Sashe 10
Sanadin Kenan Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
*****
Sujjada ce kadai Ilya bai yi wa Amina saboda girmamawa da kauna lokacin da Goggo ta fayyace masa ko me kenan a washegarin ranar, Ji-kas nasa zai auri Amina. Ya shirya sati mai zuwa zai raka kwamishina Turaki da waliyyan Baban Ameena Shira wajen iyayenta maza a yanke maganar daurin aure.
Allah ne ya yi ba zai hadu da su ba, don da ya sauke Amina bai shigo gidan ba ya kada kan motar ya tafi zance wajen budurwarsa Sadiya. Don bai taba kawowa a ransa sune suka zo a wannan kujajjiyar motar ba.
A lokacin ya gaya wa Goggo shi ma yarinyar da yake nema an ba shi, kanwar babban abokinsa ce, an ce ya turo in ya shirya. Yana rokon a yi daurin aurensa rana daya da na Amina, don ya samu tubarrakin ta, ita din ta zamo yarinya mai sa’a mai albarka a rayuwarta. Gidan da ta rushe ta sake gine masa, an gama komai.
Goggo ta ji dadi, Ilyanta ma zai zama magidanci, Amina da Ilya za su kawo mata jikoki kwanan nan...... Sai godiyar Allah.
Amina a can dakinta bayan fitar Goggo, wayarta ta rike tana jujjuyawa, umarnin Goggo ya yi mata tsauri, ga shi Goggo ta ki karbar uzurinta, ta ce dole ita za ta kira Ma’arouf ta ce ta amince za ta aure shi. Shekarar ta guda tareda Ma’arouf Jikas amma sau biyu ta taba kiransa a waya, kuma duka dalili tayi. Tana son kira na uku ya zama wani dalilin ba wannan ba.
"Goggo kin kasa ganewa, jan aji a wurin diya mace ai wani abu ne mai daraja. Haba Goggo ya ya za ki ba ni wannan umarnin mai zafi?" Abin da ta ke fadi a fili kenan ita kadai kamar zautacciya.
"Maza masu wuyar samu a wannan zamanin irin Ma'arouf Habibou Ji-kas a ke ja wa ajin Dr. Amina? Anya ba zai tsitstsinke ba?" Wani sako na zuciyarta ya kawo wannan kalubalen.
"Banda SANADIN ciwon 'yarsa kina tunanin haduwa da shi ma ko a hanya abu ne mai sauki? Balle har ya yi bad-da-kama ya tako gaban mahaifiyarki da kafafunsa? Zauna nan kina ta jan ajinki Anty Laila ta kwace abinta ya kira ki ya ce ya fasa.......".
Ita da kanta sai da ta yi wa kanta dariya. "......Baban Ameena ya maida ni zautacciya saboda sonsa da kaunarsa...!".
Abin mamaki sai ga kira ya shigo cikin wayar. Da ma kuma wayar na rike a hannunta, 'JI-QAS' kamar yadda ta yi 'saving' shi ke yawo a madubin wayar.
Shidewa ta yi na wucin-gadi, daga bisani murmushi mai taushi ya bayyana a kan siraran labbanta. At last!Ya cece ta daga umarnin Goggo mai tsauri da hasashe daban-daban da zuciyarta ke kawowa akan hakan. Ta tabbata Ma'arouf na sonta, ya damu da ita, ya ajiye rawanin Gwamna ya nada na yakin neman aure da neman soyayya. Ita ta fara yin sallama bayan ta amsa, ta san halinsa shiru zai yi mata.
"Kina sha'aninki, Allah ya ja da ranki".
Murmushi ta yi, "Bana kowanne sha'ani, Allah ya ja da ran Baban Ameena".
"Ina ki ka je har karfe takwas na dare?"
Ya yi tambayar ne bada irin muryar da ya soma magana ba, wannan kai tsaye cike da tuhuma yayi maganar. Don haka itama ta kwantar da murya, cikin ladabi da girmamawa.
"Mun je Shira ne ni da Ilya gaida Baffannina".
A take ya sassauto, ya saki ransa. Ya koma magana da wacan muryar mai cike da kulawa da yayi amfani da ita da farko. Allah ya yi shi da son ka amsa laifi a take in ya tuhume ka.
"Da ma ku 'yan Shira ne? Kin fi kama da mutanen gabas".
