← Book details Sanadin Kenan Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 14

Sashe 5

Sanadin Kenan Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Amina ta yi murmushi ta sauke wayar daga kunnen ta. Tunda ya kashe tasa alamar bai son (anymore word from her) karin wata kalma daga gare ta. A kalla ta samu peace of mindyanzun (kwanciyar hankali). Ta yarda da duk abi da ya fada. Ta shiga tunanin zama karamar attajira mai zaman kanta sanadin ilminta, ta samu zuciyar mutum irin Ma'arouf Habibou Ji-Kas SANADIN ILMINta. Dadin-dadawa ta samu (exposure) na rayuwa kala daban-daban a gidan gwamnati, wanda za su taimaka mata wajen tafiyar da zamantakewarta har karshen rayuwarta.
Har Akilu ya yi fakin a kofar gidansu tana wadannan tunaninnikan. Sai da ta ji motar ta daina motsi ta farga.
"Sai watarana Akilu, sai watarana! Daga yau an gama!!!".
Murmushi ya yi, a ransa yace “yanzu aka fara dai”, a fili kuma ya ce,
"Ranki ya dade mungode, Allah ya kyautata rayuwarki,yadda ki ka kawo karshen matsalar ubangidanmu Allah ya kawo karshen matsalolin rayuwarki.Allah ya kara wa Ameena lafiya".
"Amin Baba Akilu, sai watarana!". Ta fadi tana 'waving' dinsa ta shige gida tana jan kafarta, sakamakon nauyin data yi mata, ga wasu tawagar hawayen sabo da suka shimfido mata, shi kansa Akilun kewarsa take, zuciyar ta na gaya mata ta rabu dasu fa kenan, ta bar gidan gwamnati har abada! Alfarmar ubangidan nasu ba mai yiwuwa ba ce agareta, ba shine irin mijin da ya dace da ita ba, ina ita ina kishi da Anty Laila?
Aka ce yaro tsaya matsayin ka kada zancen ‘yan duniya ya rude ka! Kwarya ta bi kwarya in tabi akushi sai ta fashe. Jikas, (as a governor) mijin mata da yawa ne ba shine Mr. Right dinta ba.
Tunaninta yafi karfi ga cewathe best is yet to come.....A ra’ayin ta data tsara a zuciyarta tun lokacin da ta soma mallakar hankalin kanta:Tanaso ta auri mijinta ita kadai don tanada tsananin kishi, yaro matashidaidai ita, wanda bai mallaki komai ba sai kwalin ilmin boko, wanda bai taba yin aure ba, akanta zai fara, wanda zasuyi fafutukar rayuwa tare su gudu tare su fadi tare su tashi tare, amma Jikas ai mijin mace hudu ne.
A lokacin da ta tuna alkawarin data yiwa Goggo kafin ta barta ta fara aikinsai hankalinta yayi mugun tashi......

“Duk mijin da ya fara zuwa ko waye zata bar aikin tayi aure.....”.
Akan haka suka tsaya itada Goggo, kafin ta amince mata zuwa gidan gwamnati. Ta tuno da maganganunnoble laureateZainab Alkali inda take cewa.

“Dreamsare conceived, but not all dreams are born alive, some are aborted. Others are stillborn”. (Mafarkai kamar ‘ya’ya suke, ana yin cikin su, amma ba duka ake sa’ar haifesu a raye ba, wasu tun suna ciki ake zubar dasu, wasu kuwa a mace ma ake haifarsu). In hakane ba lallai ka samu duk abinda kake so ba a rayuwa kuma ka zauna lafiya???

