← Book details Sanadin Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 17

Sashe 6

Sanadin Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba shi da lafiya Cikin tausayawa Ustaz ya ce, Allah sarki, me ke damunsa? An ce wai ya samu (stroke). Amma yana samun sauki Allah ya kara wa Baba lafiya, ki dinga karanta fatiha kafa bakwai a ruwa, ki karanta suratu Yaseen ita ma kafa bakwai, ki ba shi ya sha, a kuma shafe masa jikinsa, insha Allahu zai kara samun sauki Amina ta ce, Zan yi insha Allahu Ya dube ta na yan sakanni, sannan ya ce. Ni da har na ba da sunanki matsayin wadda za ta wakilci jihar Bauchi a International competition a kasar Masar, ban san halin da ki ke ciki ba ke nan Amina cikin girgiza kai, Ba zan iya zuwa ba Ustaz, don Allah ka cire sunana, ban sani ba ko nan gaba, idan na ga Babana na takawa da kafafunsa Ustaz ya jinjina kai, ko nawa ne yan da suka damu da iyayensu haka irin AMINA? Yana rokon Allah ya ba shi ya mata masu albarka irin Aminatu, domin an ce akasarin ya mata masu jin kan iyaye ne. Zo ki tafi Aminatu, kada ki manta da addu ar da na gaya miki, Allah ya kara masa lafiya, ya albarkaci rayuwarki Ta kuwa suri jakarta ta fito, da ta tabbatar ta yi wa Ustaz nisa, sai ta kwasa da gudu. Ustaz ya girgiza kai domin yana kallonta. To haka a boko ma, kullum cikin makara ta ke, a yi ta yi mata bulala da horon da ake yi wa yan makara, amma ba ta damuwa. Don ba ta fita sai ta tabbatar ta gama komai na ayyukan gidan, tun asuba in ta tashi ba ta komawa za ta share gidansu tsaf! Da ganyayyakin bishiyar umbrella ke batawa; ta share dakunan Goggo da na Baba, ta yi wanke-wanke, ta dora sanwa, ta dama musu koko, ko kunu, ta yi musu dumame na abin da aka ci daren jiya. Sannan ta yi wanka ta yi shirin makaranta a iya shekarunta goma sha biyu. Haka Goggo za ta yi ta saka mata albarka don ko ta ce ta bar mata in ta gama hidimar babanta za ta yi, Amina ba bari za ta yi ba. A zuciyarta cewa ta ke, Don wa nake karatun? Ai don in tallafi rayuwarku ne watarana, to kuma Baba ba shi da lafiya, in na rasa shi ko ke Goggo me ye amfanin karatun nawa? A shekarar Amina ta shiga karamar sakandire, da kyar da sudin goshi, domin duk abin da suke samu a sana ar Goggo a maganin Babansu da abin da za su sanya a bakin salati yake karewa, an tattaro Tantabarun babanta na kasuwa an jibge musu a gida, ita ke kula da su. Wani zubin sai ta zauna tana mamakin Kawu Sule, tunda ya yi kudi ko gaida Yayan nasa da jiki ya daina, matarsa Atika ita ma halinsu daya, daga su sai yansu uku suke rayuwarsu, ya manta da nakasasshen dan uwansa, wanda shi da ya samu nasa rufkin asirin sai ya dauko shi ya kawo maraya, ya yi masa silar tsayawa da kafafunsa. Ko takardar magani aka ba su a asibiti in magungunan masu tsada ne ta kai masa, ya soma lissafo mata matsalolin da suke ciki ke nan shi da nasa iyalin, dole suka hakura suka daina kai masa. Tana aji biyu na sakandire, mai yanke buri da soyayya ta yanke tsakaninta da mahaifinta. An ce idan ajali ya yi kira babu makawa sai an tafi, wannan haka ne, amma mutuwar Malam Mas ud rashin kulawa da rashin magani, ko gashin kashi da ake masa gagara ya yi, ta abin da za su ci kawai suke. Goggo sai dai ta tayar da shi ta ba shi abinci, ta kwantar. In ya yi lalura ta tsaftace shi, hannun ma da kafa da suka soma warkewa bayan barinsu gadon asibiti daina motsin suka yi saboda rashin magani da (contineous treatment). Allah ya jiqan Malam Mas Misalta halin da Amina ta shiga na rashin mahaifinta ba zai fadu ba, kwananta bakwai tana zazzabi mai tsanani, Goggo ta dage da yi mata addu a ba dare ba rana, kada rashin ya yi mata yawa, ba ta da kowa a Nigeria sai su, domin tuni iyayenta suka koma kasarsu Sirrleone. Da taimakon Allah Amina ta samu, amma fa da kullaci a ranta na kanin Babanta Alhaji Sulaiman, da kawun mahaifinta Malam Bilya, wanda ko gaisuwa bai zo musu ba, a cewarsa ba ruwansa da bakin haure, Mas udu lokaci ya yi ko daga can inda yake ya yi masa addu a Allah zai karba. Kafin rasuwar mahaifinta ne Allah ya hada Goggo da maraya Ilya, sun yi zaman mutunci da iyayensa kafin Allah ya dau ran mahaifinsa, har yanzu kuma mahaifiyarsa Zulai suna mutunci da Goggon, shi ya ba ta shawarar ta kara wata sana ar bayan itace da kananzir tunda yanzu lokacin zafi ne kuma tana da freezer katuwa, shi zai rinka kai mata makarantu. Ta shiga wani shiri na koyon sana i da