← Book details Sanadin Kenan Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 14

Sashe 4

Sanadin Kenan Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alamu Dr. Amina ta ji na an zauna a gefensu. Ta yi saurin bude ido, ta juya inda ta ji alamun zaman mutum din da kamshin turarensa na koyaushe ya gaya mata MA'AROUF JI-KAS ne.
Hadiye kukan ta yi baki dayansa ta saki Ameena ta ba shi baya. Bata so ya ga kukan ta ba, bata so ya ga hawaye a idonta ba kada ya yi zargin tana kuka ne don za ta bar Government House.

"Kukan naku ya yi yawa...".

Ya fada a hankali.
Ba ta ce komai ba, ya koma kan diyarsa.
"Kukan me ki ke yi haka Ameena?"
Ta share hawayenta da tafukanta biyu, kafin cikin shessheka ta ce,
"Aunty ce take hada kaya za ta koma gida yau, wai saboda na warke. Daddy ni ma ba zan zauna ba. Aunty zan bi Daddy......".
Ya janyo ta jikinsa, ya aza ta gefen kafadarsa ta dama yana lallashinta, "Ameena makaranta zan sanya ki, wadda ake kwana acan. Dr. Amina ta gama aikinki za ta koma asibiti, tacigaba da taimakawa wasu marasa lafiyan, za ta yi aure ta haifa maki kanne. Ba kya son wadannan ci gaban ga Auntyn taki?"
Ta yi sheshsheka.
"Ina so Daddy. Amma ita zan bi, bana son makarantar kwanan......".
Rigima sosai Ameena ta ke yi, ta birkice musu, hatta Dr. Amina ta tsorata da borin da yarinyar ke yi, ta juyo ta kamo ta tana nata lallashin. Amma Ameena ta fizge ta tubure.
Ya kai hannu ya cire hular kansa da ya mayar ya ajiye a gefe, sai gumi yake duk da na'urar sanyaya daki da ke aiki babu kakkautawa. Idanunsa sun kada don ko fushin Ameena ba ya so balle kukanta, shi ma ya san zamanta da Laila ba zai yiwu ba, Ji-kas ne waje na farko da ya yi tunanin maida ita ta zauna wajen Hajiya.
Amma lokacin shiga makarantarta ya yi har ya wuce, ya kamata a ce tana Primary 1 amma ko nursery ba ta fara ba, shekarunta shidda. Abin da ba ta sani ba shi ne; ya fi ta jin tafiyar Dr. Amina.
Wata maceguda daya tal a duniya da ta shigo cikin rayuwarsa ta sauya ta. Rana daya ta yi fatali da bulullukan da ya gina rayuwarsa a kai na falsafar auren mace daya. Ya dade yana nazarin kansa akan Amina kafin wadannan bulullukan su ruguzo. Bai taba haduwa da mace mai kyawawan halayenta da nasibobinta ba, (he’s sorry to say) hatta A’ISHA.