Akilu direbadai sai bada kayanta ya yi aka shigo mata da su don ya lura kwata-kwata bata cikin hayyacinta har ta shige gida. Abin ya wuce ace kewa ce kadai ta sanya ta a wannan halin, ga dukkan alamu akwai wani muhimmin al’amarin a tare da ita kamar yadda suke hasashensa daga ubangidansu.
Jikin sa ba laka ya ja motar ya tafi shima cikin kewar Amina.Yana addu’ar allah ya maido ta cikin rayuwarsu bada jimawa ba. Yarinya ce mai matukar kirki, girmama manya da shiga zuciya,wadda ba zuciyar Jikas kadai ta shige ba har ta wadanda ke zagaye dashi sabida halayenta ababen so.
*****
Goggonta kadai ta samu a gida, suka yi murnarsu har suka gaji. Wannan karon ma ba ta gaya wa Goggo adadin kudin da ke cikin asusunta ba. Tasan Goggo tsorata zatayi ko ta darsawa ranta zargi, ta dai gaya mata ya biya ta albashinta cikakke, da kudin tantabarunta. Ta ce masa kyauta ta ba shi, ya ce in ba ta karba ba, zai maido mata kayanta.
Goggo ta ce,
"A'a ba a yi haka ba, ki karba".
Ta yi murmushi,
"Na karba Goggo".
Sun yi sallar isha a daren ranar, bayan Amina ta idar da shafa'i da wutiri ta ji wayarta na kara. Ta dauka ta duba mai kiran 'HAJIYAN JI-KAS' Kamar yadda ta adana sunan, shi ke yawo a fuskar wayar.
Ta juya ta kalli Goggo, sai ta ga lazimi ta ke, da cikakkiyar nutsuwa, da ladabi mai yawa ta amsa kamar yadda ta saba amsa wayar Hajiyan.
"Assalamu alaikum Aminatu".
"Amin wa'alaikumus-salam Hajiya, Ya ya Ameena?"
Hajiya ta ce, "Kya bari mu gaisa ai, Uwa Mai Ameena, kwana uku baya ya kamata in bugo wayar tun sanda na ji Ameena ta mike a kan kafafunta.
To garin in kira ki saboda zumudi da farin ciki hannun nawa karkarwa ya shiga yi na jefa wayar tawa a ruwa, sai yanzu da ya zo ya hada min wata (tana nufin Ma'arouf).
Ubangiji shi Ya nufa, amma da kokarinki da sadaukarwarki. Mun gode, madalla Amina. Ba ni mahaifiyarki in tana kusa mu gaisa".
Amina ta mika wa Goggo,
"Hajiyan Ji-kas ce".
Ba tun yau ba Goggo Hauwa ta san Hajiyan Ji-kas, Amina ta sha hada su su gaisa idan ta zo (weekend) Hajiyan ta kira ta. Don haka da sanayya suka gaisa Hajiya ta yi mata godiya a kan taimakon da Dr. Amina ta bawa jikarta.
Goggo ta ce, "Babu godiya a tsakani, ai aikinta ne. Ko ba ta yi wa Ameena karama ba za ta yi wa sauran al'umma ko ba ko sisi balle Amina da ake biyanta".
Ita dai Hajiya Saude godiya ta ke tana karawa har suka yi sallama. A ganinta basu da abinda zasu biya Amina duk tarin dukiyar su.
****
Kwana daya, biyu, Amina ba ta da kuzari, ta rasa kwarin gwiwar isar da sakon Ma'arouf ga Goggo. Ta barwa zuciyarta wannan al'amari mai girma da ya tunkaro ta. Ta kasa aiwatar da abubuwan da ta saba yi yadda ya kamata saboda tunanin amsar da za ta bai wa His Excellency da kwarin gwiwar sanar da Goggo. Tuni dai zuciyarta ta riga ta gama nutso da ninkaya cikin maliyar So. So irin wanda ba za ta iya fassarawa ba.
Tun tana ignoring fassarar abubuwan da take ji din da ganganakan Ma’arouf, da kalubalenta kala-kala marassa madafa, ba shine Mr. Right ba da sauransu, wannan da wancan,har ta yarda ta fassarasu da Son Ma’arouf ne. Idan akwai abinda yafi Mr.Right to Ma’arouf to Ma’arouf Ji-Kas ne. Ta yarda da Zainab Alkali.
Wanda ba lokaci daya ya shiga zuciyarta ba, ya dade yana kassara ta, yana huda kasusuwa da bargonta a hankali a hankali (like a biological VIRUS). Bata bashi muhimmanci ba ne tun lokacin da ya soma samun muhallin, don sanin cewa abune da ba zai taba yiwuwa ba, zuciyarta yaudararta ta ke yi. Don ba ta taba ganin wata alama da ke nuna hakan daga Ma'arouf Ji-kas ba. Mutumin da ko cikakken kallo ba ta ishe shi ba a baya.
A hankali suka soma shakuwa, shakuwa mai yawa akan siyasarsa, duk da haka babu wata alama makamanciyar wannan data gitta a tsakaninsu.
Sannan kuma ta kan tuna matarsa 'yar kwalisa Anty Laila. Ina ita ina iya shiga kishi da wannan kasaitacciyar mace? Wadda bata ajiye kanta anan kusa ba? Yaushe ma ta kai wannan matsayin banda giggiwa irin na zuciya? Beside, tana jin kamar lokacin yin aure ya wuce mata, babu wanda zai kara cewa yana sonta daga shekaru ashirin da shida. Tunanin komawa karo ilmi ne a ranta da zarar ta bar gidan Gwamnati, don haka ta dauko gingimemen bulo da katon dutse ta danne gurbin da kedarsa soyayyar Ma'arouf a zuciyarta (A baya kenan).
Amma daga kwana uku bayada ya furta neman soyayyarta da ra’ayin sa na son aurenta da kansa ba waya ba ba aike ba, gaba daya sai ta ji kamar an sauke wannan bulo da dutsen da ta adana tsofaffin ajiyarta suka fito suka yi yabanyakoriya sharr suka lullube zuciyarta.
To amma da wane harshe za ta gaya wa Goggo? Ya ya Goggon za ta dauki al'amarin? Kada ta zarge ta da cewa tun can baya soyayya ta ke yi ba aikinta ba, duk da ta san Goggo ta yarda da ita dari-bisa-dari. Hasashen zuciyarta ne wannan kawai. Gaskiyar magana shi ne, kunyar Goggo ta ke ji. Bari ta yi shiru abinta kawai. A ina zai ganta har ya bukaci jin amsa daga bakinta? Ta san yawan ayyukan da ke kansa ba za su bari ya kara tunawa da wata Dr. Amina ba.
Don haka ta like bakinta da (super glue) ta shiga sabgoginta da kula da tantabarunta. Lokaci-lokaci littleAmeena Ma'arouf na fado mata a rai, sai tace cikin ranta, ko an kaita makarantar kwanan? Ko ba’a kaita ba? Ko me take ciki? Amma in ta tuna tana hannun Hajiyan Ji-kas sai ta ji damuwarta a kan kewar yarinyar ya ragu. Tana da yakinin tana samun kauna da kulawa yadda ya kamata fiye da na Babanta.
Ta lura shi kansa ba ya alakanta rayuwar diyarsa da matarsa Laila, ko me ye dalili? Oho!

*****
Chapter 5 · 0% Book details