← Book details Shaawar Ta Nikeyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 15

Sashe 4

Shaawar Ta Nikeyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kiran sallar azahar ne ya tayar da ita bayan tayi Sallah ta had'a tea ta sha kana ta sauya kaya riga latvia ce ta saka iya guywa ta kwanta a jikinta hips d'inta da nononta sun fito chassss tayi parking din sumar kanta tsakiyar kai ta saki jelar gashin ta sauka har gadon bayanta, ta shafa read d'in jan baki ta saka bak'in gilashi sai baza k'amshi takeyi wasu takalmi ta saka masu masifar tsini ta fito saiga Anam d'auke da pilet d'in abinci tace "Ayma ga abinci na dafa mana." Ayma tace ki aje min fita zanyi." Aman tace"Okey a dawo lafiya. " Rufe d'akin tayi kana ta fita

tinda ta fito mutanen layin ke kallonta suna lasar baki wasu na hadiyar yawu, tana kule da mutanen da suka zuba mata na mujiya, ai kuwa da gangan take baza musu d'uwawu, kamar suci babu har ta kai bakin titi ta samu napep, yace "Hajiya ina zuwa." Tace kaini gurin cin abinci na manyan masu kud'i." Yace "Bakida matsala Hajiya." Suka kama hanya Wani babban gurin cin abinci ne daya amsa sunansa ya sauketa kana ta zare dubu biyu ta bashi sai Godiya yakeyi."
Ita kuwa cikin takon isa ta shiga cikin Wurin sai data duba teburin da ba kowa taje ta zauna ta saka akawo mata Cake da juice sai ruwa, fitowa tayi da wayar Ayman ta kunna data tana kallo sai Wani murmushi takeyi, tana nan zaune taje anyi mata sallama, Wani Alhaji tin shigowarta yake kallonta hat ta zauna kasa jurewa ya yi dole ya biyota,

bazai iya hak'uri Wannan zazzafar ta wucesa ba amsa sallamar tayi batare data juyo ta kallesa ba yace "Kyakkyawa zan iya zama.?" Wani fari tayi mai da lolo eyes d'inta masu kama da me jin bacci tace "Zaka iya." Zama ya yi yace "Barka ya kike.?" "Alhamdulillahi." Kawai ta fad'a shiru ya yi saboda ya rasa ta ina zai cigaba da yi mata magana,

saboda kule kule y'an mata ba halinsa bane dolece ta sa haka, yana wannnan tinani ne yaje tace "Sai anjima." Zata bar gurin da sauri yabi bayanta yace muje na rakaki ko." Suka fita tare, ganin ta nufi titi yace "Ashe bada Mota kika zo muje na saukeki gida." Ayma tace "Kaji nace ma da Mota nazo ne.?" Yace "A'a haka nayi tunani kiyi hak'uri." Batace komai ba ya bud'e mata gaban motar ta zauna,

kana ya shiga mazaunin Direba, sai da suka d'auke hanya yace "Baby ya sunanki.?" Tace "Ayma." Yace "Wow Nice name Ayma ana nufin princess Gaksiya wannan suna ya dace dake." "Thanks kawai tace murmushi ya yi yadda take jan aji Hakan ya burgesa yace "Ni sunana Alhaji Abubakar Mai dala." Ayma tace"Wow Nice name Abubakar Sadeek."

haka ya yi ta janta da hira kafin yace "Wace unguwa zamuje.?" Ayma tace "Sabon layi." Okey kawai ya fad'a, sai da suka shiga cikin layin ta tsayar dashi gab da gidan Barau tace "A nan zan sauka." Ta fad'a tana k'ok'arin fita Motar yace "Ayma baki bani number ki ba." Tace banda layi fa." Yace "Okey." Ya juya kan Motar tace "Ina zamuje.?" Yace

