← Book details Sanadin Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 17

Sashe 2

Sanadin Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nagode agaida yara zasu ji. Allah ya tashi kafadun Amina Ji yayi kamar ta yi masa addu ar Allah ya sanya shi a aljannah. Wato komai na dan siyasa baya buya. Kamar kasawa ake a faranti ana terere da shi. Kowa yasan yana da ya mara lafiya. Dr. Turaki na komawa gida matarsa Zainab ta isar masa da sakon abokin nasa, ko abinci ta kasa bari ya ci. Balle ta barshi yayi wanka, amma tayi kokari ainun wajen boye azarbabinta da murnarta na yau ta yi magana da Ji-qas. Tauraron taurari a wurin al ummar Bauchin Yakubu. Zan kirashi gobe dana shiga office Haba kai kuwa Baban Aadil, ka kirashi yanzu mana muji menene? Ka sani ko kujerar Makkah ce? Dr. Turaki ya tuntsire da dariya, Zainab mai idon cin naira, ki bari Allah ya bashi kujerar Bauchin, Makkah kinje kin dawo insha Allahu Ita dai Zainab ba haka ta so ba, ta so ya kirashi tana zaune taji kwaf! Ko samu ne. Kamar yadda ya cewa matarsa, yana shiga ofis washegari ya bude tagogi Ji-qas din ya fara kira. A lokacin yana baiwa Amina golden morn ya dakatar ya daga kiran Turakin. Sai yanzu kaga damar kira na? Afuwan Yaa Maulaaya, lokutan likita a kididdige suke yayi murmushi, ba raha ya kira shi suyi ba kamar da, da ya bashi amsa don haka kai tsaye ya zarce da gaya masa makasudin kiran. Akan yar ka Amina ne. Mun bar gadon asibiti don dukkannin mu ba zamu iya ba ni da Hajiya, saboda wasu muhimman uzurirrika musamman ni da yanayin rayuwata ba na tsuguno bane a wuri guda. Sai na tsaya nayi tunani akan abinda yafi kawai inyi hiring professional Ina son hayar (physiotherapist) da zata cigaba da baiwa Amina (treatment) a gida da kula da komai nata bilhaqqi, zata bar aikinta na asibiti ta zauna da Amina a gida ta cigaba da kula da ita tsahon shekara daya mu ga abinda Allah zai yi. Zan ninka mata albashin data ke karba a asibiti sau hudu a kowanne karshen wata. Saidai Turaki ba kowacce ba, shi yasa ma na biyo ta kan ka ban bi ta kan likitocin Amina ba. Ina son wadda akwai sanayya ta sosai a tsakaninku, ka yarda da ita, ka yarda da tarbiyya da amanar ta. Mata tsoro suke bani Turaki. In kana da kudin da zaka basu babu mai zama da kai tsakani da Allah. Yau na firgita na tsorata da al amarin mata yadda baka zato. Sun karya min zuciya sun kara sa ni kewar Mahaifiyar Amina. Mata irin ta tsiraru ne a cikin al umma. Dr. Usman ya ja numfashi, babu wadda ta zo masa a rai sai likitar da ya raina da hannunsa, ya kwashe shekaru bakwai zuwa takwas tare da ita, ya lakanci dukkan halayen ta; Dr. Amina Mas ud Shira! Dukkan suffofin da Ma arouf ke so (proffessional) din ta kasance dasu Amina ce ta mallake su. A dai likitocin wannan bangaren nasu (physiotherapy) da ya sani a duniya. AMINA MAS UD SHIRA! Ya furta da sauti mai dan kauri (husky) kuma a hankali, kamar a zuciyarsa ya fada, Ma arouf din ma bai ji sosai ba. wacece haka? Suna ne na likiciyar data dace da komai daka ambata ne. Dalibata ce, ni na raine ta, physiotherapist ce Ka yarda ta hada duk abubuwan dana lissafa a sama? har ma ta zarta. Proffessional ce data san kan aikinta at a very young age. Bayan lakantar aikinta harda baiwa cikin al amarin ta. Ta karbi award shekarar baya na Best Physiotherapist in Africa . Sannan yar babban gida ce, by saying this, ba ina nufin gida na masu kudi ba a ah, gidan tarbiyya da mutunci. Ka fahimce ni? Na fahimta. Ka yi mata magana toh. Cewa zan dauketa kwangila na tsawon shekara daya in bata da aure. Ta kula min da mai sunanta paralysed diya ta. Zan ninka mata albashin ta sau hudu in ta amince. Duk karshen mako sai ta tafi gida, nikuma zan maida kwana biyun lokutan zamana da Amina in cigaba da kula da ita har ta dawo.... .......excuse me please.... Turaki ya katse shi da wani irin tune mai kama da tun zura a muryar sa, meye amfanin matarka idan har bazata iya kula da abinda ka haifa ba ko da na kwana biyu a sati? Murmushi yayi, zuciyar sa ta hasko masa yadda karti biyu suka tube Amina a bandaki a bisa umarnin Laila, tana gefe toshe da hanci, idanunsa suka wani irin rine sukayi jajawur da kyar ya bashi amsa. Ban aureta don in sa ta jinya ba. Yaushe zaka yi magana da likitar? lallai Inji Dr. Turaki. Ya san zurfin cikin Ma arouf din bazai barshi ya zurfafa zancen ba, haka Allah ya halicce shi, amma jikinsa ya bashi akwai wata a kasa. Ya kyale zancen shima ya bashi amsa. insha Allahu gobe. Yau tana off. Sannan sai ka dan tsahirta ta rubuta (leave without pay) that s in har ta amince kenan. Zanyi kokari a bata (leave) din don ba kowa ake baiwa ba. In kuma bata amince ba