← Book details Shimfidar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 12

Sashe 6

Shimfidar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"a'a aunty wlh tsoro nakeji ni bazanje yanzuba".

.
.

Maryam d'akin ta takoma, ta dad'e a tsaye tana tunanin ta fara aikin da Ummu ta sata yau ko kuma ta bari, da sauri ta janye tunanin ta tafad'a toilet, ta dad'e tana cud'a jikin ta da had'in sabulun da Auntyn ta (k'anwar Mamy) ta had'o mata, tana fitowa ta goge jikin ta tazauna a gaban mirrow, b'arin humra tayi wa jikin ta kamar babu gobe, simple makeup tayi ta saka riga da siket wanda d'inkin ya tafi da shape d'inta, acikin d'inkunan da ummu ta matane, d'auri ta zauna ta cancara, tayi kyaw sosai, ta k'arewa kanta kallo a mudubi tayi murmushi, ta ce yanzu nazama mace, Allah na gode maka da kawo Fateema rayuwa ta da yanzu ban iya komai ba.

.
.
.

.

Anwar tunda ya shiga ya kasa tab'uka komai sai tarin b'acin rai dayake sake shigar shi, shi baiga dad'ewar da Maryam tayi da za'a sata a gaba haka ba, koma dai menene yana son
matar sa koda bata haihuwa, a sab'ule ya mik'e yaje yayi wanka yanata mamakin yau basu biyo shi ba, yana d'aure da towel yana goge kanshi da wani, k'amshin turaren maryam daya had'e da humra ya doki hancin sa, sai da ya lumshe ido ya bud'e ya juya a tunanin sa Fateema ce yasan ita take saka rikitattun k'amshi a jikin ta haka, tsayawa yayi cak ganin Maryam, tayi masifar yi masa kyau ba kad'an ba, nan take ya manta da b'acin ran da yake ciki, cikin murmushin ta tak'ara sa gare shi, ta d'an langab'ar da kai tana turo baki ta ce "shine ka shigo kanata b'ata rai ko"?

rungumo ta yayi yazuba mata ido yana murmushi, a kunne ya rad'a mata "kinyi kyau Maryam".

Kiss tamasa a kumatu tafara karkaɗe masa ruwan kanshi da hanun ta, kallon ta yake tayi, tayi masa wani irin k'warjini, shi kaɗai yasan yanda yakeji har cikin jikinshi, tana kwalliya amma yarasa meyasa na yau yafara ruɗashi.

Duk wankan ki idan baki san irin kayan da zakisa mijinki yaji ajikinsa ba to duk aikin banza ne, kiyi shigar da idan yaganki jikinsa zai amsa shine magana.

Ta hure mishi ido ta ce

"kallon fa"?

murmushi yayi yasaka hanunshi ta k'ugun ta yajanyo ta jikin sa, ya mannata da k'irjin sa yana wani irin lumshe ido, kamar jira takeyi takai bakin ta saitin nashi tana lasa da harcen ta, (duk ummu ce takoya mata wannan dabaran).

cikin zak'uwa ya saka harcensa a bakin ta yafara juyawa yana tsotsa, numfashin Maryam har sama yakeyi, bata taɓa sanin haka abun yake da daɗi ba, sunkai kusan 30mnt ahaka, jin yafara zare mata rigane yasa tayi saurin ja da baya tana maida numfashi, ya dube ta da fitinannun idanuwan shi yakasa magana, ido ta kaɗa mishi ta ce "ka shirya muje kaci abinci"
Futa tazo yi, yayi sauri ya jawo ta, ta faɗa jikinsa, ya ce "kiyi hak'uri Maryam, ko kina haihuwa ko baki haihuwa inason ki ahaka, kada wataran sheɗan yazuga ki kiyi tunanin nayi aurene saboda haihuwa, ko kaɗan ban taɓa sakawa araina ba, duk naji abunda Hajiya tayi...
Hararar shi tayi ta ce "laɓe kakeyi ko"?
Yayi dariya ya ce "laɓen yayi amfani ai tunda na rage muku aiki".
Itama dariya tayi ta ce "Fateema tamun abunda bazan manta da ita ba, yau kaɗai naji inaso nasan wacece ita, da gaske sadakar ta aka baka"?

🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏
*SHIMFID'AR MIJINA*
🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏

.

.

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
PML
_We dont just entertain and educate we also touch the hearts of the readears_

.
.

.

Writen By *Princess Eshat Aysm*

.

.

Page 12

.

.

_k'irk'irarren labarine banyi don cin zarafin wani ko wata ba_

.

.

Saida yayi jum kafin yace "Bawanda ya bani sadakar Fateema, ni naganta naji inaso na aure ta".
B'ata rai tayi zata mik'e ya zaunar da ita ya ce "kiyi hak'uri".
Kuka tafarayi k'asa2, ita a dole ta koyi kissar kuka, ya kwanto da ita jikin sa ya ce "Bana son kukan ki, a farko na auri Fateema ne haka kawai badan so ko wani abuba, nidai tsintar kaina nayi da son auren ta tun ranarda na mata kallon farko, nayi ta addua Allah yasa auren yazamo alkairi a gareki, saboda kwanciyar hankalin ki akan auren zaifimun komai, bayan anyi auren na lura batada matsala, kuma har cikin ranta babu batun kishi, nayi ta ɓoye miki yanda nakejin daɗin zama da itane saboda kisamu nutsuwa da kwanciyar hankali, duk wani ɓacin rai dana saki acikin rashin sani ne, iyayen Fateema Talakawa ne Sosai, banyi tsammanin zan sameta tanada tarbiyya ba saboda yanayin shigarta, sai daga baya nagane al'adar garin ne haka, nadaɗe ina jarrabata nagane ko akwai manufar ta na cutarwa akanki amatsayin ta na kishiya amma bangani ba, yau nadaɗa tabbatar da Fateema abokiyar zamarki ce, abu ɗaya zan rok'eki akai shine, kada kibari wani ya zugaki ki nemi cutar da ita, na rok'eki".

Dukka hannuwan shi ta kama ta manna musu kiss tana dariya, ta ce "naji abunda nakeson ji, basai ka rok'eni ba, ina tare da ita".

.

.

Bayan kwana biyu.
Hajiya Jamila sai zuba ido takeyi taji labarin Maryam da Anwar sun rabu amma shiru, yau ta yanke hukuncin zataje gidan taji ko Fateema batayi abunda tasata bane, har tagama shiri zata futa taji shigowar Anwar, komawa tayi ta zauna tayi kamar ba wani waje zataje ba, cikin ladabi ya gaishe ta kamar kullum, da fara'a ta amsa tana murmushin yak'e da babu gaira babu dalili.

Hanu yasa a aljihun sa ya ciro maganin ya mik'a mata, farinciki fal ranta amma ta ɓoye ta ce "me zanyi da wannan? Lafiya ta law ka haɗani da magani"?

Ya sunkuyar da kai yana dariya, duk yadda yaso ya ɓoye dariyar sa saida yayi, yanda ta haɗa rai ne abun yabashi dariya, katse shi tayi da cewa "yaya zaka sani a gaba kana dariya kamar wata mahaukaciya".

Dariyar yasake yi kafin yace "Hajiya abunne abun dariya, ashe Maryam maganin da take sha kenan takasa haifa miki jika".

Tamau ta sake murtuk'e fuska ta ce "shine abun dariyar"?

Adana dariyar shi yayi ya ce "idan na tuna irin dukan dana matane abun yake bani dariya, ta cucemu Hajiya".

Daɗine yaso kashe Hajiya Jamila ta ce "banfa gane me kake cewaba, kana nufin batason haihuwa damu, saki nawa kamata"?

