Sashe 21
Tawa Ta Sameni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kai alamar eh bayan shi fa?nace ba komai ya mike ya ciro min hoton ya hado da wani shima mai kyau cikin jan JC kan kujera ya zauna sannan ya kama hannuna gabana ya fadi naji wani yarr a jikina ya rike yatsuna da zoben nan yake jiki wanda ya kawo min tsaraba kar ki rabu da wannan zoben komin wuya kinji? kasa magana nayi,yace wannan lallan ya min kyau waya miki?kafin na bashi amsa sai akayi sallama gami da shigowa gaba daya tsoro ya kamani da na juya naga Anty Mimi itama tsoron ne da mamaki a kan fuskarta na dubi yayanmu shi ko namijin duniya ko a jikinshi ya saki hannuna yace Mimi lfy na ganki yanzu?ta juya da gudu tana kuka yace me aka mata oho,yayi tambaya ya ba kansa amsa na mike da hotuna sai nayi gidan su Amira ban koma cikin gida ba ita ko Anty Mimi dakin Haj Yaya ta nufa da kukanta da komai,ta sanar da hajiyan komai haj yaya ta cika tamkar zata fashe ta dubi mimi tace kince yana rike da hannunta?Mimi tace sai kallon juna suke yi,haj yay tace lallai ma yaron nan jiya fa haka su Bilkisu suka ce min sun ga ya shiga mota da ita banyi maganin abun ba bari in kirashi,ta soma daddana waya tana fadin kannanshi bai taba sa su a motarshi ba sai wannan bakar mummunar yarinyar,ta soma magana kazo yanzun nan ta kashe wayar taci gaba da fadin sun asirceshi shima kamar babanshi na shiga uku ni Murja tsakanina da Habiba Allah ya isa ban yafe mata ba,yayanmu yayi sallama ya shiga dakin tana zaune kan kujera sai cika takeyi ya ballama Mimi harara sannan ya shiga ya zauna,duban wulakanci ta mishi sannnan tace yanzu kai saboda Allah me ke tsakaninka da yarinyar nan Iman yar karama da ita shine ta ke juyaka ta shanye ka nan gaba ma kila kace aurenta ma zakayi ko?ya sunkuyar da kai kasa bai amsa mata ba tace jiya ina kukaje?yace Haj waya kawo maki wadannan kananan surutan ne?nifa mutunci ne tsakanina da yarinyar nan tana hidima dani sosai don Allah haj ki daina jin zancan mutane yarinyar nan ita da uwarta suna da kirki kum....ta katse shi an baka kaci a cikin abinci ba dole kace haka ba na gaya ma ka koyaya ni zan mummunan saba maka ta nuna Mimi wannan ita menene laifinta?da zaka sasu a kasuwa sai kowa ya riga zabar Mimi kuma zanyi maganin agola a gidan nan wayarta tayi kara ta dauka ta duba ka dai ji na gaya maka ga babanku nan ma ya dawo shi ne yake kira bari naje,ta dube shi sai ka bata hakuri ai,tana fita ya galla ma Mimi harara sannan yace ke ma zan yi maganinki bakina hada ni da uwata ba ya mike ya zo kusa da ita wllh wllh in kika kuma hada ni da ita sai na fasa auran nan ke ko an daura sai na sakeki akan Iman, Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Yayi waje ya barta cikin mamaki da tsoro koda haj yaya ta dawo bata sanar da ita yanda suka yi ba ta dai ce ya bata hakuri ya tafi haj yaya tace ai nasan zai rabu da yarinyar nan sai ma kin shiga gidanshi Mimi tace haj ce min yayi fa in anyi bikinmu da sati biyu zai tafi england ya barni dama yaje dani don akwai masu mata a can,haj yaya tace gsky haka za'ayi sai dai za'a yi fama kafin ya yarda na ma huta hankalina ma ya kwanta baya kusa bare in ta fargaba kar yace yana son yar iskar 'yar can shima Kabiru zuwa zanyi na matsa mishi yayi auran tunda yana aikinshi dama jira nake yayanshi yayi tukunna cikin farin ciki Mimi ta fita ta san da haj yaya ta mishi magana shi kenan zai yarda su tafi tare. Da yamma na dawo daga gidansu Amira in da ta nuna min gwaggwaro ba tace don Allah kisa yammata kowa zai sa mu uku iri daya ?ami ta sai mana kalar namu daban ne ma nace to in ya shiga da kayana zansa danni ba anko zan sa ba tace me zaki sa?nace kayan gun yayanmu,a falonmu su hajiyar maska ce da sauran dangin alhj wadanda suka zo biki na rusuna na gaishe su sannan na shiga dakinmu sai da naci abinci sama sama sannan nayi wanka ina gaban madubi ina shafe shafe waya tayi kara na dauka ga mamakina sai naga lambar yayanmu ina da lambar amma bai taba kirana ba nima ko da wasa ban kirashi ba nasa kunnena ban ce komai ba inaji yace hello?sannan yace kina jina?a kasalance nace umm da wani abu nake ji yana fita daga wayar zuwa cikin kunnena yana raba ma jikina qani sako ne mai wuyar fassara yace me kike yi yanzun?na samu kaina da rike murya nace mashi ina shafa mai ne yace to kiyi kwaliya da kyau amma kar ki kula ko wanne saurayi kinjini?nace eh dukkanmu muka yi shiru