← Book details Tawa Ta Sameni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 22

Sashe 22

Tawa Ta Sameni Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ina ta zuba musu kudi cikin dauriya yayanmu ya juyo ya fara zuba min na juya zan fita ya rike min riga amma ba wanda zai kula don ta gefe ya rike ya dan matso kusa da kunnena kar ki fita yanzun ki min rawa din dan ban iya rawa ba nima ai ban iyaba Amarya ranta ya baci ta dubeni ashe ita ta kula da abin da mukeyi guri ya kaure liki wasu sun sha nice amaryar ne?ko ra'ayi ne?oho sai ni suke ma liki gudun rikici yasa na fita abina na koma na zauna,Amira tace yar gori a ina kika sami kudi kike bari dasu?nace shi ya bani dubu ashirin kuma na like musu abinsu Amira tace duka?nace a'a Mami ta iso gunmu taja hannuna zo muje ki dan taka nace bana rawa fa ta dubi Amira tace duk yanda suke da yayanmu wai bazata yi rawa a bakinshi ba Amira tace ai ta basu shawara yanda zasu zauna da juna,Mami tace yauwa na tuna dazun me yace miki da naga ya wani karkato dai da kunnank?nace ba zan fada ba Amira tace ashe kin lura kema?sunyi kyau tamkar itace amaryar nace kun cika sharri Mami tace to zamuje kiga hitunanku da masu hoto sukayi suna ta saidawa a waje mu uku muka fita wajen hall din gsky mami ga hotunanmu nan nida yayanmu wani tare mukayi wani ni kadai wani shi kadai an barbaza wanda yafi birgeni wanda mukayi da yayanmu ya dan karkato yana min magana fuskarshi a sake ni kuma ina murmushi fuskata tayi fayau idanuwana sunyi haske kitsona ya zuba a kafaduna Duk masu daukar hoton nan sai da na bisu na saye hotunanmu sannan muka koma ciki nace kije kunnan gidado tace a ina zaki ganshi ta fita kiran,ni kadai na zauna can ji an min sallama cikin hausa da bata goge ba yace na zauna?nace zauna mana ya zauna nadan dube ahi kamar na so na gane fuskarshi yace baki ganeni ba?nace ban ganeka ba yace abokin Maska da muka zo daga England nace ok na ganeka,yaci gaba da cewa ina sonki amma Maska yace krt zakiyi? nace haka ne yace toh zan jiraki mana nace kayi hakuri dan zan dade ban gama ba,koyaushe zan jiraki,muna cikin hirar ne can idona ya kai Ango da Amarya harara ya sakar min na dauke kaina daga duban gunshi a raina nace kai gara kai ka kama taka naci gaba da hirata jim kadan wayata tayi kara na duba sai naga lambar yayanmu da sauri na dubi gurin da yake bashi nan sai na dauka nace hello ya katseni ki sameni a wajen hall din nan gurin wayoyin nan ta kofar baya na fita da sauri can bayan wasu furanni na ganshi na isa cikin fargaba ya dubeni fuskarahi ba annuri yace me gayen nan yace miki?nayi shiru ba zaki gaya min ba?ya daka min tsawa jikina yana rawa nace yace ne yana sona,da sauri ya dubeni sonki?.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Na gyada kai alamar eh yace oh my God bana sanar dashi krt zakiyi ba?to naji me ke kikace mishi?nace nima haka nace mishi ya dunkule hannunshi ya naushi dayan hannun sannan ya dinga kai kawo a filin gun mamakin shiga damuwar dayayi na tsaya yi a raina nace ya bar amaryarshi yana yin abin da bai dameahi ba,kamar ya san tunanin da nakeyi sai naji ya dawo gabana daf dani yasa hannuwanshi ya rike kafaduna yace kar kiga na shiga wannan halin kiyi tunanin inayin shishigi ne a cikin abinda bai shafeni ba,no yin karatunki shine kwanciyar hankalina kuma muddin na yarda wannan dan iskan ya soma cusa maki ra'ayin sonshi to zai min illa domin nasan Adam ba sanin yau ba yana da sa'a a rayuwarshi zai yi wuya ya nemi abu bai samu ba tamkar ni yake,so bazan yarda da huldarku ba,nayi shiru ina tunanin wannan iko na yayanmu tunda yace tamkar shi yake sai ma naji ya burgeni na dubi yayanmu nace to in dai zai bari na gama karatuna why not na aureshi in kasan yana da hali mai.....kafin na karasa sai saukar mari naji cikin firgici na dube shi shima ni yake kallo ranshi a bace,hawaye ya zubo min a kan fuskata yace kina hauka ne?kike kiran wani ya aureki?sai kuma naga yayi shiru ya juya min baya,Aminatu yaja sunan kafin na amsa sai ya juyo da sauri ya zo guna ba zato sai gani nayi ya rungume ni tsam tsam a jikinshi gabana yana faduwa jikina na kyarma amma na kasa kwacewa ,nama kasa kokarin kwacewar gwaggwarona kaina ya fadi gashina ya bayyana a waje kitsona ya sauka a kan kafaduna ni kam tamkar an jona ni a lantarki haka nake jina,cikin sanyin murya yake magana,Amina bana son ki saurari Adams zaiyi ma rayuwata illah nafi son sai kin gama karatu ne kafin ayi maganar auranki,ki fahimceni ba ina nufin hanaki aure bane a'a ina son kiyi krt ne,wani haushi naji ya kamani domin a lokacin nayi zaton zai ce min yana sona ne,yanda naga yayi mugun shiga damuwa sannan ya kamani ya wani rungume yana faman ajiyar zuciya tamkar jinjirin daya kwana uku ba tare da ya sha nonon uwarshi ba ina fama da sonshi tamkar na mutu shi kuma ya nan yayi aurenshi sannan ya zo ya wani rungumeni yana min maganar banza nasoma kici kicin kwacewa ya girgiza ni yace come on my sister ki.....kafin ya karasa maganar da zaiyi sai jin salati mukayi akanmu,cikin tsananin tsoro na juya su dayawa daga cikinsu akwai kannanshi da Amarya da Haj Laure uwar Amarya da wasu daga cikin danginsu,duk tsoro ya kamani,Amarya tasa kuka na dubeshi shi kuma ko ajikinshi duban su ma yake yi na tattare zani zan gudu sai naji ya sa hannu ya riko ni.......Masha Allahu Alhamdulillah, mun Kammala littafi na daya Mu hadu a littafi na biyu jinjina agareki HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Share

DOCUMENT CREATED BY
ZAHARADEEN SHOMAR
WHATSAPP ,,08168575100
Chapter 22 · 0% Book details