← Book details Shimfidar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 12

Sashe 3

Shimfidar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To amma bazan iya futa ba kad'auko mun sai
muci anan".
tsintar kanshi yayi da cemata "to".

yana barin d'akin tayi sauri ta saka key ta koma ta kwanta, wayar ta ne ya fara ruri ta tashi ta d'auko, ganin Sakina yasa ta saki dariya ta d'auka.

"Amarya Amarya".

"ke ina wani amarya nasha azaba, wlh dak'yar nake tafiya".

Sakina ta kwashe da dariya ta ce "Kice kin more, kinga yanzu ne ma yakamata ki kula da kanki kada kwana biyu aji kin buga, ki tashi yanzu ki da'au gyanyen magaryan nan ki dafa ki shiga ciki, 30mnt ki fito ki goga man zaitun zakiji kin warware, idan kin gama ki k'irani".

"to k'awata".

kettle ta kunna cikin hanzari ta dafa ta juye a baf, yana d'an hucewa ta shiga ciki harda 'yar k'ararta daga baya kuma tafarajin dad'i yana shigar ta.
.
.

Azaune ya sameta ta rafka tagumi.

"kinsan Allah yarinyar nan bata tashi ba".
binshi tayi da kallo kafin tace "shine ka shanyani kaje kayi zamanka"?

ya lakuce mata hanci ya ce "fanfon toilet d'in tane naji ruwa yanata zuba ashe b'aci yayi da k'yar nasamu na gyara".

Ta sauk'e ajiyan zuciya, ta fara zubawa yace

"ki zuba naki yanzu banajin yunwa sai anjuma zanci".

mamaki ya kamata, ta fara ganin canji har acikin k'wayar idon shi, ta basar ta zuba nata taci ta k'oshi ta wuce d'aki ta barshi, mamakin ta ya k'aru ganin bai biyota ba, ta lek'o shi taga waya yakeyi don haka ta masa uzuri.

🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏
*SHIMFID'AR MIJINA*
🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
PML
_We dont just entertain and educate we also touch the hearts of the readers_
.
Writen By Princess Eshat Aysm
.
.
Page 6
.

_K'irk'irarren labarine banyi don cin zarafin wani ko wata ba_

.
.
.

*Nayi mstk naturo page 5 a matsayin 4, yanzu page 6 zan tashi*

.
.
.

.

ya dad'e yana zaune a wajen duk hankalin shi yana kan Fateema, yana so yakai mata abincin kuma baya so Maryam ta d'ago shi.
saida ya shafe awa d'aya kafin ya d'au abincin yayi d'akin Fateema, tana ganin shi ta taso da sauri ta rungumo shi tana dariya, bayan sunci ta d'au dogon hijabin ta tanufi d'akin maryam, a kwance ta tarar da ita da alama tayi zurfi a tunani.
Ta zauna daga d'an nesa da ita ta ce "Aunty ina kwana".
sai a lokacin tasan da shigowar ta, ta amsa fuska a sake ta ce "kinci abincin kuwa"?
"Aunty naci, ba wani aikin da zan miki ne"?
Maryam tayi dariya ta ce "Babu".
shiru sukayi na tsawon mintina kafin Fateema ta ce "zanje na kwanta".
Maryam murmushi kawai tayi ta bita da kallo harta b'ace, ta sauk'e ajiyan zuciya ta koma tayi kwanciyar ta.
.
.
.
Haka zaman nasu yayita tafiya, tare suke aiki Fateema tana girmama ta sosai amma Anwar ya canza mata kwata2, yanzu k'iri2 yake wasu abun wa fateema a gaban ta idan ta gudu d'aki yabita bazata sake ganinshi ba har sai gari ya waye, ranar da yadawo
D'akinta kuwa ko kallo bata isheshi ba, motsi kad'an yace bari na duba Fateema, ganin abun nashi ya fara yawa yazo zai sake futa ta taroshi da sauri, "Anwar meyasa ka canzamun, me kake zuwa yi d'akin fateema a darennan, kai kacemun ba don ka wulak'an tani zakayi aure ba yanzu menene sunan abunda kakeyi"?
Tak'arasa kamar zatayi kuka.
"yanzu idan banda fitina me nake miki, zuwa nake naga ko tayi bacci, wani lokacin bata bacci da wuri".
murmushi tayi ta koma ta kwanta, zuciyar ta kamar zata fashe don bak'in ciki, ahankali ta fara salati aran ta.
jikinshi ne yad'an yi sanyi ya koma kusa da ita ya kwanta, ya jata jikin sa ya ce "kiyi hak'uri".
Hanun ta tasaka a bakin shi ta ce "bakamun komai ba".
Tausayin ta ya kamashi, shi kanshi baisan yana mata wani abun ba.
D'an wasannin daya saba mata yayi bawai yanajin dad'in abun ba, lokacin da ya kusance ta ji yayi kamar ya kurma ihu, (babu magi babu gishiri balle su kananfari da masoro hhhhh lolx).
.
Da wuri ya koma falo yana sallar asuba ya gwammace ya kunna Tv,

