← Book details Silar Graduation Party Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 12

Sashe 12

Silar Graduation Party Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Duka *SILAR GRADUATION PARTY* mama Kinga halinda bira take ciki, kaicomu rayuwarmu *SILAR GRADUATION PARTY* yamuna mugun tabonda saidai mu mutu dashi, Allah ASTAGFIRULLAHA Allah kaimuna Aikin gafara, Allah muntuba Allah" wani kuka tasake saki, Hakama Aman Sosai yayi kuka gamida tuba, Wa'azi gamida fad'a kuwa sunsha shi, _BAYAN WATA D'AYA_ Zaliha tahaife y'arta k'yak'yawa Rok'onta Abas yayi kansu saka Mata sunan Ambi hakan kuwa ta kasance, sosai Ambi taji dad'in karanda Abas yamata.. "to Wai Ambi haka Zaki zauna ba Aure ne" cewar mama Mik'ewa tayi Zaune daga kwancenda take Cikin mutuwar jiki tace"Mama wakike tunanin zai iya Aurena Bayan ba Wanda baisan Abunda muka Aikata ba nikam ai narasa farincikina Tindaga sanda *SILAR GRADUATION PARTY* ya auku" Dafa kafad'arta tayi Cikin tausayawa tace"Waya fad'a Miki Hakan duk da nasan Abunda kuka Aikata laifine Mai Muni Amma ai Baki Aikata zinaba WALLAHU GAFURUL RAHEEM, tayu saboda Allah yana k'aunarku da Rahamarsa shiyasa yabarku raye haryanzu saboda wasu lokutan Allah yakan bawa bawansa Damar domin yagani shi zai shirune ko A'a zaicigaba da Aikata FASADI ne Saboda Haka kudage da tuba Kuma miji Zaki samu koma nace kin samu" Mik'ewa tayi Zaune Cikin mamaki tace"Nasami miji kuma,"? "Eh sosai iyayen Aman sunzo neman Aurenki Kuma munbasu domin lurada da Aman d'in Shine Abokinda kuka Aikata laifin tare saiku had'a kanku domin neman tuba ga Ubangiji" Girgiza kanta Kawai tayi sai hawaye domin dai tasan tarasa Abas har Abada Kenan dama Dole watsatstse saidai yasamu watsatstsen bawai mutumin kirki ba domin Allah baya tab'a cutarda bawa saidai Shi bawa ya cutarda kansa Babu Abunda Kuma yajanyo hakan face *SILAR GRADUATION PARTY*,.. B'angaren Aman ma ya d'auke hakan matsayin k'addara gamida cutarwa daga *SILAR GRADUATION PARTY* Haka Ad'aura Auransu badan kowa daga cikinsu yanason d'aya ba saidai *SILAR GRADUATION PARTY* yasaka Dole su Rayu dajuna........ Tinda yashiga d'akin yad'auke kansa domin yakasa yarda kan Ambi ba ba y'ar iska bace, dak'insa yashige yayi kwanciyarsa cikeda kewa gamida danasanin Abunda ya aikata gashi yak'are da wadda baitab'a tunanin zai aura ba K'aramin tsaki yasaki tareda kwanciyarsa, Sarai taji motsin shigowarsa saidai ganin baizoba yasa takwanta cikeda bak'inciki domin da Yanzu tanacan da farincikinta tareda Abas bawan Allah Kuma mutumin kirki, tana cikin Wannan tinanin bacci ya d'auketa, Dasafe suka had'u parlourn gaidashi tayi kamar baijiba zama tayi gefe cikin mamaki tace"Wai meke damunka Aman nalura Yanzu ko son ganina bakayi Gaba d'aya" "Ke dalla rufamin baki tayazanso zama dake Bayan kingama zubarda Mutuncin Awaje kinrasa Mai d'aukarki shine Ni Aka yayabamun masifa" Cikeda mamaki take kallonsa"bangane ba mekake nufi Aman kallon y'ar iska kakemin,"? "Hunm kallo to ai idan nace kallo to banyi Abunda yadace ba Gaba d'aya a y'ar iska karuwa nake d'aukarki" Kuka tafashe dashi" tace Aman nikake jifa da Wad'annan munanan kalamai,"? "To ai duk Abunda nace kin cancanceshi ne inba y'ar iska ba karuwa taya Zaki wanke k'afa kije party har kiyi rawa da maza bako Kunya ai duk maccen da zata iya zuwa Cikin dubbannin maza tayi rawa