Sashe 9
Sanadin Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wadanda jin dadin rayuwa ya hana ku san da su, sai yanzu da suka soma zama mutane yadda za su amfane ku? *** *** *** Wannan zangon su Amina karatu suke ka in da na in, domin daga shi ne za su shiga aji shida na sakandire in sun dawo hutu. Ranar wata asabar suna labirare (library) ita da Hafsa, a gabansu tintimemen littafi ne an rubuta (Organic Chemistry) na T.W Graham , suna aikin wani (assignment). Hafsa ta ce, Amina Mas ud, me ki ke so ki karanta ne a jami Ba tare da ta dago ba tana ci gaba da rubutun da ta ke yi, ta ce, Ciwon da ya kashe Babana. Na ga yadda yake, ina tausaya wa masu fama da shi, domin rabin jikinsu ne a raye, rabi a mace. Sannan jinyarsu sai mai hakuri, juriya da sadaukarwa. Na jinjina wa Goggona da ta yi jinyar Baba babu korafi, babu gazawa. Ina rokon Allah ya sada su a inuwar aure a gidan aljanna Hafsa cikin tausayawa ta ce, Wane ciwo ne? Ta ajiye bironta a kan littafi stroke Hafsa ta ce, kina nufin za ki karanta (Physiotherapy) ne? Amina ta ce, Insha Allahu Hafsa ta ce, Amina kin rakito karatu mai tsayi, anya Goggo za ta barki? Maganar aure fa? Ko da wasa ban taba ji kin yi min maganar wani da sunan yana sonki ko kuna (dating) ba, ni na gaya miki har kudin aurena an karba, mahmud yana Russia yana nasa karatun, (family friends) muke da su, da ya kammala shekara mai zuwa zai zo daidai da mun kammala mu ma za a yi mana aure mu koma tare, in shiga jami ar a can. Ki yi kokari ki fidda miji Amina, don in ki ka fara karatun likitanci ba za ki samu lokacin irin wadannan abubuwan ba. Gabadaya hankalinki zai afu ne ga cimma abin da ki ke son cimmawa, amma da aurenki in ki ka yi sa ar abokin rayuwa komai zai tafi miki da sauki. With someone aside who is always helping, supporting and encouraging your dreams will be realized (tare da wani a gefenki wanda kullum zai kasance mai taimaka miki, da ba ki kwarin gwiwa mafarkanki za su zamo gaskiya). Mace na bukatar namiji a gefenta (as soon as) ta kai munzali. Don kiyaye addini da mutunci. Ki yi nazari, karatu ba ya hana aure, haka aure ba ya hana karatu Amina ta mike ta soma tattara takardunta don Hafsa ta ishe ta, ba ta da gamsasshiyar amsar da za ta bata, don Goggo ma abin da ta ke fada mata kenan. Ta bar mata wajen shi ne mafi a ala a gare ta. Hafsa ta jinjina kai tana murmushi, ta bi bayan Amina da kallo. Haka kawai Amina Mas ud ke burge ta. Yarinyar ta san kanta, miskilar gaske ce, sannan wani bai isa ya canza mata ra ayi ba komai kusancinta da shi, shi ya sa ba ta faye fadin ra ayinta ba ma a kan abubuwa, sai dai ta yi a aikace a gani. Ita ma ta mike ta harhada nata takardun ta bi bayanta. *** *** *** Ilyan Goggo da Goggo sun baje kudi a tsakar dakin Goggo suna ta lissafi, Ilya ya ware wasu gefe ya sanya a leda ya mika wa Goggo, Ajiye wadannan a gefe, kudin makarantar Amina na shekarar karshe, Waec, Neco da Jamb kamar yadda aka ba mu list Goggo ta amsa ta aje a gefe, ita ma ta ware wasu ta mika masa, Wadannan kuma dubu sittin ga su, ka sayi sabon babur ka dinga amfani da shi, kada ka yi min musu, umarni ne ba shawara ba Ilya ya sanya hannu biyu ya karba, idanunsa suka ciko da kwalla. Abin da zai ci sau uku a rana Goggo ce, suturar da zai sanya ita ce, Allah bai ba shi kwanyar karatu ba, amma Goggo ba ta barshi ya zauna cikin duhun jahilci ba, ta sanya shi dole ya shiga makarantar yaki da jahilci, ga albashi 10% da ta ke ba su duk wata shi da Talatu. Me zai yi ya biya wannan baiwar Allah ban da ya ci gaba da tsaya mata a kan kasuwancinta saboda Allah? Abin da yake fada cikin zuciyarsa ke nan. Aka yi sallama aka daga labulen falon, Hafiz ne da kayan ma aikatan MTN masu kalar yellow da baki a jikinsa, da gani daga aiki ya dawo ko gida bai je ba. Goggo da Ilya suka amsa, ya ce, Inye! Hajiya Goggo da Ilyanta, zakka ake fitarwa ne? Goggo ta yi murmushi, Ilya ya ce, Yaya hafizu ka lallashi Goggo ta yarda a bude mata (account) a banki tunda tana da abin da ya fi karfin abin da ta ke zubawa a dashi duk wata, ni ban ce ta daina dashi ba, amma abin da ya haura abin da aka zuba a dashin a sanya shi a banki. Karatu Amina ba ta kare ba don ta gama wannan tunda jami a za ta shiga, kuma likitanci ta ke so, an gaya min kuma ya