← Book details Sanadin Kenan Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 14

Sashe 1

Sanadin Kenan Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

SANADIN KENAN!

3

SUMAYYAH ABDULKADIR
[email protected]
[email protected]
SADAUKARWA
Sadaukarwa ne ga duk makaranta littattafan TAKORI. Wadanda na sani da wadanda ban sani ba, Allah ya hada mu cikin alherin sa, har zuwa ranar da muka daina numfashi.

DON TUNAWA DA
Domin tunawa dake marigayiya Kakata kuma Goggo na HAJ. HAWWA ABUBAKAR WALI (Hajiya mai Mage).

GARGADI
Ban yarda a kwafi wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba ko karanta shi a rediyo ba tareda iznina ba, hakan zai kaimu ga tsayawa gaban hukuma, wadanda bansan inda kuke ba kuma zamu hadu a kotun Allah ranar da bawa bashi da abin biyan hakkin dan uwansa sai kyawawan ayyukan sa. Takori

JINJINA
Littafin SANADIN KENAN! 3&4 Dole Ya jinjina miki AUNTY ZULAIHA ZUBAIR (Mrs. Late Tafidan Kano Hakimin Kura) sabodagudummuwarki gareshi. Aunty Zulai Madallah Allah ya kara zumunci.

FATAN ALKHAIRI
Fatan alkahairi gareku makaranta nada jimirin bin littattafaina ina yi muku fatan alkhairi a duk inda kuke nagode madallah da yabawarku.

SANADIN KENAN! 3
An shake katafaren dining-table din da nau'ikan abinci da abin sha kala daban-daban. Ga wasu greeting-cardsmanya-manya an manna a kowacce kusurwa ta falon. Mutum biyu ne zaune a 'dining' din suna cin abinci, a jikin kowanne greeting-cardan rubuta 'Welcome to Government House ILYAS'.
Duk suka dago suka dube ta da murmushi, Ilya ne da Gwamna Ma'arouf Habibu Ji-kas. (Ilyan Goggo). Ta hada ido da Ilya, wanda idonsa ya ciko da hawaye, ga murmushi yana yi duk a lokaci daya, da gani babu tambaya hawayen farin ciki ne. Ya sha farar shadda kal 'yar ciki da babbar riga da hula da bata taba ganinsa da su ba, yayi fes kamar ba Ilya ba.
Ta kama baki da hannunta cikin mamaki tana kallonsu (extremely puzzled). Baban Ameena murmushi yake yi yana dubanta, saida ya tabbatar ta gama jikuwa cikin mamakin sannan cikin rashin damuwa yace.
“Karaso mana! Ilyas ne. Ko baki gane shi bane?”Ilya na kuka da dariya, ya ce,
"Dr. Amina!".
Amina ta ajiye mamakinta a gefe, ta gunguro keken Amina ta nufo su, ta ce, "Ilyan Goggo?"
Ya ce, "Na'am Amina, SANADIN ilminki, Sanadin ilminki yau ga ni gaJI-KAS! Ba zan iya kwatanta miki farin cikina ba. Sanadinki na hadu da wanda na fi kauna a rayuwa ta......". Sai kuka.
Amina ta karaso inda suke tana turo keken Ameena a hankali, ta zauna a wata lallausar kujera a gefen Ilya, little Ameena na cikin wheel dinta a gabanta.
Ta ce"To Ilya ai ni kun kashe ni da mamaki, ban fada masa ba, ban taba yi masa zancenka ba.........".
"Kada ki cika kwakkwafi mana......". In ji Baban Amina,ya fada yana murmushi hadi da mikewa tsaye alamar sun gama cin abincin.
"Kina zaton zan amince in damka amanar 'yata guda daya ga mutumin da ba ni da cikakken sani a kansa da asalinsa? Ba abinda bansaniba a kanki da kowa naki.Ba wajenki ya zo ba, ya tsaya neku gaisa, don an gaya masa kina ta nemansa kafin ki taho last week".
Ya fada yana goge hannayen sa da bakinsa datissue ya wuce su ba tareda ya sake duban inda take ba, ya kama hannun little Ameena ya sumbata ya saki ya wuce.
Amina jikinta har rawa yake ta kara matsawa kusa da Ilya.
"Ilya ya aka yi? Last week ya ce in gaishe ka, shine nake ta nemanka in gaya maka, in kuma tambayeka a ina ku ka hadu?Ina cikin rudu. Kai ka ba shi account number dina?"
Ilya ya goge idonsa yana dariya, "Wallahi Amina ni ne. Wannan kwamishinan malaminku ya zo har gida bidar account number din da kansa ba aike ba. Goggo ta ce in ba shi. Ya tambaye ni, ni ne Ilya? Na ce ni ne, sai kawai ya ce in biyo shi.
Da farko Goggo ta dan ji tsoro kada a ce laifi na yi, na ce mata ta kwantar da hankalinta shi ne wanda ya zabeki ki yi aikin ai. Haka ya dauko ni a mota, bai ajiye ni a ko'ina ba sai ofishin Gwamna, sai ga ni ga JI-QAS ido da ido.
Ya ba ni hannu mukayi musabaha, ya ba ni ruwa na sha. Kwamishina ya gaya masa ni Yayanki ne ba na ciki daya ba, kuma kin gaya masa yadda nake matukar kaunarsa tun kafin ki fara aikin nan, da yadda na ja ku ke da Goggo ku ka je ku ka jefa masa kuri'a. Ya ji dadi sosai, ya gode mini, ya kuma gayyace ni yau in zo mu ci abincin rana tare. Wadannan kayan na jikina shi ya aika mini ya ce nashi ne, in sanya in zan zo....".
Amina ta ce, "Ikon Allah!".
Ya ce, "Ke ce SANADI ai. Ya kuma dauke ni aiki a gidan nan nima, ni ne shugaban babban kichin.
Da fari ya tambaye ni ko na yi karatu? Na ce a'a sai na yaki da jahilci. Ban taba dana sanin rashin tsayawa in yi karatun zamani ba Amina sai yau. Don cewa ya yi, da nayi karatu daya ba ni mai bashi shawara kan harkokin matasa. Duk da haka bazai barni haka ba ya san abin da zai dace dani".
Amina ta yi dariya, "Har na hango Ilyan Goggo a office".
Suka sa dariya, ya ce, "Wannan din ma da hadadden ofis dina, duk abinda da za’a ci a gidannan nine mai bada umarni ga masu dafawa,cefanen gidan bakidaya yana hannuna, amma fa da kyar in zan karba, in na bar Goggo ya ya za ta yi da tata sana'ar tunda ni ne karfinta?"
Amina ta girgiza kai "Ka nada wani cikin yaranka masu tayaka wanda ya gane kan sha’anin sosai, amma kai namiji ne iyali za ka tara Ilya, dole ka tsaya da kafafunka.Goggo ma za ta fi son haka fiye da a ce saboda tata sana'ar kai ka kasa tsayawa ka gina kanka".
Ya mike yana sabe hannun babbar riga, "Ke kin faya tsari. Bari dai sai na yi shawara da Goggon. Ni na tafi".
Ka gaida gida, Goggo da Inna Zulai, Talatuna da tantabaruna".
"Za su ji! Wannan ce 'yar taki?" Ya fada yana dafa kan Ameena.
"Ita ce Ameena".
"Allah sarki! Yarinya kamar Babanta ya yi kaki. Allah ya ba ki lafiya Ameena".
Ameena karama ta ce a hankali, "Amin".
Suka yi sallama ya tafi, ta tura Ameena suka koma daki.
Chapter 1 · 0% Book details