← Book details Tawa Ta Sameni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 22

Sashe 15

Tawa Ta Sameni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama taga abin ya isheta bani magana sosai koda yaushe a kwance ga jarabawa ta matso amma bana wani krt sati da lahdi suka zo suka wuce amma banje islamiya ba wato (sanawiyya),Ranar monday mama tace kar naje makaranta na shirya muje Asibiti nace lfy ta kalau tace na dai shirya muje kawai rimi clinic mukaje mama tayi ma likita bayanin yanda nakeyi,likita ta barshi dani bayan fitar mama sai likita ya dubeni yace sanar dani yadda kikeji sai nace kasala nikeji sai kirjina da ke min nauyi kuma bani son yawan surutu yadan gwaggwadani sannan yace kina yawan tunani ko?nace eh yace to tunanin me kikeyi?nace ba komai yace karya ne da na rasa ta cewa sai na ce jarabawa ce nake tunani ba dan ya yarda ba yace to shi kenan ki daina yawan tunani kisa Allah a gaba ya rubuta mana magunguna muka tafi,haka nayi ta shan magunguna amma tamkar ana zugani Mama ta koma na gargajiya ni dai nawa shane a haka jarabawa ta same ni mukayi ta nidai ban sa rai da zanci ba ranar da muka gama ne a nata murna masu hoto nayi,niko sai kallon mutane nake,Mami ta dafa ni tace ga wata yar ajinku can tana nemanki nace ina take?ta nuna min ita ashe Hauwa'u Aminu ce nan tamin korafin rashin sanin gidanmu ita kuma ta bani no wayarta ni kuma nace mata in na fara anfani da tawa sai taga tawa lambar,sai da zamu bar harabar makarantar ne sannan naji duk kewar makarantar ta ka mani.Abdulrahim zaune a kan kujera a cikin falon Hotel din da yayi masauki, ko nace nan ne dama club dinsu suka kama mashi tun farko,kanshi yana jingine a bayan kujera, tebur ne dan karami cike da kayan ciye ciye da shaye shaye amma sam ya kasa cin komai tunanin yakeyi wayarshi tayi kara ya juyo ya dube ta kamar kar ya dauka sai kuma ya dauka Mimi ce ta kirashi bai san dalili ba sai yaji wani kunci a ranshi amma sai ya daure ya dauka,tace yayanmu kana lfy?yace lfy kalau,yake dinfa?tace ina nan lfy dama naga tunda ka tafi baka kira ba ne,yau kwana shida kenan?yace ban sami dama bane,tace to ina jiran kiranka,yace to kawai ya kashe wayar juyawa yayi ya dubi abincinshi kusan minti arbain kenan da kawo abincin amma ya kasa ci ya kai hannu ya bude plate din abincin da yafi so yayi order amma sam sai yaji kamshin abincin ma baya mishi dadi kokadan a fili yayi magana yace yarinyar nan ta bata ni da kalolin abincinta masu dadi,yayi shiru yana tunani tun zuwan shi kasar nan bai wani ci abinci ba daga ruwan lipton sai dambun naman nan,kwankwasa kofar akayi ya bada izinin a shigo ne abokinshi ne shima dan kwallo ne amma shi bature ne ya dubi Abdulrahim sannan yace cikin turanci Maska naga baka shirya ba ne,wannan karon baka so dawowa ba ne tunda ka dawo sam baka da kuzari,me yasa?Abdulrahim ya mike yana fadin tunanin gida nakeyi ya shige dakin barcinsa shima ya shiryo cikin JC na training suka fita.A daran daya cika kwana bakwai da zuwa yana zaune a harabar Hotel din haske ne ya kewaye gurin kamar rana gabanshi gwangwanin coke ne da dan karamin plate cike da dambun nama sannan ya kai hannu ya dauki wayarshi ya soma sana'ar wato danne danne wayarshi can yayi tsaki ya kashe wayar ya mike,da ya kamata ya nufi gurin abokanshi ne tunda ba dare ne yayi sosai ba kuma yasan zasu sa ran zuwansa, amma sam sai yaji ba zai iya ba saboda wani abu da ya taba zuciyasa sama ya nufa dakinshi ya zauna a bakin gado sannan ya aje tarkaccen hannunsa a kasa wayarshi ya rike sannan ya soma sarrafata cikin kwarewa, Babanshi ya kira bayan ya dauka sai yace Alhj ina yini?bayan sun gaisa sai yake cema Alhj dama ya kira ne dan ya amshi lambar wayan Maman sagir domin yana da lambar kowa a gidan itace bai da ita,Alhj yace gata nan ma Habibar ku gaisa,bayan sun gaisa ne sannan ya bukaci lambarta ba tare da wani tunani ba ta bashi,ya jima yana tunanin dalilin karbar no kafin daga karshe ya gane sai dai wani tunaninshi abin zai zamar mashi abin kunya da nunawa cikin abokai,muddin suka san halin da yake ciki,nan a dalilin wata kankanuwar yarinya wacce da yayi auren wuri tabbas zai haifi kamarta.Kwance yake akan gadonshi amma sai sautin daddadar muryar yarinyar yake dawo mashi ya tuno ranar da bashi da lfy duk gidan ba wanda ya kula dashi tamkar ita muryarta ya tuna sannu yayanmu za ai maka wani abu ne?ya sake tuno yanda ya kara tsorata ta ranar da ta daukan mashi kujera tabbas in tana cikin tsoro tana matukar burgeshi yayi magana a fili inda yace nayi missing din ganin tsoranki. (Lallai Iman kinga takanki, mudai daganan