sai mu nemi wata.... no please. Ita kadai na aminta da. Idan bata amince ba I will find another solution Jikina yana bani zata amince saboda tana ganin girma na kuma bata yi auren fari ba Da wannan suka kawo karshen tattaunawar tasu. **** Dr. Amina Mas ud tana (ward round ) ranar Litinin da safe aka aiko wata nos ta gaya mata Dr. Turaki na kiranta in ta gama abinda take yi. Ta amsa da a zuciyarta tana fadin this is not his habit (wannan ba dabi ar sa bace) kebewa da mata, ko kiran likita yana tsakiyar aiki. It must be important. Kwana biyu basu zo aiki ba saboda election (zabe), bayan zabe kuma taje kauye gaida Baffanninta ta kwana biyu, don haka yau tanada aiki da yawa zai shiga lokacinta gaskiya. Ta cigaba da zagaya marassa lafiyarta daya bayan daya tana rubutu a files dinsu bayan ta yi musu tambayoyi har ta gama. Sannan ta nufi ofishin consultant din nasu. Da sallama ta bude kofar ya amsa sannan ta shiga, have a seat please Dr. Amina Ta zauna, sannan ta gaisheshi. Ya amsa cikin sakin fuska sannan ya dora bayani. Nasan kinsan Engnr. Ma arouf Ji-qas ko? Ba sai na gabatar dashi a gareki ba? Na fara sanin shi a bakin Yayana Ilya, na sanshi a kafafen yada labarai tun yana dan majalisa, na kara sanin shi shekaranjiya waccan as the elected governor (matsayin wanda ya lashe kujerar Gwamna). Ka ga kuwa na san shi da yawa. Har kuri a saida Ilya ya tattagemu muka je muka sa masa nida Goggona. An shaideshi da cewa mutumin kirki ne. That s all I know about him. Bayan wannan bansan komai da ya dangance shi ba Da kyau. Kin taba sanin yana da (paralysed daughter) mai shekaru biyar? gaskiya bansani ba. I know nothing concerning his personal life (bansan komai na kebantacciyar rayuwarsa ba. Maybe Ilya ya sani, sabida shige-shigensa da bin kwakkwafinsa a kansa Usman Turaki yayi murmushi. To shine yake neman wani taimako daga gareki.... kodayake ta wani fannin baza a kirashi taimako ba tunda aikinki ne ya gaji hakan, kuma abu ne da ba kyauta zaki yi shi ba. You are on your proffession. Yana so ki koma gidansa da zama ki cigaba da bawa yarinyar sa (treatment) da asibiti ke bata zuwa shekara daya mu ga abinda Allah zai yi. Kinsan dai yadda (paralysis) yake ba abu ne da za a ce ga ranar tashi ba tunda bashi da kayyadadden lokaci. Yayi alkawarin ninka miki albashin da kike karba daga gwamnati sau hudu a kowanne wata. Duk (weekend) zaki tafi gida ki dawo Monday. Na yarda da kwarewar ki akan aikinki da sadaukarwa. Shiyasa na zabo ki cikin dubu. A ganina wannan wata hanyar samun alkhairi ce mai dimbin yawa gareki da iyayen ki. Amma zamu baki gajeren lokaci kiyi tunani ki kuma nemi amincewar iyayenki daga yau zuwa gobe saboda hakan ya bukata, yaya kika gani? Amina ta nisa. Tunda ya fara magana bata katse shi ba. Ba rayuwa a government house ne abinda ya dadata da kasa ba a ah, kudin nan da za a ninninka a bata wadanda in a asibiti ne sai tayi shekaru tana Tarawa, ba kuma amfanin kanta zatayi dasu ba, burin data dade dashi akan Goggonta zata cika dasu ta huta tarin data soma tun fara aikinta mai bata lokaci da cin rai, har yau kuma bata tara kwatan abinda take son tarawa ba tunda ba wani dadewa tayi da fara aikin ba, gaskiya ilmi mai zurfi yayi a rayuwa don har abada bazaka daina cin moriyarsa ba. Allah yasa Goggon ta amince. ****** Amina da Goggonta, tareda Inna Zulai Babar Ilya kuma aminiyar Goggon, da Goggo ta kirawo don ta taya ta jin wannan almara ko kuwa rashin kan-gado da Amina tazo mata da shi. In banda rashin kan-gado irin naki Amina, ina hankali na zai kwanta kina kwance wani muhalli daban da nawa, alhalin nasan ban yi miki aure ba? Goggo ta fada cike da damuwa, muryarta a sanyaye. Inna Zulai ta ce Dama ace aurenki zai yi ne don ki kula da diyar da ya fi armashin ji Amina ta jefawa Inna Zulai harara ta gefen ido, ganin tana tufksa tana kara warware mata. Amina ta gyara zama. Goggo akan aikina nake. Mune proffessionals din da ake hiring har gida mu kula da mai lalurar shanyewar barin jiki if a person can afford (idan mutum zai iya biya). Sannan ban bar aikina na gwamnati ba za a bada aro na na shekara daya ne in daina karbar albashin gwamnati in karbi na wadanda suka haye ni. Ki kwantar da hankalinki Goggo duk karshen sati zan taho gida in koma Lahadi da yamma. Sannan fa akwai matar aure a gidan. Kuma Goggo gidan gwamnati ya wuce duk yadda kike tsammani. Girmansa da fadinsa in ba kai ka nemi mutum ba ba abinda zai hada ku. Albashina za a ninka sau hudu Goggo bada jimawa ba Allah zai cika min burin dana ke dashi akan ki. Ki barni nayi aikina Goggo in har kin yarda akan-kanki cewa kin bani tarbiyyya
Chapter 2 · 0% Book details