Sashe 15
Sanadin Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A cikin wadannan shekaru Aisha ta goge, ta waye, ta zama cikin wayayyun matan Arewa a Lagos. A Lekki suke da zama. Ta shiga (Unilag) ta yi digirinta a kan (Accountancy) ta yi hidimar kasa a nan Lag ta adana takardunta a karkashin gado don Ma arouf bai yarda da aiki ba, ko da ya barta ita ba ta da ra ayi, burinta kullum ta kula da Ma arouf ta janye idanunsa daga sauran mata masu auren maza don abin hannunsu. Sai kuma ta yi sa a shi Ma arouf din akan karan-kansa ba mai ra ayin aure-aure ba ne. Sannan iyayensa a tsaye suke a kansa wajen yi masa addu a da ba shi (azkar) iri-iri yana yi duk inda zai shiga. To da ma Ubangiji ba ya barinka haka ba tare da ya jarrabe ka ta wani bangaren ba. Hakan ce ta faru da Ma arouf da Aisha, ko batan wata Aisha ba ta kara yi ba, tun wannan barin data yi a cikin jirgi, haihuwa sun neme ta sama ko kasa Allah bai ba su ba. Shekara biyar ke nan da aure. Tebirin likitoci iri-iri a Lagos da Abuja babu inda ba su tsugunna ba. Duk amsar daya ce, dukkaninku lafiyarku kalau, Allah ne bai nufa ba. In suna da damuwa a rayuwarsu, to wannan ce. Har taimakon magungunan Hausa Hajiyan Ji-qas ke kawo wa Aisha, amma shiru, kamar an aiki bawa garinsu. Mr. Timothy wanda da zuciya daya yake kaunar Ma arouf ya zauna yake tunani, shi ga shi shekaru sun tura, ya san kuma yadda dukkan ma aikatansa ke kishi da Ma arouf, idan ya yi (retire) ko ya mutu yanzu Ma arouf zai ga ba daidai ba a Lange & Grant ga yaron ya taimaka masa ya tara dukiyar da shi kansa bai san iyakarta ba cikin shekaru biyar kacal, kuma an ce dadewa a bauta yanci ne, ya kamata ya taimaka masa ya tsaya da kafafunsa. Don haka ya wari wani kaso na dukiyarsa ya tura account din Ma arouf, abin da ya firgita Ma arouf ya zo ganinsa har gida afujajan. Sun kulle kansu a dakin ganawa da bakinsa na musamman, a nan Mr. Timothy ke yi masa bayanin kudurinsa a kansa. Cewa daga yau ya bar Lange & Grant ya zama (contractor) mai zaman kansa, zai buda masa hanyoyin karbar kwangilar gine-gine daga kwastomominsa. Wannan godiya ce a gare shi na wahalta masa da ya yi da zuciya daya har kamfaninsa ya kai matsayin da ya ke da shi a yanzu. Ba shi da abin cewa sai godiya, don ya san halin ogan nasa, ba ya niyyar yin abu ya fasa, amma da ya ce masa zamansa karkashinsa ya fiye masa dadi, kuma (remuneration) din da yake samu a karkashinsa ya ishe shi. He is contented with his life as such... Amma an ce ba a maida hannun kyauta baya. Kuma a yadda ya san abin da Ogan nasa ya mallaka, wannan ba wani big deal ba ne a wajensa (babban abu). Don haka ya dauko Baba da Hajiyan Ji-qas da Alhaji Mansur (surukinsa) suka zo har Lagos suka je suka yi wa Mr. Timothy godiya. Sai ya hau Ma arouf da fada, (how dare ) ya kwaso dattijai haka ya ba su wahala. Ba zai kira shi a waya su yi maganar ba (a lokacin waya ta shigo, amma rike ta sai wane da wane). Shi ma ya sayar da duk kadarorinsa, filaye da gonaki biyu da ya saya a Bauchi, ya hada da capital din da ubangidansa ya ba shi, ya gina kamfanin kwangilar gine-gine mai zaman kansa, kuma da yake ya san kan harkar, idonsa ya riga ya bude da ita. This is the beginning Da wannan JI-QAS CONSTRUCTION COMPANY LTD ya kafu, mai hedikwata a Abuja da Lagos. Ya dauki karantattun ma aikata ya zuba, suka soma karbar kwangilar gina wani (oil-refinery) a jihar Ondo, daga gwamnatin tarayya, da abin ya yi gaba ya dawo gida Bauchi yana karba daga gwamnatin jiha, makarantun firamare ne, gadoji ne, tituna ne, gyaran Dams, hydro-electric power, da sauransu. Allah kuma ya sanya albarka a ciki. arouf in ya zauna yana tunani a kan kansa, yana kididdiga arzikin da ya samu cikin dan lokaci kalilan, sai ya ga ya kamata ya soma wani tallafi ga matasan jihar Bauchi, wadanda ke zaman banza, da wadanda ke da zuciyar neman ilimi babu damar yi, wadanda suka yi karatu babu aikin yi, da ilimin yara kanana a jiharsa Bauchi ganin yadda gwamnati ta yi wasarere da su saboda abin ya yi mata yawa ita kanta gwamnatin, hakkin masu hannu da shuni ne su sanya hannu a gudu tare don ci gaban al umma, amma fa masu zuciyar taimakon kadai. Ya fiddo da wani tsari na gina matasa mai suna (Ma arouf Foundation), ya sa aka rika cigiyar matasa a kafofin yada sadarwa masu matsalolin can da ya ambata a baya. Matasan Bauchi da iyayen yara talakawa suka amsa kiransa da gaggawa, ya dora ma aikata masu amana, aka soma yi wa matasan maganin matsalolinsu daga cibiyar