"Idan munje zaki gani." Wani babban shagon siyar da wayoyi ne suka tsaya ya shiga be jima ba ya fito kana ya shiga Motar kwalin waya ya bata yace ga sim card nan ciki, idan keyi chargin wayar zan kiraki." Godiya tayi mai kana suka kamo hanyar dawowa gida wayarsa ce ta soma ringing dubawa ya yi tare da dafe kansa, yanayin fuskarsa ya sauya,

d'auka ya yi tare da karawa a kunne yace"Ina jinki." Me kiran tace "Kaga Alhaji na gaji da iskancin me aikin nan gaba d'aya yau batazo gashi yunwa nikeji kasan ba abinda na iya fa saboda haka ka biyo min da abinci ina jiranka." Tsaki yaja cike da takaici yace "Wai ke Marwa ko kunya ba kya ji na fad'ar wannan magana to Wallahi bazan siyo ba na gaji ni a haka zan k'are da yawon siyen abinci,

idan bazaki shiga kitchen ki dafa ba sai dai yunwa tasan yadda tayi dake." Marwa tace "Wallahi Allah bazan shiga saboda ni ba kallar shiga kitchen bace kaga ba abinda ban iya ba amma Wallahi bazan shiga kitchen na wahalar da kaina ba saboda ni y'ar hutu ce miye amfanin kud'inka idan ban huta ba.?" Alhaji Abubakar yace "Okey to da kyau." Ya kashe wayar, duk maganar da sukeyi Ayma taji komai,

Kallon Alhaji Abubakar tayi kana tace "Idan ba damuwa zan iya taimaka maka akan wannan matsalar.?" Alhaji Abubakar yace "Ayma taya zaki taimaka min Wallahi ina cikin wani hali Matata k'azama ce ajin K'arshe, ba girki ba kwalliya ba iya mu'amalar aure, sai bak'in kishin tsiya bata shiri d y'an uwana gaba d'aya sun dena zuwa garin nan saboda ita ." Ayma tace "Ai wannan abu mai sauk'i ne inaso gobe da safe kazo ka d'auke ni."

Alhaji Abubakar yace "shikenan na gode." Ya sauketa kana ya juya zuwa gida, Ayma kuwa tana shiga gidan, ta soma kiran Anam amma shiru saboda haka ta bud'e dakinta ta shige, tare da fitowa da wayar, ta sakata charge ta shiga wanka bayan tayi sallar magrib,ta kunna wayar tare da saka sim card,

tana janyo wayar Ayman tayi number Saudat data Ayman ta d'auka tare da wasu numbers ta kashe wayar gaba d'aya ta ta saka cikin jaka buga k'ofar d'akin akayi tace Waye Anam tace "y'ar uwa." Bud'e k'ofar Anam ta shigo d'auka da kwallin wayoyi guda biyu tace "Alhaji Sambo ne ya aiko direba ya kawo miki wayoyin kiyi amfani da wacce kike so." Karb'a tayi tana duba iphone 16 ce da Ridmi tace "Kina da waya.?"

Anam tace Eh ina da ita amma keypad ce." Ridmi ta bata kana tace"Okey rik'e wannan mu gani zuwa nan gaba sai a sauya miki wata sim card ta saka cikin Iphone 16 d'in, ta saka ta charge bayan ta cire. Wacce Alhaji Abubakar ya siya mata iphone 17 pro max ce Anam tace "Wani fa yazo nemanki." K'irjin Ayma ne ya buga tace "Waye.?" Anam tace bansan shi ba amma yace sunansa, Suraj." Ajiyar zuciya Ayma ta sauke kana tace "Okey shikenan, kawo min abinci yunwa nike ji."

Anam ta fita, ta kawo mata abinci jalop d'in shinkafa ce da kifi taci sosai kana ta sha ruwa, nan take baiwa Anam labarin Alhaji Abubakar har wayar da ya siya mata Anam tace "Me zai hana ki auresa.?" Ayma tace "Ina ba lilsafin aure a liltafina sai dai nan gaba, yanzu inada abubuwan masu yawa a gabana,

saboda haka zanyi abinda nike da niya." Anam tace "Ba damuwa Allah ya kyauta." Suka cigaba da hira Anam tayi bak'o ta fita,

