← Book details Shimfidar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 12

Sashe 4

Shimfidar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani nauyayyen nufashi ummu tayi ta ce "shine kike kuka a gaban shi"?

"ji nake kamar na mutu na huta, wlh asiri ta mishi ummu, bansan yaya zanyi ba".

Ummulkairi ta dube ta cikin nutsuwa ta ce "Anya kina kula da gidan ki a matsayin abu mafi matuk'ar muhimman ci a gareki"?

"sosaima ummu, banida lokacin kowa sai na gidana dana mijina, burina kullum na faranta wa Anwar, kuma kinsan bana wasa da tsafta".

Ummu ta ce "Ba wannan nake nufi ba, ina nufin ya kike sarrafa rayuwar auranki? ya kike sarrafa soyayyar dake tsak'anin ki da mijin ki, abu na farko me muhimman ci shine mijin ki ya samu nutsuwa dake, saboda samun nutsuwar sa shine naki, duk namijin
da bai samu nutsuwa da matar sa ba, a duk yadda yakai da sonki sai an samu matsala babba da rashin kwanciyar hankali, nutsuwa shine ki kyautata shimfid'ar sa ako yaushe ya kwanta dake ya samu wannan jin dad'in wanda shi zai bashi dukkan wata nutsuwa da kwanciyar hankali, lokuta da dama mu muke cutar da kanmu kuma muzo mufara kuka an asirce mana miji, shikenan mu fad'a neman taimako daga k'arshe mu fad'a hanun bokaye, bawai asirin ne bazata iya miki ba amma nafi so ki gyara abunda kika gaza idan babu canji sai mu koma yi masa addu'a kawai".

Maryam ta cire tagumin da tayi ta ce "na fahimce ki, shi yasa bana b'oye miki matsala ta ummu, sai dai ta yaya zanyi naga ya samu nutsuwar nan, nifa ban tab'a hana mishi kaina ba ko bana so nakan kwanta yayi abunda yaga dama dani".

🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏
*SHIMFID'AR MIJINA*
🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
PML
_We dont just entertain and educate we also touch the hearts of the readers_
.
Writen By Princess Eshat Aysm
.
.
Page 8
.

_K'irk'irarren labarine banyi don cin zarafin wani ko wata ba_

.
.
.
.
.
.
.
.

Ummu sai da tayi dariya tace "shi namiji sarrafa shi akeyi kamar yadda yake ɗan miki wassannin nan yana motso sha'awar ki to kema haka zaki mishi, yakasan ce kina cin kayan itatuwa da ganyayyaki, kina yawan cin abinci me ɗan romo2, kidaina amfani da ruwan sanyi ta ko yaya, mace ba'aso tasha ruwan sanyi balle tsarki dashi, kizama kullum kina cikin ɗumi, ki yawaita shiga ruwan gabaruwa da kika dafa da garin lalle da magarya....

Shawarwari tayi ta bata harda irin shigar da zata rik'a yi idan ranar girkin ta yazo, d
sai a lokacin Maryam ta gane Babban sakacin da tayi, sai kiga kina ladabi iya ladabi wa mijinki, kina tsafta kin iya girki, kina kula dashi amma sam baya tausayin ki baya kula dake yanda ya kamata to wannan shine matsala mafi girma a gareki, wasu kuma sun sani amma sakaci da baiwa karatun novels muhimmanci yasa basu taɓuka komai.....
.
.

Saida sukayi sallahr azahar Maryam tana shirin tashi ta nemo musu abunda zasu ci, Fateema ta shigo,
cikin dogon hijabin ta kamar kullum nan kuwa kayan jikin ta tamkar da tsirara ne, Har k'asa ta tsuguna ta gaida Ummu sannan ta dubi Maryam ta ce "Aunty abinci is ready".
murmushi maryam r
tayi tace "ok sannu da aiki".
Mik'ewa tayi tabar ɗakin, Ummu tace "gaskiya kinsamu kishiya yaran yanzu ai sai sufara ɗaga maka kai, kinga ni wallahi tsoron kishiya nakeyi shi yasa bana wasa da *SHIMFID'AR MIJINA*
.
.

