Sashe 5
Shimfidar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har suka k'araso falon bata daina k'iraba, Ganin Mamy kwance acikin kujera yasa ta zunɓuro baki tace "yanzu mamy kina jina kika share ni? shiyasa bana ɗaukin zuwa gidannan idan Dady bayanan".
Tun tasowar ta mahaifiyar ta bata wani jata ajiki ba shiyasa takenan a sangarce batasan komai ba, Fateema ta tsuguna cikin ladabi ta gaida Mami, cikin sakin fuska ta amsa ta ce "itace k'anwar taki"?
Maryam tace "itace mami".
Mami ta kalli Fateema a fakaice ta ce "eyya sannu da zuwa, ban samu zuwa na duba ku ba, ina fata kuna lafiya"?
Fateema ta sunkuyar da kai ta ce "lapiya law".
Ta dubi Maryam ta ce "kin tsaya k'erere, kishiga ki nema muku abunda zakuci".
"a'a mami ba zama zamuyi ba, zan kaita wajen Hajiyar Anwar daganan zata wuce kasuwa ni kuma...
Katseta tayi tace "ki kaita kidawo yanzu ina son ganin ki, tun jiya nake neman numban Anwar akan yakawo mun ke amma bansamu ba".
Maryam ɓoye mamakin ta tayi ta ce "Fateema muje ko".
Turaren wuta mami ta ɗauko wa Fateema ta ce "kiyi hakuri da wannan ban san da zuwan ku ba".
cikin farinciki Fateema ta amsa tana godiya.
.
Mahaifiyar Anwar ta tare su da murna, cikin k'ank'anin lokaci aka cika musu wajen da kayan ciye2, a nutse suka gaishe ta, ta amsa faram faram da alama ta lura suna zaman lafiya, lokaci guda ta ɗaure fuska, Ita dai Maryam batama luraba, hankalkn ta yana wajen tunanin me Mami zata faɗa mata har take nemanta, a iya sanin ta bata taɓa wani magana da ita me muhimman ci ba, a ɗarare ta ce "zulaihat tananan kuwa"?
Hajiya Jamila ta yamutsa fuska kafin ta ce "wani abun zata miki"?
"a'a dama zata raka Fateema kasuwa ne".
Daɗa ɓata rai Hajiya tayi ta ce "daɗin haihuwa kenan, ace mutum shekaru biyu ko ɓatan wata babu, itama amaryan banga alamar motsi a tare da itaba".
Wani mummunan faɗuwar gaba ne ya dira wa Maryam, ita harga Allah ta manta da wani zancen haihuwa tunda ko a fuska Anwar bai taɓa nuna mataba, to waima shekaru biyu kawai har anfara mata gori, ɗan tsaki taja aranta, mik'ewa tayi kamar bataji abun da ta faɗa ba, "Zanje wajen Mami, idan an samu yaro ya rakata".
Hajiya tayi shek'ek'e tana kallon halin ko inkula da Maryam tayi wa maganar ta, Fateema kam kamar ta rusa ihu haka takeji, da sauri Maryam ta futa har tana tuntuɓe.
Hajiya Jamila tayi k'wafa, ta dubi Fateema ta ce "Babu abunda ta iya sai shan k'wayoyin hana haihuwa, ni nasan Anwar bai saniba amma da tuntuni ya ɗauki mataki".
Fateema ta kaɗu sosai, a ranta tace me yasa Aunty zatayi haka alhalin mijin ta nason haihuwar nan, Hajiya ta katse mata tunani da cewa bakiga ina fara maganar ta kauda kai ba, to nidai Allah yagani inason naga jikana, abu ɗaya zakimun ki temake ni kuma ki temaki mijin ki, zan bada kuɗi yanzu a siyomun k'wayar, kisaka a ɗakin ta inda kika tabbatar zai gani, idan yagani nasan zai ɗau mataki kuma zata daina sha".
Zaro ido Fateema tayi tana kallon hajiya, kafin ta fara girgiza kai alamar bazata iya ba.
Hajiya Jamila ta daka mata tsawa ta ce "kina so na mutu banga ɗan Anwar bane, ƙkada kicemun ke zaki haifamun, ni dukkan ku nake so ku haihu, ina so ku cikamun gidan da jikoki, don Allah kiyi abunda nace, zanbaki so da k'auna irin wanda mahaifiyar ki take miki".