bai kashe wayar ba nima haka can yace to sai mun hadu a can ya kashe na rungume wayar a kirjina ina jin tamkar shi na rungume,soyayya kenan ban taba tunanin akwai ranar da zata zo na shiga irin wannan halin ba sai gashi yanzu ina ta nutso cikin kogin son wanda bai ma san inayi ba,Allah kenan shi ne mai iya sanya fari ya koma baki.Kwaliya sosai nayi tamkar ni ce amarya nasa lesa din da ya umarceni nasa ya shiga da gwagwaron sai takalmi da jaka su ma kalan gwagwaron ne ni kaina dana dubi madubi sai da naji tsoro don kyan da nayi wayar Mami na kira tace min tana can hotel din na kira Amira tace min tana mota ne taga an gama kwashe mutane shine taga kabir ta tambayeshi ni shine yace kamar ya ganni a can ace mata ina gida ko fitowa banyi ba na mike na cire gwagwaron na rike na fito falo dankwalin na rufa kaina nayiwa mama sallama tace kai kin ko yi kyau,iman yau dai ba zancan hijabi kenan?nayi murmushi na fita ina isa harabar ajiye motoci duk an gama kwashe mutane sai kawayen amarya na nufi waje da nufin in hau mashin sai ga yaynmu shi da Nasir da wani abokinshi ya dubeni yana daga cikin yayi min alamar in tsaya da ido na ko tsaya ya fito ya kirani gefe yace kin ganki kuwa?kinyi kyau fa nace nagode yace to ya baki tafi ba?nace ai yanzun na fito shine naga an watse sai kawayen Amarya yace kina da kudin liki ne?nace ina dasu amma ba sababbi bane yace ok bari mu shiga ki amsa na bishi abokanshi na zaune a falonshi ya shige uwar dakinshi jim kadan yace Iman na ce na'am yace zo na shiga da sallam ya amsa sannan yace shigo mana kin tsaya nan kudi na gani a kan katifarshi ga yan ashirin ga yan hamsin har zuwa dari biyar,ya dubeni dauka wanda kikeso na sa hannu zan dauki ashirin ya dafe hannuna sannan yace ki dau wannan yan dari biyu ne,ya samin a tafin hannuna na gode na fada ina kallon idonshi,Man din akwai sirrin kyau mai birgewa muka fito falo ismail ya dubeni yace kai maska wannnan yarinyar ko dai kai kake ma kanka farauta ne? Sai naga yayi kicin kicin da fuska ya harari Ismail yace ku kun cika yarda girma ban da yarda girma menene na cewa inayi ma kaina farauta? bani son haka,jikina yayi sanyi zan fita yayanmu ki jirani zan sa akaiki Ina tsaye a bakin gate yazo ya dubeni menene kike bata ranki?na dubeshi ba komai ya juya ya kira musa musa direba yazo yace ina zaka na ganka da key a hannu?yace haj ce ta aikeni gidan haj laure,yace to ka kai Iman gurin party nan hotel yace to can na sami su Mami da kowa yana ta hidimominsa inata neman Amira sai can ita ce ma taganni muka zauna kujerun gaba na ce uwar sauri shine kika wani taho Amira tace kar kiga laifina yayanku Kabir shi yace min kina nan,nace don ni ce zan shirya gun ba?dole na riga kowa zuwa yana sani don dai ya dauke ki ne ta ce anji ki min shiru mu bar zancan.Biyar saura ango da amarya suka zo less dina na gida irinshi amarya tasa nace gara da na sa wannan din na dubi ango sanye yake da wata dakakiyar shadda ruwan sararin samaniya tamkar less din jikina ina cikin mamaki Amira tace kunyi anko ke da ango sanya gwagwaron ki nasa na gyara cikin raina nace kila ma don muyi anko ne yasa yace nasa,mai gabatarwa ya fito yana kiran kawayen Amarya bayan bude taro da addua suma abokan ango an kirasu yawanci duk turawa ne,sai kadan,Nasir da Mami aka hadashi tako sha harara gurin ango can aka kira sunana Iman idris zata ba amarya shawara ba don na iya turanci ba da nasha kunya Amarya ta cika don haushi niko duk na tsargu Amira tace don Allah tashi kije mana nace Amira bansan me zance ba dadai tun a gida ne aka sanar dani da na rubuta ana ta kiran suna na na dubi yayanmu yamin kar da ido fuskarshi ba walwala na mike daidai lokacinda mai gabatarwa yace ko bata nan ne?Iman Idris a hankali nake tafiya har naje kan abinda aka tanada don hawan mai magana da sallama na soma sannan nayi wa Annabi salati kafin na soma bata shawara akan zaman aure na kawo ayoyi da hadisai wadanda sukayi magana akan zaman auren da hakkokin auran kansu. Dana gama na sha tafi gun mutane na koma na zauna haka akayi ta gabatar da komai har zuwa sanda zasu ciyar da juna don kar in gani na dauko wayata ina ta danne danne zuciyata kuwa sai zugi takeyi,can na mike zan fita Amira tace ina zaki je gashi shalele na ta waka yanxun za a soma rawa dole na tsaya suna shiga yayanmu a tsaye yake baya rawa amma Amarya har da juyi nace wawiya ba kunya ba jan aji nice na fara liki