sai muce! Allah yakyauta) Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Ya cigaba da juyi a kan gado ba komai ke dawainiya dashi ba sai begen yarinyar da yake gani abin kunya ne ace ya sota ya tuna da mimi yarinya mai kyau jinin larabawa sai dai shi baya jinta a ranshi yanda yake jin wannan yar mitsilar yarinyar zai auri Mimi ne kawai don bin umarnin mahaifiyarshi kuma ya san duk inda suka shiga ba zai ji kunyar nunata ba a matsayin matarshi shekarunta ashirin da biyar shi kanshi shekara biyar ya bata bugu da kari gashi ta soma zurfi a karatunta,amma in yace wannan yarinyar zai aurà shima yasan rigima zai jawo,yanda mahaifiyarshi ta tsane su wata zuciyar ta ce mashi ga yaran nan da rashin kunya tana jin kace kana sonta to raini ya shiga tsakaninku gara ma Mimi hadaku akayi kuma kasan ta mutu kanka don haka baza ta maka wani rawar kai ba,"A dawo lfy Allah ya bada sa'a" ya kuma tuno muryata da yaji na karshe sannan lokacin da ta rakube a jikin bango tana mashi bye bye ya dawo mishi tausayinta yaji lokacin kuma jikinshi na bashi kamar itama tana jin yanda yake ji a ranta,zaune ya mike yana magana shi kadai tamkar wanda ya tabu yana fadin Amina kiyi hakuri bani da shà'awar auran mata biyu ki bari in runtsa ya kuma fadawa kan gado.Niko yanzu na zama kurma bana magana sosai ban kuma cika son magana ba sai dai maganar su Amira ce ke damuna da suka ce wai ina ciki mayen soyayya na dai ki sanar dasu wanda nake so,inko har zancensu gsky ne to na debo da zafi don ko in har yanda zuciyata ke mani game da yayanmu so ne to ko shakka babu gara na rufa ma kaina asiri nayi shiru da bakina don nasan ko yaji ubana zaici don nasan ni ba ajinshi bace,me kamar Anty Mimi? Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 kammala karatuna shi ya ba samari damar damuna tamakar anbi su an gaya musu musamman ma yaya Kabir shine yasani wannan ya sani wancan,su yaya ma suna zuwa,ban manta wata rana yaya Kabir ya aiko Sagir dinmu ya kirani na fito na sameshi a daki kan kujera na zauna fuskata na kallon wani katon hoton yayanmu sanye yake da JC kore da fari irin na yan wasan Nigeria hannunshi a kan kirjinshi daga gani lokacin suna taken Nigeria ne aka dauke shi,muka gaisa da yaya Kabir ya soma yi min zancen soyayya niko hankalina ba ya tare dashi, yayanmu kawai nake kallo da kyaun da Allah yayi mashi ba abinda ya birgeni irin shedar sallah daya fito mishi a saman goshinshi yayi baki tamkar ya diga ina cikin wannan tunanin ne naji yaya Kabir na min magana da karfi nayi ajiyar zuciya sannan na dube shi nace ka gama?zan shiga gida yace na tambayeki baki bani amsa ba nace ni ban wani jika ba na mike nayi waje yana kirana na fito kirana naji anyi daga bakin gate ko ban juya ba nasan yaya Abubakr ne dogon tsaki naja sannan naje ina zuwa na hau shi da masifa shima kallona naga ya tsaya yi,ina cewa nace ni ba aure zanyi ba amma kun dameni don Allah ku rabu dani ko dole ne?na juyo abina wani abin haushi ina shiga falonmu sai ga yaya Suleiman zaune suna hira da Mama...(hhhhhhhhha.yarinya taki tasameki.) dakin kwananmu na wuce nayi kwanciyata naki fitowa ban fi minti goma ba mama ta shigo ta dubeni tace Sulaiman ya dade yana jiranki wai me kika tsaya yi wurin Kabir din?nace ya aike nine bayan na dawo kuma sai na gamu da da yaya Abubkr na cigaba da cewa gsky ni dai mama ki samu su yaya Abubkr kiyi musu magana nifa ba aure zanyi ba su rabu dani mana,mama tace aike ma yan uwanki ne kuma nasan in ki sanar dasu zasu kyaleki sannan suna ganin girmana sosai bazan iya tunkararsu da wannan zancen ba, nace haka fa shekaran jiya yaya Ibrahim yazo wai har yana takama zaije ya samu babana kuma ko ina so ko bani so shi zai bashi ni mama tace to bisimilla ai ga kinan taci gaba da cewa don haka ma ni koda auren ne cikinsu gara Abubakr din nace ni dai dukkansu har yaya Sulaiman din hakuri zaiyi dani dan bana son auren zumuncin nan mama ta fita tana cewa dai gashi can ku gaisa,na dauki hijabina na fito falo fuskata a daure muka gaisa yace to Iman gani dai na kuma dawowa duk da kin sanar dani krt zakiyi shine na yanke shawara ki yarda a daura mana aure ni kuma zan yarje maki kiyi krt har kiga karshen biro nace mu bar zancen nan, ina Nana?yace Nana tana nan jiya aka sa ranarta goron ne ma na kawo ma Mama nace lallai Nana yanxu itama auren zatayi?yace shine mutuncin duk wata 'ya mace nace to Allah yasa alkhair ni zan shiga na kwanta ka gaida min da su baba uwa kace da Nana inna jiran zuwanta, yace amsata fa? ko zaki yi min waya don Mama tace kin soma amfani da wayarki nace jiya na soma
Chapter 15 · 0% Book details