Fateema hawaye take bata san dalilin suba tace na amince zanyi, cikin farinciki Hajiya ta ce ko kefa, idan banda abunki wake son kishiya haka, ki kwantar da hankalin ki kinji 'yata".
🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏
*SHIMFID'AR MIJINA*
🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏
.
.
.
*CLASSIC WRITERS ASSOCIATION*
.
.
.
Writen By Princess Eshat Aysm
.
.
Page 10
.
wlh banason rainin hankali kamar wani kuɗi kike biyana zaki dameni da wani magana, @ummu labil kiyi damuwarki nayi tawa thatz y bana shiga damuwar mutane.
..
.
_K'irk'irarren labarine banyi don cin zarafin wani ko wata ba_
.
.
.
.
.
Cikin ruɗani ta shiga gida, zuciyar ta duk a jagule, Mami tana ganin ta tazauna, ta ce "har kin kaita"?
ta ce "nakaita mamy, na matsu naji dalilin da yasa kike nema na".
Mamy ta mik'e tace "muje ki gani, aikane auntyn ki ta kawo a baki, tana sauri shiyasa bata k'arasa wajenki ba".
B'ata rai Maryam tayi kafin ta ce "ni nasan dama bazaki nemeni don kanki ba".
"uwar me zanmiki to, kizo ki karɓa idan zaki zo".
Zunɓura baki tayi tabi bayan ta tana tunanin halin Mamy.
Wani k'aton robane me murfi da aka cikashi da *MAD'I*
wanda aka haɗa shi da
*Cukwai*
*ɗanbashanana*
*Gallo*
*Tsintsiyar maza*
*Geron mata*
*Ganyen taga rana*
*Farin gari*
*Ganyen runhu*
*citta da sauransu*
Duk abubuwane da suke k'arawa mace lafiya, ni'ima, inhar kina shan wannan haɗin kinyi bankwana da shiga cikin k'unci a gidan mijin ki, wlh ko yawon banza yake zai daina, haɗashi akeyi kamar tunkuza, anasha da madara, abubuwa dai da yawa ta kawo mata, idan natsaya lissafawa zamu juma, haɗaɗen humra da turaren wuta kuwa ba'a magana, daɗi kamar ya kashe Maryam ta ce "Mamy meyasa ke baki nema mun irin wannan"?
wani kallo ta mata kafin ta ce "kefa yanzu na lura baki da kunya".
murmushi Mayam tayi ta ce "Gashi ai kinsa anmun kishiya".
Mamy ta kama baki ta ce "su mazan yanzu ai kome kikayi sai sunyi auren su".
"a'a Mamy ni banyadda ba".
ta faɗa tana tattara kayan.
.
.
Kusan wuni Fateema tayi a gidan su Anwar, Hajiya rabin maganar ta akan ta aikata abunda tasaka tane, jikin Fateema duk yayi sanyi kasuwar ma fasa zuwa tayi, Daf magriba Anwar yazo ɗaukan su, koda suka biya ɗauko Maryam basu same ta ba tana gidan Ummu, murmushi kawai Bilal yayi yaɗau hanyar gidan.
.
.
Tunda suka koma Fateema ta rasa me yake mata daɗi, ita bataga wani mummunan hali ga Maryam ba balle ta saka mata da wannan ɗanyen aikin, yanda ta fahimci Hajiya Jamila kuwa zata iya komai idan bata aikata wannan aikin ba, sak'a da warwara tayi ta yi har gari ya waye.
Bayan sun kammala komai sun sallami Anwar ya tafi aiki, suka zauna a falo kamar yadda suka saba, Fateema ta ce "Aunty inaso zamuyi wata magana dake".
Juyowa Maryam tayi tana kallon ta tace "menene maganar".
Fateema ta rasa ta ina zata fara, ta daure tace "Naji Hajiyar Anwar tana miki gorin Haihuwa, kuma naga kaman maganar bata ɓata miki rai ba".