Cikin k'araji ta k'arasa maganar, saida k'irjin shi tawani yi k'ara jin an k'ira sunan saki, wani yawu me zafi ya haɗiye ya ce "Saki kuma Hajiya, idan nasake ta namata gata kenan, irin uk'ubar dana tanadar mata ya isheta azaba".

Ta ce "yanzu naji magana, tayaya akayi kaga maganin nan"?

"Hajiya basai namiki bayani ba, kinsan ance rana dubu ta ɓarawo ce ɗaya tame kaya".

"wannan haka yake, Allah yamaka albarka,itama ɗayar idan takai shekara babu bayani sai ka auro wata".

Murmushi yayi ya mik'e ya ce "ni na wuce".

Koda ya koma bai faɗa musu yanda sukayi da Hajiya ba, ce musu kawai yayi ya nunawa Hajiya yaga maganin, sannan yadaɗa baiwa Maryam Hak'uri, ta ce "haba husby menene na bani hak'uri".

Fateema ta ce "Allah yakawo miki haihuwa cikin gaggawa aunty".
Dukkansu suka amsa da ameen.

Abubuwa da yawa sunfaru, zaman mutunci da amana su Maryam sukeyi, ba inda zasu shiga ace kishiyoyi ne, idan 'yan uwan Fateema sunzo duk a wajen Maryam suke tarewa, ta jasu a jiki tamkar itace 'yar uwar tasu, Albarka kam kullum Maryam tanasha a wajen Anwar, takance Fateema ce abun sanyawa Albarka tunda ita tashigo gidan da kyakkyawar niyya, shi kuma yakance duk kyawun niyyan ta idan baki karɓeta ba baza'ayi zaman lafiya ba.

Fateema takanje ta wuni wa Hajiya Jamila, gata kam tana gani tun lokacin datayi aikin da tasa ta.

Maryam kam ta gyara shimfiɗar ta sosai har tafi Fateema k'warewa saboda dama tafi ta kyaw nesa ba kusa ba.

.

.

Yau ta kama Lahadi tun safe Maryam ta tashi da wani irin mura me zafi, har yafara saka mata zazzaɓi, ga tare daya sauk'ar mata lokaci guda.

🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏
*SHIMFID'AR MIJINA*
🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏

.

.

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
PML
_We dont just entertain and educate we also touch the hearts of the readears_

.
.

.

Writen By *Princess Eshat Aysm*

.

.

Page 13

.

.
.

.

*Zahra Bello*

"Very interesting book wlh kin burgeni me book dinnan rubutun ki yazo da salo na daban".

.
.

*Zahra Bello*

"Duk book din dazaa rubuta inde an had a mata biyu to se ansa ana rigima da bin boka Amman wannan ya banbanta. Keep it up".

.
.

*Ameenah Ali Musa*

"Gaskiya kika fada zahra, marubuciyar tasauya akalar zamantakewar kishiyoyi d sabon salo, Allah yasa masu kishiya suyi koyi d Maryam D Fatima."
.

.

*Zahra Bello*
"

Gsky akwai fasaha a book din nan".
.
.

.

*Salbiyya Adam*

"Walh nima naji dadinsa sosae allah yasa muna aiki dasakon dake ciki".
.
.
.
.

*Fatima Umar Zubairu*

"Sosai naji dadin da babu boka ba batan hanya, a cikin book dinta, zallan fasaha kawai da dabara takeyi keep it up thanks".
.
.

*Zahra Bello*

".Ai in a zaman aure akwai fahimta to komi yazo da sauki. Fasa da dibara da hskuri sun ishe Mu zaman aure".
.

.

.

*Aliyu Nana Firdausy*

"pls keep it up princess eshat".

.
.

*Zaharaddeen A Ibraheem*

"Very interested book. May almighty Allah (S.W.T) reward u abandontly".

_ire iren wannan cmmnt ɗin ynamun daɗi_

.
.

.
Chapter 6 · 0% Book details