.

Sai dare Ummu tabar gidan, Anwar sai mamaki yakeyi ganin yanda Maryam take ta jan Fateema ajiki, ko kaɗan babu alamar ɓacin rai a fuskan ta kamar ba itace tayi ta narkan kuka ba, yadai zuba mata ido kawai yana mamaki, koda dare tayi fateema bata barshi ya shiga ɗakinta ba tasa key, itama Maryam kwanciyar ta tayi zuciyar ta fal da tunanin ta ina zata fara, tana jin shi yashigo tayi kamar tana bacci, wanka yashiga ya gama shirin kwanciya duk tana ganin shi har ya gama yazo ya kwanta a bayan ta, tsoron ta ɗaya kada ya nemi kusantar ta don tasha alwashi sai tagyara komai datayi loosing.
Shi kuwa so yake ya tambaye ta me yasa ta mari Fateema, kuma bayya son tashin ta a bacci, kamar tasan tunanin da yakeyi ta ce "kayi hak'uri da abunda nayi ɗazu".
sosai mamaki ya kamashi ya ce "Dama likimo kikayi? ni kaina kin bani mamaki saboda ganin mace me hankali nake miki ashe.... Juyowa ta tana fuskantar shi, hakan yasa yayi shiru yafara susa kai daya tuna shima ya ɗaga hanu zai mare ta, "sharrin shaiɗanne da zuciya da kuma sharrinka".
ta faɗa tana kallon shi, zaro ido yayi, ta ce "sharrin ka ma yafi yawa, tunda kayi aure ka canza kana wani ɓare2, ina kai zuciya ta nesa, abun yazama kadawo ɗakina ma bazaka barta ba, shiyasa nayi tunanin Bata barka hakaba".
Sosai yagane kuskuren sa, ya janyo ta jikinsa ya ce "kiyi hak'uri maryam, wlh tsintar kaina nake da hakan amma zan kiyaye ki yafemun".
wasanni ya fara mata ta hankaɗa shi ta koma nesa dashi ta ce "kayi bacci kawai".
sororo yayi yana kallon ta ta shige bargo ta barshi, ya lumshe ido yana tuno daɗin da yake sha a wajen Fateema, da haka shima bacci ya kwashe shi, zaman gidan ya gyaru sosai Maryam bata fushi saboda tasan matsalar ta, komai zata gani takan danne zuciyar ta, kuma duk nacin Anwar bata bari ya kusan ceta ranar girkin ta, abun yana taɓa masa zuciya yafara tunanin kodai ta fara k'yamar sa ne,

Tun yana share ta har yafara faɗa amma ko ajikin ta, ta dage da shan duk abun da ya kamata ta daina tsarki da ruwan sanyi, kullum da yamma kuwa sai ta tsiyayi miski da man tafarnuwa tayi matsi dashi, Ummu ta aiko mata abubuwa da dama kuma tana amfani dasu, ita kanta tanajin canji a jikin ta, wani lokacin taji sha'awa ta kamata amma sai ta daure, ita dai nufin ta tana so taji ta matse sosai sannan ta ciko tayi ruwa tayi ɗumi ta zamo cikakkiyar mace me iko.

.

.
.

Matsalar Anwar yanzu ɗaya shine haihuwa, abun ya fara damunshi yana so yaga jininsa, duk inda yaje yaga yara sai hankalin shi ya tashi,
Mahaifiyar shi kullum k'orafi a kan Maryam tak'i haihuwa aure shekara biyu (sai kace ita ke bayarwa kanta).

.
.
.
.

🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏
*SHIMFID'AR MIJINA*
🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏
.
.
.

*CLASSIC WRITERS ASSOCIATION*
C.W.A
.

*REALLY MISS YOU PURE MOMENT*
_ALLAH YASA HAKAN SHI YAFI ALKAIRI_

.
.

Writen By Princess Eshat Aysm

.
.

Page 9
.

_K'irk'irarren labarine banyi don cin zarafin wani ko wata ba_

.
.
.

.

.

