Sashe 6
Sanadin Kenan Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
MA’AROUF JI-KAS!
A ofishinsa yake, bayan tafiyar Dr. Amina da kwana uku. Mutanen da ke son ganinsa sun fi dari. Ayyukan da ke gabansa wadanda suke bukatar ya sanya hannu (signing) sun fi guda hamsin. Amma me? Ya kasa yin ko daya, ya kasa (attending) ko mutum daya. Idan ya tuna in ya koma gida ba zai tarar da Dr. Amina da Ameena ba sai ya ji wani irin kadaici da damuwa sun taru sun lullube shi. Kamar shikadai ya ragea duniyar Subhana.
Ya kasa aiwatar da komai wadanda ya saba yi a rayuwarsa. Hatta kiran waya damuwa yake jefa shi don jira yake ko Amina za ta turo masa sako, ko ta kira shi ta ba shi amsa kan bukatarsa, na zamowarsu abokan rayuwar juna na har abada, amma har aka cinye kwanaki ukun, babu 'text' ko wayar Dr. Amina.
A karshe ya gane mafitar daya ce, ya bar komai ya ajiye komai dake gabansa, ya yi yakin mallakawa zuciyarsa abin da ta ke so da kauna, wannan preciousgem mai daraja wato AMINATU don ya zauna lafiya cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, wata da watanni yana dannewa, yana boye halin da zuciyarsa ke ciki.
Amma yanzun an zo wani limit(geji) da ya fahimci cewa, ci gaba da dannewar nan ba abin da zai haifar a gare shi sai (psychological depression), mafitar kawai ita ce mallakarAMINA.
Wadancan falsafofin na son rai wato nagudunauren mace fiye da daya, a yau ya sauke su a gefe, ya cinna musu ashana ya kone su kurmus! Dama bai taba rantsuwa a kai ba. Ya kan fada ne dai kawai a matsayin ra’ayin sa. Ya fahimci in ya tsaya ta jin amsa daga bakin Amina zai shekara bai ji ba, soyayyar da ke cin zuciyarsa ta zauta shi. Ya yarda ko Amina ba ta sonsa to ba ta kinsa.
Ya amince zai aure ta ko da ba ta sonsa, in dai har zai mallake ta cikin gidansahe believed zai samu soyayyar a hankali, kai ko tana kinsa din ya amince ya aure ta a hakan, in dai za ta dawo cikin rayuwarsu shi da Amina, ta bar downstairs ta koma upstairs wannan shi ne babban burin zuciyarsa a yanzu, ya yanke shawarar sauke rawanin Gwamna ya nada na yakin neman soyayyar Amina da aurenta.
Ya dauki wayarsa ya kira mataimakinsa Prof. Yusuf Bugaje, ya ce duk ayyukan nan da ke gabansa ya yi masa, ya ci gaba da handling komai, zai yi hutu na kwanaki uku. Farfesan ya amsa da girmamawa komai ya koma hannunsa.
*****
Ilya ya shigo gidan da yammacin ranar da Amina ta yi kwanaki uku da dawowa. Goggo ta shiga makota barka. Ya ji dadin samun Amina ita kadai. Tana suyar awara ne da ta tashi da marmarinta tun azahar ta ke aikinta. Ta gama soyawa tana kwashe wa Ilya ya tsaya a kofar kicin din.
"Anty Amina, ina nawa? Raina ya biya wallahi".
Ta ce, "Dauki guda daya, shugaban kicin din gidan Gwamna da kwadayi, ban taba ji ba".
Ya kyalkyale da dariya ya mika mata farar leda.
"Ungo ga guzurin gidan Gwamnatin na yo miki ke ma, don na san kwana biyu kina kewarsu".
Ta galla masa harara, "Wa ya ce da kai ina cin abincinsu? Wanda na saba ci shi nake dafawa da kaina".
Ta dai karbi ledar ta leka, (shawarma fal, soyayyun kaji da samosa, springroll da wani dunkulallen cake). Ita da ta ke cewa ba ta ci, sai ga ta tana cika baki tana taunewa tana hadiyewaharda lumshe ido, kunnenta har motsi yake. Ilya ya dinga yi mata dariya, ya yi kyau ya yi kiba, ya yi tsaf farinsa na Fulani ya fito. Amina har mamaki ta ke yadda Ilya ya murje cikin 'yan watanni ya waye sosai, kamar ba shi ba.
Ya ja kujera 'yar tsugunne ya zauna, "Ke muhimmiyar magana ta kawo ni, gidan Goggo ya kammala fa, har an yi fenti. yanzu kudaden abubuwan da za a zuba za ki tura ta account dina, ga takardar abubuwan cikin gidan su kujeru, air-conditions, kayangado, labulaye, cooker gass, carpet, kayan kicin da sauransu. Ga list din da kudin komai a rubuce a kasansa".
Amina ta karba tana dubawa, ta yaba da komai, Ilya dan baiwa yana ba ta mamaki, ya san kaya na zamani masu tsada, amma da quality da nagarta, ban sha'awa da burgewa. Ta zabi kalolin da ta ke so wanda Goggo sune kalolin da ranta ke so, ruwan madara da brown, ta ce, "An jima zan sako (transfer) in na gama ciye-ciyen nan, yunwa nake ji yanzu, motar fa?"
"Mota tuni ta iso tana rumfar adana motoci na gidan, kamfanin ‘Julius-Berger’ na hayo ta hanyar wani abokina a gidan gwamnasukayi ginin cikin sati biyu.Yanzu har ya fara bushewa. Nafi so sai ta je can ta same ta. Amma ya za mu yi mu daga Goggo da komai nata daga gidan nan ba tare da ta sani ba? Sai dai mu dauke ta mu kai ta har dakin barcinta?"
Amina ta yi dan tunani, "Ta ce min za ta Shira jibi bikin 'yar Kawu Bilya, kuma tun safe har dare don haka ka yi kokari daga yau zuwa gobe a saka komai a muhallinsa. Washegarin dawowarta da safe zan ce mata ta raka ni asibiti duba matar Kwamishina Turaki ta haihu na san ba za ta ki ba, Astagfirullah na shirya karya".
Ilya ya yi dariya, "A kan abin alkhairi ki ka yi karyar ai, Allah zai yafe miki. Gama ci maza ki turo min".
Ta ce, "Saura kai Ilya. Gidan nan na ba ka shi halak malak. A rushe shi ko a yi furnishing dinsa da kyau ya zama na zamani ka nemi mace haka ka yi aure Ilya. Ni zan dauki nauyin ginin.Ni dai burina ka yi aure Goggo ta ji dadi, tunda nawa babu rana".
Ilya ya tsura mata ido, kwalla suka cika idonsa.
"Dr. Amina hidimar ba ta yi yawa ba? Na fa tsaya da kafafuna yanzu ina tari tunda na fara aikin nan".
"Ba ruwana da aikinka Ilya. Burina in faranta wa wadanda suka tsaya min a rayuwa ta a lokacin da na rasa mahaifi. To Ilya kai ne mutum na biyu bayan Goggo da ku ka tsaya wa ilmina. Ba ni da abin da zan biya ka sai dai in kamanta ihsani. Baba Talatu zan turo maka kudi ka ba ta ta yi duk abin da ta ga dama da su, ta tallafi ilmin marayunta. Haka Inna Zulai. Za ka raka ni Shira kuma in na kara hutawa in ba su abin da ya rage min a account bana bukatar komai a rayuwa ta, I'm o.k, mota kawai zan saya saboda zuwa aiki".
Shi dai Ilya ya kasa magana daga karshe ya yi ta sanya mata albarka kamar shi ya haife ta.