bai tab'a sanin kyawun mace ba'a fuska yake ba sai yanzu, shi yanzu ko muryar Fateema yaji yakanji sanyi a ranshi, yana jin yafi sonta fiye da kowacce mace, ashe sha'awa yakan zama so...
Motsi yaji a bayan shi yasashi juya wa, fateema ya gani sanye da kayan baccin ta, tashin ta kenan tayi sallah ta fito, ganin Maryam da wuri take aikin gidan yasa itama ta fito taga oga yau yana d'akin ta, kallon mamaki ta mishi ta ce "meya fito dakai a yanzu"?
Ya mik'a mata hanu alamar taje, ba musu ta k'arasa kusa dashi, wani mayen kallo ya bita dashi yana had'iye yawu, hanun nata ya rik'o ya d'aura a bakin shi, ya saka yatsan ta d'aya aciki yana tsotsa, itadai batayi yunk'urin hanashi ba har ya gaji ya sake hanun ya d'aura ta a cinyar sa yana shak'an k'amshin ta.
"Ina Auntyn na ganka anan"?

.

a kasalance yace "tana bacci".
zamewa tayi ajikin sa ta ce "zanyi aiki, ka koma ɗaki".
Sauk'owa yayi shima yace "tare zamuyi".
Itadai duk mamaki ya hanata magana, gashi tana tsoron maryam tafito tagansu tare tasan ranta bazai mata daɗi ba, gashi bata son tashin hankali ko kaɗan ba'a koya mata ba, tare sukayi aikin sai mammane mata yakeyi.

.

maryam data tashi bata ganshi ba da sauri ta nufo falon taga ko ɗakinsa ya koma, tsorone ya kamata ƙlokacin datayi arba dasu, kukane ya kufce mata ta koma ɗaki da gudu ta faɗa gado ta saki wani kuka me tsuma zuciya.
"me nayi wa Anwar?
Haka maza sukeyi idan sun k'ara aure?
ko kuma asiri ta mishi daga shigiwar shi? Na shiga uku"!

Kuka takeyi sosai tanaso tasan amsar tambayar ta.
.
.

.

To readers wazai amsa mata😀

🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏
*SHIMFID'AR MIJINA*
🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
PML
_We dont just entertain and educate we also touch the hearts of the readers_
.
Writen By Princess Eshat Aysm
.
.
Page 7
.

_K'irk'irarren labarine banyi don cin zarafin wani ko wata ba_

.
.
.

*BARKA DA SALLAH GA DUKKANIN D'AUKACIN MUSULMAI TA DUNIYA BAKI D'AYA*

.
.

_JINJINA GA TASHAN FARIN WATA SHA KALLO HAJIYA AISHA INA GODIYA DA IRIN ADDUAN A KIKAMUN KEMA ALLAH YABAKI IKON BUD'E TAKI TASHAR MUSHA KALLO_
.
.

*NIFA BURINA KU GANE SAK'ON DANAKE SO NA ISAR, DUK WACCE BATA GYARABA TA TSAYA LALACI KO KUNYA YA HANATA GYARA SHIMFID'AR TA, NIKUWA NA AURE MIJINTA🤣🤣🤣🤣*

.

..

..

.
.
.
.
.