Tana son Maryam sosai amma akan haihuwar nan duk tabi ta takura mishi akan a duba ta wai ko bata da k'wan haihuwa ne, shi dai bai taɓa nuna wa Maryam abunda yake faruwa ba, shi fatan sa Fateema ta samu ciki tunda Maryam har yanzu shiru.

.

.

Maryam ne da Fateema zaune suna kallo suna taɓa hira jefi2, Fateema tace "Baki zuwa ko inane, ban taɓa ganin kin fitaba".
"ina zanje Fateema, kiwane yake hanani futa".
Fateema ta ce "ko kasuwa baki zuwa, wlh ni nagaji da zama waje ɗaya, don Allah ki tambaya mana muje akwai abun da nake so na saya".
Shiru Fateema tayi kafin tace "duk abunda zaki saya kibaiwa Anwar zai siya miki".
Dariya ne ya kama Fateema ta ce "Akwai abunda zaka siya wanda bazaka so yasani ba".
Maryam tayi jum tana wani nazari can tace "Dama akwai gidan da nake son zuwa, idan munje sai a kaiki kasuwan".
Cikin murna Fateema ta ce "yauwa aunty".
Shiru sukayi na tsawon lokaci can Fateema tasake jefo mata wata tambayar "Aunty Yaushe zamuje gaishe da mahaifiyar Anwar, tunda nazo banga wani nasa yazoba".
Maryam k'osawa tayi da tambayar ta mik'e tace "idan mun futa sai mubiya can, bacci nakeji zan shiga ciki".
Kai kawai Fateema ta ɗaga mata taci gaba da kallon ta.
Ba'a jumaba Anwar ya dawo, da hanzari ta mik'e ta taroshi tana masa sannu da zuwa, hancin ta yaja yace "ina Maryam yau nagan ki ke kaɗa"?
Ta ɗanyi far da ido ta ce "yanzu ta shiga ciki".
yayi murmushi yace "bari na dubata".
Binshi tayi da kallo har ya wuce, taja dogon mumfashi ta zauna.

.
.

A zaune ya sameta tana waya da Ummu, tana ganin shi ta mata sallama ta ajiye wayar, pick ƴya mata a goshi yace "yunwa nakeji".
"Bakaso gaskiya ba, nasan ,Fateema tana kusa kaje ta zuba maka".
Shiru yayi naɗan lokaci kafin ya ce "Maryam meyasa kika canza ne, na lura kamar baki son ganina, idan wani abun nake miki kifaɗamun".
Ta juya kai ta ce "Har kana tunanin wani abu kamun? Matar sadaka fa ka auro, mezaisa kamun wani abun da zai ɓata mun rai".
Sake baki yayi yana kallon ta yakasa magana, ita kuwa ci gaba tayi da cewa "Lokaci yayi da zaka daina hanani futa, ko gidan ku baka kaini balle nayi zumunci da 'en uwana da k'awayena, idan Allah ya kaimu gobe zan kai Fateema ta gaishe su".
murmushi yayi ya

kamo hanun ta ya ce "har yanzu banji laifina ba, idan kin faɗamun sai nabarki kije".
Ta kalle shi ta ce "nifa ban san canzawar danayi ba".
k'ok'arin kai bakin shi cikin nata yafara yi, tayi saurin rufe bakin ta fara ture shi, yasa hanun shi cikin rigar ta, tayi saurin tashi zata gudu, ya ce "kinga abun da kike mun".
Dariya ta mishi ta ce "wannan basai kamun laifiba, nabarka ka huta ne, kaji da matar sadakar taka".

Kamo ta yazoyi ta matsa da sauri, yace "Ni nafaɗa miki matar sadaka"?
irin borin kunyar nan, tasakar mishi harara ta ce "waye ya faɗa".
Ya kaɗa kai ya ce "ni yunwa nakeji".
Yasa kai ya futa, washe gari da wuri suka gama komai suka shirya, shi yaɗauke su yafara sauk'esu a gidan su Maryam, tun kafin suk'arasa shiga tafara k'wala wa maman ta k'ira
Ko ba'a faɗa ba tasan Maryam ne, zanga ranar da Maryam zata girma, ta faɗa aranta.
Chapter 4 · 0% Book details