← Book details Sanadin Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 17

Sashe 5

Sanadin Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ka barshi haka Malam Hadi ya ce, Shi ke nan Masa udu, Allah ya kawo kasuwa mai albarka Masa udu ya ce, Amin Hauwa ta rusuna ta ce, Na gode Kai ya daga mata, Babanta ya wuce gaba, ta bi shi a baya. Masa udu tun ganinsa da Hauwa ya kasa sukuni, kwana uku bayan nan ban da tunaninta ba abin da yake yi, daga baya ya gane kaunar Hauwa u ce ta shige shi farat daya. Ya kuma yanke shawarar kai kukansa ga mahaifinta ko da ba zai ba shi ba a kalla ya samu sukuni cikin zuciyarsa. Washegari ya tadda Malam Hadi a nasa kejin, ya sunkuyar da kai, Malam Hadi ya ce, Ya aka yi ne Mas udu? Mun gaisa ka yi shiru bayan da ganin bakin nan naka akwai motsi a cikinsa ud ya muskuta ya daure ya ce. So nake ka ba ni izinin shiga cikin maneman Hauwa u Malam, in har ba an yi mata miji ba Malam Hadi ya yi murmushi, a ransa ya ce, Na san za a yi haka . A fili kuma ya ce, Ka zo sau uku ku shirya, in ta amince ni da ma a shirye nake da in aurar da ita Zuwan Mas udu biyu wajen Hauwa suka shirya kansu. Ya tattara ya tafi Shira don turo danginsa. Iyayensa sun dade da rasuwa, sai kannen Babansa guda biyu Malam Bilya, da Malam Tasi u. sai kaninsa Sulaiman wanda a lokacin yaro ne. Ko da ya kai maganar ga kawunsa Bilya sai cewa ya yi, Ni nan ai na riga na yi maka mata, kanwarka Talle. Jira nake ka zo da ma in yi maka zancen Masa udu ya ce, Ba zan iya auren zumunci ba Kawu, don Allah ka amshi zancen Hauwa u, ita ma iyayenta mutanen kirki ne Malam Bilya ya danne bacin ransa na kin amsar yarsa da Masa udu ya yi, ya ce zai zo marayar ya sauka gidan amininsa ya yi bincike a kan yarinyar da iyayenta, kafin ya yarda ya shige masa gaba kan aurenta. Ya je ya dawo bayan sati daya. Masa udu ya kasa barin satin ya cika, kwana shida ya yi ya dawo Shira wajen kawunsa, sai da ya gama sha masa kamshi sannan suka zauna. Na gama bincike na tare da aminina Malam Dahiru, abin ikon Allah ma makota suke da iyayen yarinyar da ka ke nema din. Bincike ya nuna iyayenta bakin haure ne daga can wata kasa da ban taba ji ba wai Saliyo. Don haka ni ba zan shige maka gaba kan auren wadda ban san asalinta ba. In ba za ka auri kanwarka ba, to ka nemo wata yar asali amma ba na cikin auren bakin haure Masa udu bai hakura ba, sai ya koma kan daya kawun nasa Tasi u, don shi kam mai ilimin addini ne, limami ne guda a shiyyarsu, shi kam ya karbi maganar da muhimmanci, da ya yi nasa binciken ya nuna ban da kasancewarsu baki iyayenta mutanen kirki ne da aka yi musu kyakkyawar shaida, yarinya kuma ta samu tarbiyya da ilmin addinin islama har alqur ani ta sauke. Don haka shi ya shige wa Mas ud gaba ya auri Hauwa, ya sayar da gonarsa ya saya musu gida a nan inda suke zaune har yau. A lokacin duniya na kwance sayen gida ba tashin hankali ba ne. gidansu yana nan a unguwar Gwallaga, wanda suke raye har yau a ciki. Sana i iri-iri Hauwa ta yi don ta taimaki kanta da mijinta. Sun dade Allah bai ba su haihuwa ba, sai da suka shekara goma da aure, sannan Allah ya ba su Amina. Lokacin da Masa udu ya yi karfi a kan sana arsa sai ya dauko kaninsa Sule daga Shira ya nuna masa sana ar Gwanjo, ya sai masa dealer , ya fasa yana sayarwa da dai-daya, cikin sa a sana ar ta karbe shi, har dai da ya yi wani ubangida da ke ba su (dealer) su fasa su sayar su kawo mishi uwar kudi su rike riba. Ya ba shi daki a nan zauren gidansa suke zaune tare, kasancewar iyayensu su biyu rak suka haifa, Kawu Bilya da Kawu Tasi u duk uba suka hada, shi ya sa sau da yawa idan Hauwa na nuna damuwarta a kan rashin haihuwa ya kan ce, ni kam ba na damuwa, watakila rashin haihuwa a cikin jinina yake, don duk zuriyar su mahaifiyata daga mai Da daya sai mai biyu. Da Sule ya yi karfi a sana ar gwanjo ya yi gidan kansa, ya auri yar ubangidansa Atika, sannan ne ya bar gidan Yayansa Mas udu Baban Amina, domin zuwa lokacin ya fi Yayan nasa samun nasibi don Alhajinsu na ji da shi, har dai da ya auri Atika, shi ma ya sakar masa harkar sosai, har Turai yake zuwa ya shigo musu da kaya. Amina, ta taso yarinya mai hazaka da son karatu, ga naci a kan abin da aka koya mata, har sai ta ga ya zauna a cikin kanta. Ga son iyaye da son kyautata musu. Tun tana shekara shida ba ta barin Goggonta da ayyukan gida, ko dai a bar