fi kowanne karatu cin kudi Hafiz ya samu kujera ya zauna, duk da Ilya ya ba shi haushi da ya ce Amina jami a za ta shiga, ya danne bacin ransa. Goggo me ya sa ba kya son ajiya a banki? Cikin nutsuwa Goggo ta ce. Ba wani abu ba ne Hafizu, abu ne na rai da rayuwa, ka gama wahalarka ka zuba a banki, ka zo ka mutu wani naka bai san da su ba tunda rayuwar ba ta da tabbas Jikin kowannensu ya yi sanyi. Da kyar Hafiz ya ce, Ba wanda ya san gawar fari, amma mu ga mu, mun san kin yi ajiya a banki Idan dukkanmu muka fadi muka mutu fa? Insha Allah Goggo ba za mu fadi lokaci daya gabadayanmu ba Ilya ya kyalkyale da dariya, ita ma Goggon Hafiz ya ba ta dariya. Ga shawara . In ji Ilya, A bude asusun da sunan Amina, tunda komai aka saka na karatunta ne, duk abin da ya kama ta cira da kanta ta biya, mu sakawa ne aikinmu bayan mun ware uwar kudi, na cefanen gida da albashin ma aikata Goggo ta ce, Na amince A zuciyar Hafiz ya ce, Wannan yaron Ilya kwakwalwarsa tana ja, da ya yi karatu da an ga kasuwanci . Bai gama tunaninsa ba Ilya ya kara mamakantar da shi da cewa. Goggo za a kara jari fa, dazu mai kula da kantinan cikin asibitin koyarwa (containers) ya yi min magana cewa, mu dinga kai wa kantinan cikin asibiti, an yarda da tsafta da nagartar kayanmu, kasuwa za ta kara fadada da yardar Allah Goggo ta ce, Duk abin da ka ce Ilya na san wanda zai amfane mu ne, in na dau wannan dashin maimakon a kai banki, to a kara jarin. A bude asusun da abin da ke hannuna yanzu Hafiz da ya ji ba su da niyyar sako zancen Amina ya muskuta ya yi gyaran murya. Ni Goggo ba gobe ne Amina za ta zo ba? Goggo ta maido hankalinta gare shi, Eh, haka na ji a radiyo, gobe ne hutun yan makaranta ko? To Goggo ki yi zamanki ni da Ilya mu je mu dauko ta mana? Cikin girgiza kai Goggo ta ce, Ba za ta yarda ta biyo ka ba Shi ma sai ya yi shiru, don ya san gaskiya ta fada masa. Amina ba ta son shi ya sani kamar mala ikan daukar rai ta ke kallonsa. Ya rasa abin da ya sa zuciyarsa ta kasa hakura da ita. Mata iri-iri binsa suke yana yakice su, amma Amina ce kadai ta samu nasarar tsayawa a kahon zuciyarsa. Ba irin fada da zagin da mahaifiyarsa ba ta yi masa a kan ya rabu da gidan su Amina, don su suke magance shi yake son Aminar, don su shigo cikin arzikin ubansa da ya yi musu nisa, amma da ta gama zai karkade jikinsa ya tashi, hakan ba ya hana gobe in ya dawo aiki gidan su Aminar zai koma ya ci abincin rana. Hafiz shi ne Da na farko a wurin kawu Sule da Atika, sai kanwarsa Tasnim, tana sakandire aji hudu da kadan Amina ta girme ta, sai Saifullah da bai wuce shekaru tara ba. Kamar yadda Baban Amina ya ce ne rashin yawan haihuwar na mahaifiyarsu ne, shi da Kawu Sule, su Kawu Bilya da Tasi u uba suka hada ba uwa ba. Ranar hutu Amina da kanta ta dawo gida ko hutun baya ma da kanta ta dawo, ta hana Goggo zuwa, ta ce su daina hidimarta haka (she is old enough), wato ta yi girman da za ta dinga daukar wasu (responsibilities) na rayuwarta. Yara suka sauke mata kayanta a tsakar gida ta bude jakarta ta ba su ashirin-ashirin, gidan ban da kamshin suyar kayan dadi ba abin da yake yi, Baba Talatu ce ke suyar Goggo na gefe tana kirgawa a cikin bokitan roba. Lale marhabin da yar gidana . In ji Baba Talatu. Amina ta sunkuya ta dan rungume ta ta baya, kamin ta isa ga Goggo ta yi mata cikakkiyar runguma. Ta lumshe ido cikin farin cikin samun Goggonta lafiya. Ta sake ta ta dan ja baya ta sanya hannu ta dauki (meatpie) daya cikin daruruwan (meatpie) din da aka soya, ta kai bakinta ta gutsira ta soma taunawa, kunnenta ya yi wani irin motsi har can ciki sai da ta sa hannu ta sosa. Goggo mai kayan dadi! Goggo ta yi murmushi, Ya hanya? Hamdullah . In ji Amina. Da haka ta wuce daki don ta kimtsa, ta huta. Tunda ta yi sallar la asar wani irin bacci ya dauke ta, sai yanzu ta san ta tara bacci da gajiya mai yawa a jikinta saboda jarrabawar da suka yi ta wucewa aji shida. Su Goggo suna ta aikinsu, ba su san bacci ta ke ba. Sanda aka kira sallar magriba duk suka mike. Goggo ta shimfida sallaya za ta tada sallah ne ta ankara da Amina da ke can karshen gadon katakonta tana bacci. Ta san baccin wahala ne ya kayar da ita, ba ta taba ganin yaro mai nacin karatu ba irin Amina, hakan ya sa duk sakamakon jarrabawa Amina ba ta wuce na