Amsa d'aya tabaiwa kanta lokacin data gama kukan ta, watau asiri ta masa, take taji ta tsani Fateema tace shegiya ga ladabin k'arya, (matsalar mu kenan abu ba abuba ace asiri bazakiyi tunanin menene matsalar ki ba, to nidai ku gyara ycn).

.
.

Anwar Kam hankalin shi kwance sukayi aikin su da fateema, dak'yar ta hanashi shiga d'akin ta, shi kanshi bai san dalilin dayasa yake manne mata ba.

k'arfe 9am suka hallara wajen brkfst, fuskar maryam a d'aure kamar zata fashe, dak'yar ta amsa gaisuwan da Fateema take mata, ita kuwa fateema jikin ta ne yayi sanyi ta kasa cin abincin, Anwar yana lura da ita ta kasa cin komai, ya kalle ta ya ce "me yake damunki"?

ta ce "babu komai".

amma kamar zatayi kuka, nanfa ya rud'e, ya matsa da abincin dayake ci ya ce "babu komai a wannan fuskar"?

Ta mik'e zata bar wajen yayi saurin janyo ta, ta fad'o jikin sa, Maryam fashewa ne kawai batayi ba, da k'yar ta mik'e ta fizgo fateema ta sharara mata mari har 2, cikin zafi Anwar ya d'aga hanu zai kai mata marin itama wayarshi tayi
ruri, ya d'aga yaga BILAL ne sannan ya kara a kunne, "Matata na kawo taga amarya kuma naga kaman baku tashi ba".

"Ganinan zuwa". ya fad'a kai tsaye, yayi k'wafa yaja Fateema yakai ta d'akin ta yana bata hak'uri. (ko bkm tasha mari, hahahaha).
.

.

Awajen da yabar maryam a wajen ya tarar da ita sai rusan kuka takeyi, ko ta kanta baibi ba, wani haushin ta yaji yanayi ta dakar mishi mata.
.

BILAL yana ganin shi ya kwashe da dariya ya ce "mijin mace 2".
harara ya watsa mishi ya ce "kafara ko? nafi mijin hajiya tunda nasamu daman k'arawa".

Bilal zaiyi magana ya d'aga masa hanu ya ce "Bari na shigar da ita kafin kafara".

Dariya sukayi kafin yayi gaba Ummulkhairi tabi shi a baya.
.

Still tana wajen bata daina kukan ba, kallo d'aya ya mata ya ce "Ga Maman Fahat".
D'akin Fateema ya nufa, a kwance ya sameta tana waya kamar ba ita ke kuka d'azu saboda zafin mari ba, ya rufa a bayan ta yayi mata rumfa, zare wayar tayi ta kashe tana ajiyan zuciya, "kiyi hak'uri". ya rad'a mata a kunne, "Hak'uri kuma"?
ta tambaya.
"eh". yafad'a yana shafa kanta.
ta ce "Nice nayi laifi, matsalan bata fad'amun laifina ba, kai kuma baka kyauta ba, yakamata ka tambaye ta ko akwai laifin danayi...
hanu yasa ya rufe bakin ta.
.

.

Ummulkairi mamaki ya hanata zama tabi Maryam da kallo, da k'yar tayi shiru saboda abun ya k'ona mata rai sosai, dak'yar ta bud'e baki tana murmushi ta ce "sannu da zuwa momyn Fahat".
"Bazan amsaba Maryam, da girman ki kizauna kina ta kuka"?
"kamawa tayi wlh nima bansan zanyi ba, muje ciki dama inason ganin ki".

.

Ba inda batayi da ita taci abinci ba tak'i, dole ta hak'ura ta d'au fahat ta fara masa wasa, ummulkairi duk tabi ta damu musamman irin kallon dataga Anwar ya mata ta tabbatar ba
lafiya suke ba, gyara zama tayi ta dubeta tace "maryam me yasame ki kike kuka"?
Ta ajiye fahat ta saita nutsuwar ta tace "Ina cikin matsala ummu, kwanan Anwar 8 kenan da aure amma gaba d'aya ya canza mun, abun yakai jiya yadawo d'akina amma wlh gaba d'aya hankalin shi yana can, asuban fari yabar d'akina duk tunani na d'akin shi ya nufa ashe suna nan tare a falonnan".
Chapter 3 · 0% Book details