MA AROUF FOUNDATION. Ya gina katuwar makarantar firamare ta kyauta, wadda gwamnati ta san da zamanta. Allah kadai ya san adadin matasan da suka samu kwalin digiri daga aljihun Ma arouf a jihar Bauchi. Su gama ya yi musu hanyar samun aiki daga gwamnati ko (private sectors), ilmin firamare mai kyau (free) ga kananan yara, masu zaman banza an sanya su (6-week orientation) sun koyi sana i ana ba su wadataccen jari. Sai a hankali sunan Ji-qas ya fita a Bauchi har ake masa kallon wani babban dan siyasa ne. Har zuwa yanzu (foundation) din na ci gaba da gudana. Wannan ne ya janyo ra ayin matasan Bauchi na son ya tsaya musu takarar gwamna na kara yaduwa. Sun yi gangami sun bayyana masa ra ayinsu na son ya shiga siyasar ya taimaka wa jiharsa, su kuma za su tsaya wajen yi masa kamfen babu ko sisinsa. A lokutta da dama hakan ta faru babu wanda ya samu gamsasshiyar amsa daga bakinsa. Daga baya jama ar suka bi ta kan surukinsa wanda an san ba ya ketare shawarwarinsa a gare shi. Sun zauna ya yi masa nasiha, cewa ya rungumi alherin da mutane suke so da shi, ya tsaya takarar ya barsu da kokarin komai na Allah ne. Mahaifinsa kuwa addu ar da ba ya fasa yi masa kullum ita ya yi masa, yana fadin, Allah ya yi jagora, Allah ya zaba mafi alkhairi Hajiyan Ji-kas, kusan ra ayinsu daya da Baba, cewa ta yi idan siyasar alkhairi ce Allah ya yi riko da hannunka Aisha ce kadai ba ta son zancen siyasar nan. A cewarta yanzu haka sai in dau lokaci ban sa ka a idanuna ba, kana nan kana can, ina kuma ga ka shiga siyasa? Ina kuma ga ka zama gwamna? Ita ma ba ya ba ta amsa, murmushi kawai yake yi. Yau da gobe ba ta bar komai ba, kwadaita masa siyasar da kowa ke yi da goyon bayan da ya samu daga sama da kasa ya sa ya amince, ya shiga siyasa karkashin jam iyyar (NPC) wato Northern People Congress . Bai tsaya takarar gwamna ba, ta dan majalisa ya tsaya mai wakiltar Bauchi ta Kudu don ya kara bude ido da yadda al amuran siyasa ke tafiya. Ai kuwa da gudu ya haye, suka koma Abuja shi da iyalinsa. Su Baba kan je, Hajiyan Ji-kas kan je ta yi hutu duk sanda ta so, su ma kuma suna zuwa ganinsu akai-akai. Ashe da kafar dama suka fada siyasar, domin a shekarar ne ciki ya billo a jikin Aisha. Murna da godiyar Allah gurin ma auratan da iyayensu da duk wani mai kaunarsu abin ba a cewa komai. Sai shukrah ga Lillahi. *** *** *** Aisha ta sauka lafiya a National Hospital ta samu yarta mace, santaleliya mai kama da ubanta a komai. Ranar suna Baba ya sanya mata suna Amina. A cewarsa babu sunan da ya kai wannan albarka (Aminatu mamar Manzo) haka yake kiranta. Amina ta taso cikin gata da soyayyar iyaye da kakanni. Hajiyar Ji-qas Abuja ta dawo kacokam tana musu jego, yanzu kam Aisha ta dade da zama tauraruwa a cikin yan uwanta, kowa nan-nan yake da ita saboda ita Allah ya rufa wa asiri fiye da su. Ba ta ki su ba, kuma ba ta hana su rabar arzikin da Allah ya yi mata ba. Dogon hannu gare ta, kullum cikin mikawa kowa abin alheri ta ke. Don albashi gare ta mai zaman kansa cikin (account) dinta, duk wata Ma arouf ke zuba mata, ba ruwansa da me za ta yi da shi. Yanzu shekarun Amina hudu ke nan a duniya, ta dade da shiga makaranta. Ma arouf (tenure) dinsu ta kusa cika, sun yi nisa da yawon kamfen da shirye-shiryen zabe mai zuwa ba da jimawa ba. Shi ne dan takarar da jam iyyarsu ke tinkaho da shi, kuma dan takara mafi rinjayen magoya baya. *** *** *** Jirgin gab yake da sauka a filin jirgin zaman Abuja, idanunsa a lumshe, fuskarsa rufe cikin hular kansa, kan nan sumul ya sha saisaye irin na su na masu madafun iko. Za ka yi tsammanin tunda ya zauna cikin jirgin bacci yake yi, sai yanzu da aka ce ya yi fasten belt jirgi zai sauka. Ba bacci yake ba (flash back) ne na gwagwarmayar rayuwarsa ya gilma masa. Ya ja dogon numfashi ya sauke. A hankali ya bude idonsa, ya cire hular daga fuskarsa ya mayar da ita mazauninta. Ya mike ya fito daga cikin jirgin inda dumbin jama arsa ke jiran fitowarsa. Daya bayan daya yake mika wa jama arsa hannu suna musabaha, kamin su dunguma su shiga motocin da suka zo a cikinsu. Motar sakatarensa Idris ya shiga suka shiga cikin birnin Abuja, sai da suka kai shi har gida sannan suka juya. Gidansa na Abuja a ne. Tuni kukun gidan ya kammala komai na abincin rana a tebirin cin abincin falon ya gaida ogan ya fita. Sallah ya fara yi, sannan ya ciro wayarsa daga cajin da ya sanya ta. Cike da mamakin me ya sa Aisha ba ta kira shi ba, in shi jama a da rashin cajin waya sun hana shi kiranta. Kunna wayar