Amina Mas'ud Shira, ta dade da canza wannan tunanin, ta kawo sabo fil ta gina, kullum kwana yake ya tashi da tunanin ta, ta inda zai tunkareta kai tsaye ya kasa. Ba wai ba zai iya gaya mata ya yanke shawarar hada rayuwa da ita ba ne, a'ah! Azancin fadar hakan ne babu, tunda ya gama cika duniya da furucinsa na mace daya ta ishe shi rayuwa, a talabijin ne, a jaridu ne, a radiyo ne da sauransu. Shi ya sa ba a so mutum ya ce ya tsara wa kansa rayuwa, muna namu Allah na naSa, rayuwarmu tun haihuwarmu tana rubuce ne a allon lauhul mahfuz. Ya nisa a hankali ya dan saci kallon Dr. Aminah, wadda ke faman fyatar hanci, ta ci kuka har ta gode Allah. Itada little din baisan wadda tafi tikar kuka ba.
"Ki daure ki kara kwana biyar, ban gama sallamarki ba ai, da bakina nace na sallameni ne iye da kike faman hada kaya?Kokari kike ki sallami kanki, albashin wannan watan bai shiga account dinki ba, tun jiya ban zauna ba balle inyi magana da Turaki, kaina yayi zafi ki barni in gama da abubuwan da ke gabana please".
Ta sunkuyar da kai, cikin ladabi ta soma magana da murya mai tsananin taushi. "I’m sorry You’re Excellency, na riga na yi waya da Goggo, na fadi mata yau zan koma, alreadynace ina hanya......".
Ya bude idanu sosai ya dube ta daga kankance su da yake yi a baya.
"Da iznin wa kika yi hakan? Ok. Sai ki fadi yadda za a yi da Ameenah......".
Da sauri ta dago ta dube shi, jin yadda yayi maganar fada-fada, bata ga laifi cikin abinda tayi ba, wannan wace irin tambaya ce? Shi ya kamata ya fadi wannan ai, ita ya za a yi ta sani, shi da 'yarsa?
Ya karanci abin da idanunta suka fadi, ya kara janyo Ameena jikinsa suka hadu suka narke mata,kallon ta yake straight into her eyes, wani ‘chemistry’ na fita daga narkakkun kwayan idanunsasuna shiga nata. Ita ta fara dauke idonta. Ilahirin jikinta babu inda baiyi la’asar ba, da karbar wani sabon yanayi da bata taba tsintar kanta a ciki ba.Data sake dagowa ta dubesusai suka bata tausayi. Ba ta san lokacin da ta bude baki ta yi magana ba.
"In za ka ba ni ina so, da ma Goggo ba ta da wadatar 'ya'ya. I'm sure za ta hada mu ta rike da amana".
Murmushi ya yi, domin ya lura iya gaskiyarta ta yi furucinta,cike da wauta da gabunta irin na ‘yan fari zai ce ko auta?.
"Ku kuma ‘physiotherapists’ haka ku ke zama gaban Goggonninku ba kwa ko tunanin yin aure? Al’adar ku ne yin hakan? Dube ki don Allah (close to 26)amma ko kunyar ambatar Goggo za ta rike kuba kya yi bayan ke ma kanki kin isa zama Goggon wasu irin su Ameenata. Amina Mas'ud Shira, in kin amince ki maye min gurbin Babar Ameena. Ina nufin, ina sonki, ina kaunarki ina ra’ayin aurenki ba don Ameena ba, I just love you, so do I since..... Amma fa idan har ban yi miki tsufa ba.
Ina son dukkan halayenkiAmeena wadanda su suka ja ni ga kwadayin ki zamo cikin iyalina. Wannan sakona ne gare ki da Goggo, na ba ki kwana uku ki yi tunani dakyakkyawan nazari ki kuma yi shawara da Goggo. Ban yarda kiyi shawara da kowa ba sai ita. Kwana uku bai yi kadan ba? Dr. Amina ki ba ni amsa!".
Amina wadda ta mutu a zaune, tun daga farkon furucinsa, 'In kin amince ki maye min gurbin Babar Ameena...' ta daskare ta kasa motsawa, sai dai abinda ya bata mamaki shi ne; jin can wani lungu na zuciyarta ya yi sanyi daga azabtar da yake yi na rabuwa da Ameena da Babanta,
"........ Amma fa in har ban yi miki tsufa ba...”.
Ta tuno jimlarsa ta gaba.
A wannan karon sai ta yi murmushi. A shekarun nasakwarai zai yi wa 'yammatayara irin masu shekara 18 da yawa tsufa, to ita mai 26 ta ce me? Kada dai sake-saken zuciyar nan yana nufin tuni zuciyarta ta aminta da soyayya da kaunar Baban Ameena?
Mutumin da duniya ke so, ba abin mamaki ba ne in itama ta so shi. Sai dai fa nata feelings din daban suke da na sauran al'umma irin su Yayanta Ilya, natanare extraordinary; ba na citizen ga leader dinsa bane, bata taba jin irinsu a kan kowa a duniya ba.
Kamar da ma suna ajiye a wani sako na zuciyarta ne, jira suke a sanya kara a zunguro su. Kuma yanzun aka zunguro sun. Kamar tun da ma can an halicce su a cikin kirjinta ne.
Ta yi nisa a duniyar sake-saken nan, ta sunkuyar da kai ta kasa dagowa. Ba ta san sanda ya mike ya nufi kofa ba. Sai da ya murda marikin kofar ya dan ba da karaAmina ta dawo daga duniyar tunaninta. A tsakiyar kanta ta tsinkayi sautinsa yana fadin.
"In kin gama kintsawa Akilu na jiranki. Ameena za mu wuce Ji-kas da ita, ki gaida Ilyas!". Ya fice.
Ta mike cikin sanyin jiki ta ci gaba da harhada yanata-yanata da kayan amfaninta. Ameena ta yi kuka ta gaji, ta bingire ta yi bacci a wajen. Wannan damar ta samu ta silale da akwatinta biyu. Duk kayan sanyawar da ta tarar a gidan ta yi amfani da su a nan ta barsu, ba ta dauki ko daya ba.
****
A cikin mota suna tafe suna gaisawa da direba Akilu, ta ji shigowar sako a wayarta. Ta dauko ta duba, sakon shigowar kudi (Alert) ne daga Kwamishina Usman Turaki. Adadin kudin sun ba ta tsorofiye da na baya, sun tada hankalinta. Da hanzari ta dannawa malamin nata kira.
Dr. Turaki ya san za a yi haka, kuma tuni ya shirya karbar kiranta, don haka tana kira ya yi murmushi ya dauka.
"Dr. Amina ya aka yi?"
Amina ta feso ajiyar zuciya. Ta tsane gumin daya tsatstsafo mata a goshi da hankicin ta.
"Doctor wannan kudin sun fi karfina, me na sayar muku? Me na yi muku na wahala haka? Doctor na fi son iya cikon albashina, Goggo za ta yi zargi, wanda dama kullum cikinsa nake a gurinta".
Ta jero maganganun a jere babu shan numfashi,amma cikin taushin murya mai nuna ladabi da damuwar da take ciki a fili.
Dr. Turaki ya yi magana cikin muryar kwantar da hankali.
“Take it easyAmina. Me na gaya miki sanda za ki fara aikin nan? In ban manta ba na ce da ke, 'Allah ya sa ta hannunki za ta samu lafiyar, ina addu'ar tukwicin hakan ya zamo naki ne'. Anyi haka ko ba’ayi ba?
Kinyi kokari sosai a kan Ameena, ta samu lafiya a hannunki.Idan Ma'arouf ya mallaka miki rabin abinda ya mallaka ba zai ji komai ba fa. Sai bai yi hakan ba, ya yi daidai hankali da tunani don kada ya razana ki. Ina so ki sani, wane neGwamna kuma Engnr. Ma'arouf Ji-kas, wannan tukwicin da ya ba ki kwatantawa ne ba kankat ba a kan son da yake yi wa 'yarsa Ameena. Ki sanya a rankiilminki ne ya ba ki ba Ma’arouf ba. SANADIN KENAN!
Ki yi wa mahaifiyarki bayani kada ta damu, ilmin da ta tsaya miki ki ka yi ne ya ba ki, babu matsayin da ilmi ba ya baiwa mutum a rayuwa. Sannan a wajen His Excellency wannan kamar an fitar da allura daga kogi ne (so relax please, say thanks to Almighty Allah, not Ji-kas)".
Chapter 4 · 0% Book details