Ya ba ta dariya sosai, "His Excellency kuma mutanen yamma ko?"
"Ni kaina ban san ni dan wane gari ba ne. Amma ki bari wataran mu sa Hajiyan Ji-kas a tsakiya ta ba ni gari daya cikin tarin garuruwana".
Amina ta tintsire da dariya, "Yanayin rayuwa babu inda ba ya kai mutum. Ka san kuwa Goggo 'yar Sierra Leone ce?"
"Haba! Akwai alamun haka. Dr. Amina, ba ta yi kama da cikakkiyar Hausa/Fulani ba. Wannan tsayin... wannan dogon hancin... wadannan manyan idanun... I'm always assessing daga ina Amina ta samo su???"
Ta kai hannu kamar yana ganinta ta rufe fuskarta tana dariya. Bai taba yi mata kallo uku a lokaci daya ba, amma ashe a kallo dayan yana gama kare mata kallo ne. Yadda ya saki jiki yake magana da ita a yau ya ba ta mamaki, ya kuma faranta ranta. Shi kansa har mamakin kansa yake yi.
"Well, ina cikin wani irin nishadi da ban taba tsintar kaina a cikin irinsa ba Dr. Amina. Kullum zuciya ta a takure ta ke, a kuntace, tun rasuwar matata ta fari. Amma tun daga lokacin da ki ka shigo rayuwarmu ni da Ameena takurar da kuncin suke raguwa a hankali.
Daga jiya zuwa yau kuwa da na yanke shawarar zuwa neman aurenki Goggo ta amsa mani ta bani babu ko kadan, na neme su na rasa a tare da ni. Jin kaina nake kamar ba ni ba, jina nake 'new Ma'arouf'. Wannan ya tabbatar min ke alkhairi ce a gare ni, wadda za ta tafiyar da dukkan bacin raina ta kawo min farin cikin da na rasa na lokaci mai tsawo. AMEENAH,I desperately need you in my life, in samu rayuwar aure nagartacce nima kamar kowa.
Amma Amina har yau ban ji daga bakinki kin ce kin amince za ki aure ni don kina sona ba. Ga shi kuma ni din, wani irin mutum ne da ba ya tilasta wani don amfanin kansa.Zan so in samu amsa daga bakinki Amina, mai dadi ce ko mara dadi duk a sikelin adalci daya zan dora su. Kin amince za ki aure ni in fito neman aurenki?"
Amina ta samu kanta cikin gigicewa, kunya da rashin tantance abin yi. Da za ta iya da ta ce da shi, "Na dade ina sonka Engnr. Ma'arouf Ji-kas, kawai ina tsayawa a matsayina ne".
Amina ba ta san cewa kalaman da take fadi a zuciyarta a kunnen Ma'arouf din ta ke zuba su ba.
Ya lumshe ido ya bude a hankali. A cikin zuciyarsa ya ce, "ALHAMDULILLAH!". A fili kuwa ya ce,
"......Tsayawa a matsayi kamar ya ya Dr. Amina?"
Amina ta ankara da sakin bakin da ta yi. Kunya ta kara lullube ta, ta tura kanta cikin pillow tana makale da wayar.
"Ka yi hakuri Baban Amina, zance ne irin na zuciya da mamallakinta!".
Dariya ta ba shi sosai,
"Ai ni ne mamallakin zuciyar. Daure ki yi min fashin baki a kan kalaminki. Ina so in dora shi a sikeli ne in yi miki bayani a kansa, wanda zai kwantar da hankalinki".
Amina ta nisa,
"Your Excellency, ina nufin matsayinmu ba daya ba ne, ni ba 'yar kowa ba ce, ba jikar kowa ba. Kowa ya ji ka aure ni zai yi mamaki, zai fadi abin da ransa ke so.......".
Murmushi ya yi, "Na fahimce ki Amina. Amma ko kin san a da ni malamin makaranta ne? Makarantar sakandire? Mahaifina ma haka, babu irin fafutukar rayuwar da ban yi ba. Irin wadda baki taba zato ba. To cut it short, babu wanda aka haifa da arziki, kowa a duniya yake samun rabonsa. Saboda haka kada ki kara yin wannan tunanin ko makamancinsa. Ina sonki, ina kaunarki, na yi wa Goggo alkawarin zan rike ki da soyayya da amana har karshen rayuwarmu!".