Sashe 17
Sanadin Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
soma dawowa hayyacinsa. Sun fita (campaign) garuruwan Ganjuwa, Itas, Katagum, Misau, Toro, Ningi, Darazo, Jama are, Warji, Dass, Tafawa Balewa cikin kwana bakwai. Inda duk tawagar Ma arouf ta gifta masoya ne ke kwararowa ta inda shi kansa bai sani ba. Sai dai kuma rade-radi ya soma yawo, ai ba shi da aure, ta ya ya zai zama gwamna babu iyali? Wannan rade-radi ya zo kunnen Hajiyar Ji-qas domin an ce ita magana tafiya ta ke da kafafunta. Dawowarsu ke nan daga garin Jama are ya zarto asibiti wajen su Hajiya. Yana tare da Amina har tsayin rabin awa. Kallo daya Hajiya ta yi masa ta karanto matsananciyar yunwa a tare da shi. Ta jawo sundukan abinci na alfarma da ke gefe ta zuba masa masah mai taushi da dadin gani a ido da baki tasa miyar ganye akai ta jawo tebir ta daura masa akai. A gefe lemon tuffah ne na kwali ta aje da kofi, Kyale Ameena, sakko ka ci ka gama magana za mu yi A duk sanda ya ga Hajiya cikin wannan yanayin maganar da za ta yi mai muhimmanci ce. Ya bi umarninta. Cikin dadin rai ya soma cin abincin don kuwa ya manta rabonsa da abinci mai dandanon gishiri cikin kwanaki biyun nan, sai (caffinated drinks) da (snacks) da yakan ci in ya samu dan lokaci. Sosai ya ci masar, har da yi wa Hajiya godiya, lemon kwali guda haka ya shanye shi. Ya tattara hankalinsa ya mika wa Hajiya don ya fuskanci hakan ta ke so. Ita ma nata hankalin ta bashi. Kana sane da cewa ka tsaya siyasa ba ka da iyali? Da sauri ya dago ya dubi Hajiya. Ita kuwa ta tsare shi da idon. Ba ka da iyali ta ya ya za ka shugabanci al umma alhalin kai kanka ba ka da abin shugabanta? Ya bude baki zai yi magana ya kasa, to me zai ce? Ya manta da wannan shaf! Kuma a da bai dauke shi da muhimmanci ba tunda ya san yana da su, Allah ne ya yi hukuncinsa, yanzu ya tuna wannan (decree) ne mai zaman kansa a sharuddan shugabanci. Hajiya ta gaji da shirunsa, Ba ka ce komai ba Da kyar ya hadiye miyau ya kalato sauti. To Hajiya ni me zan ce? Me za ka ce? To gaya min ta ya ya za a ba ka shugabancin? Ya dan kifta ido, don shi ma yanzu ya kwadaita da siyasar, don ita da ma haka ta ke, wuyarta ka dandanata sau daya. Yana kuma tuna wahalar da ya ke ta yi a kai shekaru biyu ke nan a ce ya bari don ba shi da aure? Auren wata wahala ne da shi? Ba kamar siya ake a kasuwa ba? Hajiya shirunsa ya fara bata haushi, Ka kyale ni ina ta magana, in ba ka yarda da abin da na ce ba ne ka tashi ka yi tafiyarka, zan tada sallah Ya dan muskuta ya gyara zama. To Hajiya gani na yi abin ya yi kusa. Kwata-kwata yau kwanan Aisha arba in da biyu da rasuwa, kawai kuma a ji na yi aure kamar dama jira nake ta kauce in yi aure? Hajiya ta girgiza kai. Wannan ne daidai lokacin da Manzo (S.A.W) ya umarce ka da ka yi auren. Ba don kana neman kai da Aisha ba, sai don cikar mutuncinka da kamala a wurin Ubangiji da idon al umma Ya zuki iska ya fesar, cikin kankanuwar murya kamar ba tashi ba. Na amince Hajiya ki yi duk abin da ya dace. Nawa zan bayar? Hajiya abin ya ba ta dariya, ta lura ya dauki auren kawai matsayin wani abu da za a sa kudi a sayo a kasuwa, a duk sanda ake so. Sai ta biye masa. Naira ishirin ya isa Ya dube ta da sauri, don shi da zuciyarsa daya ya tambaye ta, sai kuma ta jefe shi da gatse. Ta kalle shi cikin ido ita ma. Ka kalle ni mana tunda ka dauki auren abin siyarwa Ki yi hakuri Hajiya Ban yi fushi ba. Ka ba ni kwana uku in je Ji-qas in cigita cikin yan yan uwa ko abokan arziki. Kada gaggawa ta sa mu yi aikin shaidan Da wannan suka gama tattaunawar tasu ta ranar, ya sumbaci Amina wadda ta yi bacci ya tafi gida. Da hajiya za ta tafi Ji-qas ta ke gayawa likitocin Amina za ta yi tafiya ta kwana uku, wa zai kula da Amina? Saboda ba ta so ta kirawo matan Baban Aisha don ba zumunci na jiki sosai ne tsakaninsu ba, haka ba ta son cewa Baba ya kawo Inna Luba duk da rayuwa ta koya mata hankali yanzu ta zama mutuniyar kirki, ga Babanta yana Abuja ba ta gaya masa lokacin da za ta yi tafiyar ba, don duk muhimmancin abin da ke gabansa haka zai ajiye shi ya ce shi zai zauna da Amina. Dr. Umar Bolori ya ce, Hajiya kada ki damu, akwai (nurses) dinmu da za su kula da ita, mu ma muna tsaye fi-amanallah. Insha Allahu Da wannan Hajiya ta shirya sabon direbansa na Bauchi Akilu ya dauke ta zuwa Ji-kas, hankalinta a kwance don ta san ta baro Amina a kyakkyawan hannu. Gundarin labarin AMINA da Ma arouf yana cikin littafi na biyu. Wannan shimfida ce kawai. Ku kasance tareda Takorinku a littafi na biyu don jin me labarin Amina ya kunsa gabadaya. AMINA-1 SUMAYYA ABDULKADIR SHAPE \* MERGEFORMAT PAGE \* MERGEFORMAT Times New Roman Times New Roman Calibri Calibri Courier New Courier New Wingdings Wingdings Symbol Symbol Arial Black Arial Black Calibri Light Calibri Light Cambria Math Cambria Math !%),.:;>?]} $([{ Light horizontal _GoBack SummaryInformation DocumentSummaryInformation WpsCustomData user Normal.dotm TECNO LD7 1051 WPS Office 16.000 508704f17b59442c92ea4597bb34ceac