gwamnatin Bauchi ta shirya karkarshin ma aikatar ci gaban mata, tsawon wata guda aka ba su jari mai tsoka, da shi ta sayi freezer din, ta kuma ja jarin zobo da kunun ayarta masu shegen dadi da tsafta. Duk unguwar ma a wajenta ake saye bayan makarantu da ake kai wa da sauran wuraren hadaka na mutane, Ilya ya samu taimakon wasu yaran guda biyu inda suke raba kafa. A gefe kuma sana ar itace da kananzir ita ma tana nan. Dakin soro wanda Sule ya zauna a nan Ilyan Goggo (kamar yadda Amina ke kiransa), nan Goggo ta bar masa yake kwana domin ta yarda da hankali da amanarsa. Wani lokacin Amina in suna tadi da Goggonta ta kan ce, Goggo da fa a ce ni likita ce, kuma na karanci lalurar Babana, da fa yanzu bai mutu a gida cikin ciwo ba, zan dinga samun albashi in sai masa magani, in kuma dinga duba shi da kaina Goggo kan ce, Kul Amina! Kada ki yi sabo, kullu nafsin za ikatul maut, in sa i ya yi dole sai an tafi, likita bai isa komai ba Amina kan ce, Haka ne Goggo, amma insha Allah zan yi karatu mai zurfi Goggo, zan karanci lalurar da Babana ya yi domin jinyarta sai mai hakuri, imani, juriya da sadaukarwa. Idan na tuna yadda kullum Baba ke sa miki albarka, da roka miki aljannah, sai bakin cikina ya ragu domin hakika kin rabauta. Goggo za ki taimaka min in yi karatun? Ba za ki ce aure za ki yi min ba? Goggo ta yi murmushi, Karatu ai ba ya hana aure Amina, sai dai ki ce sai in mijin bai zo ba, in kuma ya zo to za mu yi sharadi ko da gaban alkali ne, zai barki ki ci gaba Amina kan zumburo baki, Ba sai na kula su ba balle su zo din? A zuciyarta ta ke fadin hakan, don a dabi arta ba ta ja-in-ja da Goggon nata. In ta fadi abu wanda bai yi mata ba shiru ta ke yi, hatta Goggon ta gane hakan. Amina an gama aji uku na karamar sakandire suna jiran fitowar sakamako, (double promotion) aka yi mata saboda kokarinta, ta zana (placement) tana shekara sha uku. Jarrabawar ta fito, ta ci makarantar yammata ta gwamnatin tarayya da ke Bajoga (Gombe). Amina ba ta samu tafiya makaranta a shekarar ba, saboda ana kashe kudi matuka ba kamar ta gwamnatin jiha inda ta yi ba. Ita ba ta ma san ya akai aka tura Amina wannan makarantar ba, maimakon ta gwamnatin jiha inda ta ke, wannan kuma kokari ne da Malaman Amina suka yi don a cewarsu ba a barin masu (Extraordinary talent) irin Amina su yi ta bata lokaci a kan karatu. Goggo ta daure ta kai ta can din, in har tana da hali. Goggo da Ilyanta suka zauna suna shawara, Goggo ta ce, Ka gani fa Ilya, ni fa tarin aure nake mata in na ce wannan makarantar mai tsada zan kai ta me za mu tara? Ga shi da alama ita ma ta makala zuciyarta a kan makarantar Ilya ya ce, Goggo hakura da tarin auren ki ba ta ilmi, ba abin da ilmin da za ta yi ba zai saya mata ba na auren, ki bar maganar auren a hannun Allah. Ko da mun san Kawu Sule ba zai yi ba, ni na gaya miki Allah zai kawo wata hanyar daban. Sannan ga wata shawara, dazu wani abokina yana da kanti a cikin jami ar Tafawa Balewa ya gaya min in shawarce ki, ko za ki iya a dinga yin cincin mai nama (meat pie) da kek (cake) mai kyau mu dinga kai wa joints na cikin jami a, kunun Aya da zobo a dinga durawa a tsaftacciyar robar lemuka, in har za a jura wallahi akwai samu sosai. Shi zai rarraba musu in na kai, da an siyar in karbo kudin Goggo ta ce, Ga shi Amina makarantar kwana za ta tafi balle in samu mai taimaka min Ilya ya ce, Mai aiki za mu dauka babba, ni ma zan shiga cikin aikin, kuma in mun yi mai yawa ba kullum za mu yi ba sai bayan kamar kwana uku-uku in an karbi kudin wanda aka sayar Goggo ta ce, To ka gaya wa Zulai, (tana nufin mahaifiyarsa) ta cigita mana mai aikin Cikin sati daya Zulai babar Ilya ta samo wa Goggo mai aiki, bazawara ce mijinta ya rasu ya barta da yara hudu sunanta Talatu, neman aikin aikatau ta ke ruwa a jallo, suka hadu suka fara aikin tare, har Ilya shi ma ba a barshi a baya ba, in ka ganshi ya takarkare yana murjin (Meat pie) a injin taliya sai ya ba ka dariya, duk don Aminarsu ta samu ta yi karatu mai kyau. Baba Talatu na da dadin sha ani, ga labarai na ban dariya a cikinta, suna aiki tana ba su labarai, Amina na shan dariya, tasu ta zo daya don Amina akwai son jin labarai don haka ba ka raba ta da rediyon Goggo kullum, ta murdo nan ta murdo can, tana jin me duniya ke ciki. Sana ar ta Goggo sai sam-barka, ta fara da hannun dama, ba ta ajiyar kudi a gida, adashi ta
Chapter 6 · 0% Book details