da shiga Mai bayyana surar jiki to Dole ta Ansa sunan y'ar iska," "Kodai mu k'arb'e sunan y'an Iska ba domin duk Abunda yafaru tare muka aikata ai Kuma Saboda Kai yasa mutumin kirki bawan Allah yafasara aurena kafi kowa zama d'an Iska da......." Tas tas tas tas ya d'auketa Mari kusan sau hud'u tako wanne kumatunta, Cikin b'acin Rai yace"Ni Zaki Kira d'an Iska saboda bakida tarbiya ko, yau Zanyi maganin Rashin kunyar ki ai," zare belts d'insa yayi yarufetada duka sosai ta ko ina, ihun neman taimako amma bakowa hakan yasa yamata shegen duka yafarfasa mata jiki Cikin huci Kuma yace"kije nasakeki saki uku Domin bazan tab'a iyazama dake ba Shegiya karuwa kawai," kwashe kayansa yayi yabar gidan, Zaliha da Abas ne sukazo gidan domin Basu gari Koda Akayi bikin Kuma yanzu sunzama d'aya da Ambi Shigowa parlourn Zaliha tayi da sallama shuru cigaba da Shiga tayi idanuwanta suka fad'a kan Ambi dake kwance kasan tayil d'in Cikin jini, Ihu tasaki gamida Kiran Abas Shigowa yayi cikin tashin hankali Suka kaita Asibiti cikin gaggawa Akashiga da ita emergency room domin tadaku sosai, Kiran iyayenta dama na Aman sukayi sukazo cikeda jimami saibayan Awa Uku tafarka da kuka Nan take Basu Labarin Abunda yafaru dama sakinda yamata, sosai Zaliha taji tausayinta Abas kuwa Rok'on iyayensa yayi yasamu suka Amince itama Zaliha ta Amince tinda babu Abunda yashiga tsakaninsu da Aman Hakan yasa Akasake d'aura Auranta da Abas sosai hakan yamata farinciki musamman daya sameta virgin Nan duk zarginsa gamida ita yakau daga itanuwansa yamanta Abunda yafaru Wanda idanuwansa Suka tab'a gani kanta, sosai Suke zaman lafita tsakaninsu, Nan Kuma labarin rasuwar bira yasamesu sosai Ambi taci kuka gamida nadamar Rayuwa da k'ara Shiga tsoron Allah domin Kuwa *SILAR GRADUATION PARTY* sunga k'addara kala kala, Aman Kuwa Lagos yakoma can yayi Auransa yaja tunanin yasami Matar kirki sai Adarensu na farko yagano Ashe ba budurwar bace Atak'aice dai karuwace daga baya yasami K'arin labari sosai yayi nadama da bak'incin rayuwarsa gamida tsinewa GRADUATION PARTY Domin a *SILAR GRADUATION PARTY* yarasa Matar kirki wato Zaliha Kuma *SILAR GRADUATION PARTY* yasa yaci zalin Ambi gashi *SILAR GRADUATION PARTY* ya Aure karuwa Kuma iyayensa sun hanashi rabuwa da ita hakan yasashi mugun sanyi danadamar Abunda ya aikata tuba ga Ubangijinsa yayi gamida neman yafiyar Ambi dama Zaliha d'in dole ya rungume matarsa itama Kuwa ta tuba dama sau d'aya ne ta Aikata, Dukansu kullum Cikin tuba suke gamida nadama domin *SILAR GRADUATION PARTY* rayuwarsu tasamu tangard'a kullum sai k'ara tuba ga Ubangijinsu suke.................. ALHAMDULILLAH _ANAN NAKAWO K'ARSHEN WANNAN LITTAFIN INDA NAYI DAIDAI ALLAH KABAN LADA INDA NAYI KUSKURE ALLAH YA GAFARTAMIN KUMA READER'S KUMUN AFUWA... ALLAH YABAMU IKON D'AUKAR DARASI MAIKYAU DAKE CKIN WANNAN LABARIN MARA KYAU KUMA ALLAH YAKAREMU, ALLAH KATSARE MUTUNCINMU DAMA IMANINMU.... AMEEN........TAKU HAR KULLUM MUJAHEEDAH MATAR MALAM AMMYN KHAUSAR QUEEN OF WRITER'S HAUSA NOVELS MES_MLM WRITER'S AND DESIGN GRAPHICS_

_BASEERATA ITACE ARZIKINA
WhatsApp number 07064904617 or 07031012948
SummaryInformation
DocumentSummaryInformation
WpsCustomData
TECNO LD7
WPS Office
Normal
Times New Roman
Times New Roman
Calibri
Calibri
!%),.:;>?]}
$([{
f31cda076c0840ddbefc0f55c0cf2509
Chapter 12 · 0% Book details