mata tayi, ko ta sa hannu su yi tare. Albarka kullum shanta ta ke daga bakin uwa da ubanta tun tana kankanuwa, shi ya sa ta taso yarinya mai matukar nutsuwa da wadatar hankali. Amina ba ta da aboki sai littattafanta da alqur ani. A zuwa makaranta Amina ba ta san latti ba, daga islamiyya har boko, kullum ita ke daukar tsintsiya ta share ajinsu na islamiyya dana boko saboda tana riga kowa zuwa. Amina na da shekaru goma sha biyu mahaifinta Mas udu ya gamu da lalurar shanyewar barin jiki, sun tashi lafiya sun wuni lafiya, da yamma ya dawo daga kasuwa suka taba hira a tsakar gida da iyalinsa. Ana gab da kiran sallar magriba ya mike. Yar albarka zuba min ruwa a buta ki gani in yi maza ko na samu jam Amina ta ce, Baba, ai tun dazu na zuba maka Ya kai hannu ya daga butar, Haka kuwa, Uwata Allah ya kara albarka Murmushi Amina ta yi. Yana shiga ita da Goggo suka mike don gabatar da tasu alwalar, sai ji suka yi timmm! Ya yanke jiki ya fadi cikin bandakin. Da gudu suka danna kai a bandakin daga uwar har yar, ba tare da tunanin halin da za su riske shi a ciki ba. Hauwa na kokarin taimaka masa ya mike, ta kasa don idanunsa sun kakkafe, bakinsa ya gicciye. Amina sai kuka, Goggo ta ce. Maza kirawo Ilya Ta kwasa da gudu domin kiran Ilya a dakin soro. Ilya ne ya samo taxi suka taitayi Malam Mas udu, suka sanya shi suka nufi Specialist Hospital Bacas. Duk wasu shige da ficen shi ya yi har likitoci suka karbe shi. Abin da suka gaya wa iyalinsa bayan sun dudduba shi, ya yi matukar daga musu hankali. Cewa Mas udu ya gamu da lalurar shanyewar barin jiki, (sudden stroke) don haka sun ba su gado, za a ci gaba da ba shi kulawa da taimakon gaggawa. Aka danka wa Ilya (bill) na allurai da magunguna da ake bukata, ya je gidan Kawu Sule ya kai masa, ba da son ransa ba ya kawo kudin ya bayar amma bai je asibitin ba yace da Ilya ya gaya musu tafiya ta kama shi Allah ya kara sauki. Ilya ya kawo ya biya komai harda na aljihunsa ya kara aka ci gaba da ba shi kulawa. Satinsu uku a asibitin ya ji sauki, aka ba su sallama. Yana iya motsa hannunsa da kafarsa, amma ba ya iya yin komai da su. A gida jinyarsa ta koma hannun Goggo, domin Sule ko dubiya bai zo ba bai kuma kara tallafa musu da komai ba tun bayan wancan taimakon da yayi na sayen abinda ake bukata a asibiti lokacin da abin ya faru. Sai ya zamana Amina tun tana shekaru goma sha biyu ita ke dafa abin da za su ci a gidan, ta tsaftace ko ina ta kula da sana ar Goggo ta kalanzir da sayar da itace da ta ke yi a lokacin. Har ya zamanto tana makara a zuwa makaranta, sannan ba ta da nutsuwa kwata-kwata, tana tunanin halin da za ta koma ta riski Babanta a ciki, malamanta kansu sun fahimci hazika Amina Mas ud ta canza. Da ko an tashi makaranta Amina ba ta gaggawar tafiya gida sai ta kammala rubuce-rubucenta, in aikin gida ne (homework) sai ta kammala shi a lokacin sannan ta tafi gida. Amma yanzu ana kada kararrawa Amina ce farkon fita daga aji cikin sassarfa, wani lokacin ma da gudu ta ke fita. Ranar wata lahadi a islamiyyarsu inda suke yin Tahfiz daga karfe takwas na safe zuwa azahar wani malaminsu Ustaz Abdulsalam wanda Allah ya daurawa kaunar Amina (ba kauna ta soyayya ba), bayan ta bada haddarta ya daga kai ya dube ta tana harhada takardunta don komawa gida ba tare da an yi addu ar tashi ba. Ya ce, Amina Mas ud, zauna ki jira ni in gama da yan uwanki, akwai maganar da za mu yi Ba da son ranta ba Amina ta koma bencinta ta zauna tana ta sake-sake cikin ranta, Ban daura abincin rana ba, na san yanzu daga Goggo har Baba sun dawo daga asibiti ba su samu na dafa komai ba Sai hawaye sharr-sharr. Ustaz na lura da Amina, kawai sai ya ji zuciyarsa ta karye, ya fahimci tsayar da ita din da ya yi ne ya sa ta kuka. Shi kuma so yake ya ji me ta ke yi wa sauri haka da har ya shafi hazakarta a kan karatu? Tana daga cikin daliban da ya sanya sunansu za su halarci gasar karatun alqur ani mai tsarki ta duniya (International competition of Holy Qur an) wadda za a yi a kasar Misra wannan shekarar. Bai nuna ya ga tana kuka ba, har ya gama da dalibansa uku da suka rage masa. Ya isa har gaban bencinta ya ce, Aminatu Mas Ta dago jajayen idanunta ta dube shi, a zuciyarsa ya ce, Subhanallahi Ahsanul Khaliqeen . A fili kuma ya ce, Me ke damunki ne a yan watannin nan? Ta share hawaye da bayan hannunta, Babana ne
Chapter 5 · 0% Book details