← Book details Sanadin Kenan Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 14

Sashe 8

Sanadin Kenan Part 3 Complete Hausa Novel · about 3 min read

BAYAN SATI BIYU
Ranar da sati biyun nan ta Ma’arouf ta cika Amina ta shirya za ta tafi Shira gaido Baffanninta, don ta tabbata in ta koma aiki ba za ta samu lokaci ba. Ilya ke janta a karamar motarta data siya (Kia Picanto) kasancewar hannun nata bai gama fadawa ba.
Gida-gida ta bi ta gaishe su, kowa sai murnar zuwan Dr. Amina yake yi don an san ba ta zuwa hannu rabbana. Balle yanzu da labari ya iskesu ta zama attajira ta ginawa Goggonta dallelen gida da mota, ta kaita Hajji. Haka kuwa, ba wanda bai samu rabonsa daga Amina 'yar Mas'udu ba, Baffaninta kuwa jarita basu mai tsoka na makudan kudade ta ce, su kara a gona ko su bude tireda. Amina ta sha albarka har ta gode Allah wajen tsofaffinta. Da la'asar suka kamo hanyar dawowa.
Goggo ta jaddada mata lallai ta je gidan Kawu Sule ma, don haka da suka shigo cikin gari ta gaya wa Ilya su je.
Amina dai sai da tambaya suka gane gidan Kawu Sule saboda yadda ya bi ya bushe kyamas ba shuka ko daya, ya ratattake ya lalace ba maigadi ba motocin nan nasa na alfarma. Haka dai suka boye mamakinsu suka shiga.
Ashe cikin gidan har ya fi wajen lalacewa. Kai! Komai na Duniya bashi da tabbas. Atika Babar Hafiz wadda ita ma duk ta canza wahalar rayuwa ya bayyana a jikinta ta yi musu iso dakin Baffan nata Sule. Yana kwance a kan wata tsohuwar kujera.
Ta gaishe shi cikin ladabi ya amsa sai kuma nan da nan ya kama kuka yana rokonta gafara a kan yadda ya yi watsi da rayuwarta. Ya ce,
“yanzu alhakin zumunci ya kama ni, dubi yadda karayar arziki ta rufto mini rana daya. Na hada duk abin da na mallaka nasa a wani sari na auno kaya jirgin ruwan da ya dauko su ya nutse".
Ya ci gaba da sharar hawaye yana rokonta gafara, fadi yake,
"Ban kyauta wa Yaya Masa’udu ba, ba abinda bai yimin ba a rayuwa, ‘yar kwaya daya na kasa rike masa a bayan ransa. Idan na mutu ba ki yafe min ba, ba ni da abin da zan iya yin uzuri da shi ga dan uwana, son zuciya kadai da rudin abin duniya".
Ta tabbatar masa da cewa, da ma ita da Goggo ba su kullace shi ba.
Ya ci gaba da gaya mata, "Ba don Hafiz ba, da abin da za mu sanya a bakin salatinmu ma babu. Ga shi shi kuma mace ta mallake shi, sai dan abin da ta ga dama ta ke sa wa ya ba mu. Ba kuma ya nan yanzu an canza masa wajen aiki zuwa Adamawa".
Haka Amina ta baro gidan Kawu Sule bayan ta yi masa ihsani mai yawan gaske wanda zai dade bai manta ba. Suna tafe a mota suna tattauna al'amuran rayuwar duniya masu ban tsoro. Ta tausaya wa Kawu Sule, ta koka yadda al'umma muka yi watsi da martabar zumunci, kuma a haka wai muna burin shiga aljannah. Bayan duk martabar zumunci da darajja shi da Allah (S.W.T) ya yi, Ya yi mana umarni da mu kyautata shi, yana daga cikin manya-manyan hanyoyin shiga aljannah. Allah ya sa mu dace, amin.
Ba su iso gida ba sai karfe takwas na dare. Wata mota ce 'yar karama mai duhun gilasai 'tint' a kofar gidan Goggo, ta dan fara tsufa duk ta karkarce kuma ba a shaida wadanda suke cikinta saboda bakaken gilassanta.
A daidai sanda Ilya yake kokarin sanya motar a inda ake ajiye ta. Amina ta ce, "Hala Goggo ta yi baki ne?"
Ya ce, "Ko kuma sabon saurayi ki ka yi ba?"
Ta harare shi ta bude kofar bangarenta ta fita. Kanta tsaye ta shiga cikin gida, ta baro Ilya a waje. Ya juya kan motar ya nufi gidansu budurwarsa Sadiya.
Chapter 8 · 0% Book details