji na kan wata kujera irin ta karfen nan ne dama nan ne gun zamanshi sai Mama akan kujerar gefen damanshi dayan gefen Haj Yayace sai Haj Shuwa kusa da ita Haj Kulu na dakin sai yaya ta maska(wato yayar Alhj)yayanmu na kan kafet kusa da kafar Alhaji nima na shiga na samu guri kusa da Mamana na zauna a kan kafet. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Alhj na gaisar sannan yayi gyaran murya yace to gara ke Murja(haj yaya)menene sanadin wannan fadan?na tambayeki dazu kince sai an