Washegari da safe bayan Ayma ta kammala duk abinda takeyi saiga kiran Alhaji Abubakar yana k'ofar, gida tace gata nan fitowa, rufe k'ofar d'akin tayi tare yiwa Anam sallama ta fita Alhaji Abubakar kuwa suman zaune ya yi ashe jiya bega komai ba sanye take da mini siket sai riga iya nononta kawai ta rufe ga sumar kanta daya baje gadon bayanta Wani gefen fuskarta,

jaka ce a hannunta sai wayoyinta tana wata tafiya mai jan hankali, har ta iso gaban Motar ya bud'e mata ta shiga kana yaja suka bar unguwar,

Writer Bey Pinky Darling Mrs Jay ✍️

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHA'AWARTA NIKEYI*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

(Romance and sxy)

🔞❌
Writer Bey
Pinky Darling Mrs Jay ✍️
✨✨✨✨✨✨✨✨

Following this link to join my WhatsApp channel domin samun zafafan liltafaina sabbi da tsofaffi tare abubuwan k'aruwa

https://whatsapp.com/channel/0029ValAwoOInlqYMwE1dK00

BOOK ONE
PAGE 9️⃣⏩🔟
Sai da suka d'auke hanya yace"Barka da safiya Princess.". Wani murmushi tayi mai me kashe zuciya kana tace "yauwa barka ykk.?" "Alhamdulillahi ya fad'a tare da maida hankali kan tuk'i kar ya b'arar dasu kan titi, yace "Ina muka nufa.?" Tace "Gidanka zamuje inaso ka bani masauki a ciki ka gabatar dani wurin Matarka a matsayin wacce zaka aura wannan kawai nike buk'ata ka bar ni da sauran aikin."

k'irjinsa ne ya shiga dukan uku uku Marwa ai sai ta kona gidan saboda kishi tinani yake tayi har suka k'arasa makeken gidansa mai kyau da had'uwa, ya bud'e Mata gaban Motar ta fito tare da b'allo cingam ta saka a baki tana ci, kallonsa tayi kana tace"Muje ko." Gaba ya shiga tana bayansa, yana bud'e k'ofar parlou yaci karo da kwalin lemo da robar ice cream,

tsallake su ya yi kana suka shiga ciki gaba d'aya parlon a hargitse yake ba gyara ga plate d'in da akaci abinci nan zube wasu har kan kujera, da gorinan ruwa, komai a haukace sai Tv dake k'ara shi kad'ai yastine fuska Ayma tayi tana k'arewa parlon kallo ba abinda beji ba na more rayuwa amma kazanta ta bata gidan,

Alhaji Abubakar kuwa yace "Ayma ina zuwa nasan tana ciki bata falka ba." Ayma tace "rabuda ita tafiyar ka kawai saika dawo ina ne d'akin da zan sauka." sama suka haura wani babban parlou ne har yafi na farko had'uwa d'auke yake da 4 bedroom kitchen da sauransu kamar dai parlon k'asa d'aya daga cikin room's din ya yace ta zauna rakasa tayi har zuwa Mota kana ta dawo,

ta shiga gyaran gidan daga sama har k'asa, tayi wanke wanke ta feshen ko ina da turaruka gida, kana tayi wanka ta sauya kaya, wata riga ta saka, kamar ta bacci, me hannu d'aya iya cinya rigar ta tsaya, kana ta fito parlon k'asa ta kunna kid'a, ta shiga kitchen ya soma girki sakwara tayi da miyar ugusi da jalop d'in shinkafa da naman kaji,,

ta had'a zobo da kunun aya, tana jira kayan kan teburin cin abinci saiga Marwa ta sauko cikin kayan bacci tana k'arewa parlon kallo, ga wani mayen k'amshi daya dake hancinta, Ayma kuwa yi tayi kamar bata ganta ba sai kwasar rawa takeyi, Marwa tace "Ke wacece uban waye ya baki damar shigomin cikin gida har kina wannan iskanci.?"

dakatar da rawar tayi tana k'arewa Marwa kallo gata da kyau dai dai ita amma ba tsafta ta koma kucaka ballagazar mace, wacce batasan inda ke mata ciyo ba, Ayma tace "Kega Sakara ni d'in Amaryar Mijinki ce wacce ya auro saboda jin dad'in rayuwarsa, na d'auke mai takaici da bak'in ciki, so ki iya bakinki,
Chapter 4 · 0% Book details