Maryam ta nisa ta ce "wlh maganar ta taɓani, sharewa nayi banga amfanin saka damuwata akai bane, aure shekaru biyu kawai har anfara mita, ni namanta da wani maganar haihuwa kuma bazan saka a raina ba har sai Allah ya bani, duk faɗin gidanmu ni kaɗai aka haifa, lokacin har an fidda tsammani sannan Allah ya kawo, tunda Allah bai kawo nawa ba ina miki fatan Allah yabaki kada kema a fara hantarar ki".
Jikin Fateema ya daɗa sanyi ta ce "mezai hana muje asibiti ko....
hanu Maryam ta ɗaga mata kafin ta ce "Banyadda likita yana gane mace ko namiji sunada ƙlalurar hana haihuwa ba, sai kiji sunce bazaka haihu ba kuma ka haifa, ki kwantar da hankalin ki akwai lokacin da idan yakai ban haihu ba zan damu, amma yanzu da sauran lokaci".
Fateema ta zuba mata ido na tsawan lokaci "Aunty mahaifiyar Anwar kuwa tana sonki"?
kamar Maryam bazatayi magana ba saboda bata fiye son magana ba, indai zasu zasu zauna da Fateema ta rink'a tsare ta da tambayo yi kenan "Tana sona amma bansan ko ta canza ra'ayi ganin ɗanta yayi aure ba".
"To ni gaskiya Aunty zan faɗa miki bata sonki, kuma bari ki gani".
Ta mik'e ta nufi ɗaki.
Maryam ta sake baki tabita da kallo, har ta dawo idon ta yana wajen, maganin da Hajiya Jamila ta bata, shi ta ɗauko ta mik'a mata.
Cikin rashin fahimta Maryam ta ce "mezanyi da maganin hana ɗaukan ciki kuma".
Saida Fateema ta gyara zama tace "cewa akayi nasaka aɗakin ki saboda mijinki ya gani ya ɗau mataki akanki, ni kuma bazan iyaba saboda baki ɗaukeni a matsayin kishiya ba kullum a k'anwa kike ɗaukata".
Maryam ta k'walolo ido waje gami da dafe k'irji, lokaci guda kuma ta fashe da kuka, ta ce "Na shiga uku, ina zansa kaina, waye? Hajiya ko"?
Fateema ta matsa kusa da ita tace baki shiga uku ba Aunty, kuka ba naki bane, musan yanda zamuyi mukashe wannan wutar, idan ta gane banyi ba nima zan samu matsala, yanzu menene abunyi"?
Maryam ta rungume ta tace "wlh ban ɗauka ana samun kishiya hakaba, bansan dame zan saka miki ba, amma nasan abunyi, zansa wannan maganin dakaina inda Anwar zai gani...
Da sauri Fateema ta katseta, "a'a aunty, idan yazo da tsautsayi ya sake ki fa? nidai ba haka za'ayiba.
🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏
*SHIMFID'AR MIJINA*
🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏🛏
.
.
.
.
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
P.M.L
.
.
Writen By Princess Eshat Aysm
.
.
Page 11

Anwar tun shigowar sa ya lab'e yana sauraron su, jikin shi har b'ari yakeyi, zufa kuwa ya gama yi masa wanka, "Hajiya meyasa zakiyi haka? abunda yaketa nanatawa kenan, shahada yayi yashiga, a zabure suka mik'e suna kallon shi, hanu ya mik'a wa Maryam alamar ta bashi abun da yake hanunta, hanun ta na b'ari ta mik'a mishi, baice musu komai ba yawuce ta gefensu ya wuce, da sauri Fateema ta matso tana zare ido ta ce "kaddai yaji abunda nake fad'a, na banu yanzu zaije ya fad'awa Hajiya".
Maryam ta murmusa ta ce "kinga ni naji dad'in haka, kuma wannan abunda kika yi yasa kin k'ara k'ima da daraja a ido na, a farko na d'auka zaki ruguza rayuwata da mijina amma sai ya zamana kece kika gyaramun shimfid'ar mijina".
Ta kamo hanun Fateema ta ci gaba da cewa "kin zama 'yar uwata fateema, nagode da yanzu anhad'a ni da mijina".
ta fashe da kuka,
Fateema ta ce "Aunty kibar kuka don Allah, kije yana jiran ki".
Maryam ta harare ta da wasa ta ce "yau kuma bazaki je ki masa sannu bane"?