Sashe 14
Sanadin Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baba na fi-sauran babanni ne, what an amazing father Allah blessed me with!!! Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya yi mana umarni da mu yi wa iyayenmu biyayya. Ya ga idan bai yi magana ba, zai zama ba namiji ba, su taru su zama matan shi da ita. Hannun damansa ya mika mata yana gayyatarta musabaha. Sunana Ma arouf ina nufin Ma arouf Habibu Ji-qas, cikakken sunan ke nan, ko ya sunan Malamar? Shi kansa ya yi mamakin sautin da ya yi amfani da shi wajen yin wadannan kalaman. Shi ne mafi kankanta da sirantar sauti da Allah ya halicce shi da shi. Kanta ta sanya a tsakanin cinyoyinta tana wani irin murmushi, ta kasa ba shi hannun, har ya gaji ya maida abinsa aljihun farar shaddar da ke jikinsa. To da alama abotar tamu ba za ta yiwu ba, tunda malamar rowar muryarta ta ke min. Bari in koma makaranta, da ma kudin cefane ne na mance ban ajiye ba. Ga su Ya ciro daga aljihunsa ya mika mata. Har yanzu ta kasa dagowa ta karba. Ya karasa gabanta ya ajiye mata, Tattara kayan da ta zubar a tsakar gida ki kai mata, sai dai ina rokonki ba umarni ba, wannan ya zamo mu amala ta karshe da za ta kara shiga tsakaninku Cikin nutsuwa ya juya ya fita, ya koma wajen aikinsa. Hatta dalibansa sun lura yau Malam Ma arouf yana cikin farin ciki. Wata koyarwa yake yi musu cike da nishadi wanda ba su taba gani a tare da shi ba. Ana tashi ba inda ya tsaya sai gida, ya tarar ta gyara tsakar gidan tas ta shige uwardaka ta kure karatun alkur ani mai tsarki a rediyo. Ta turare gidan da turaren wuta mai dadin kamshi. Wanka ya fara yo wa ya yi alwala ya nufi masallaci. Da ya dawo ya tarar ta shirya masa abinci, amma yau ba ta ajiye a kofar daki ba ta shigar masa da shi ciki. Ya yi murmushi, a ransa ya ce, An samu ci gaba ke nan Ya ci abincinsa ya yi kat! Ta iya girki sosai. Yau ba fita kofar gida karatun jarida. Kananan kaya ya sanya, ya fito a gogaggen dan bokonsa. Kansa ba hula, babu tarin suma, kuma bai dade da yin saisaye ba. A very smart guy. Ga turare ya fesa mai dadin kamshi, ya nufi dakin matarsa. Zaune kawai ta ke tana sauraron karatun da ta kunna, da alama bi ta ke a zuciyarta. Jin zuciyarta ta ke kamar an yi mata rahma ga dukkan zunubanta. In ba ta gode wa Allah ba me za ta yi? Ba ta ankara da shigowarsa ba, sai da ya kai hannu ya kashe rediyon. Wani irin shiruu! Ya ziyarci dakin, idonta yana lumshe ne don haka ta bude su don a tunaninta kaset din ya kare ne, suka sake yin arba da juna a karo na biyu. Zama ya yi a kusa da ita har kafadunsu na gugar na juna. Aisha ta samu kanta cikin wani sabon yanayi, ga ba wurin gudu. Sauran abinda ya biyo baya ba zai taba gogewa a tarihin rayuwarsa ba. Kullum yana tunawa, tunanin na kara masa sonta da kaunarta. The first life-partner ever, yet the best! The very best!!! *** *** *** Sun kulle sun dunkule sun zama abu daya, abokan sirrin juna, masoyan juna, kuma yan uwan juna, kasancewar dukkaninsu ba su da wanda za su kira dan uwansu na jini, sai junansu. Aisha na shara a tsakar gida wani yaro ya shigo, Wai ana neman maigidan Ba tare da ta juyo ba ta ce, Ya tafi wajen aiki, sai karfe daya da rabi zai dawo Yaro ya fita, can kuma ya dawo da ambulan mai fadi a hannunsa, Wai ga shi a ajiye masa, sako ne daga post-office . Aisha ta ce, Ta karba ta kai daki ta ajiye a kan talabijin dinta ta fito ta ci gaba da ayyukanta. Da ya dawo ba ta ba shi takardar ba, sai da ya gama komai na al adar rayuwarsa, ta dade da kashe fita kofar gida karatun jarida don a cewarta da haka zai kallo wata tunda kallon masu wucewa yake ba karatun jarida ba. Ya kan ce, Ki yi abin da ki ke so dole a bi, ko ana so ko ba a so Tare suke hirarsu na abubuwan da suka shafe su, ko al ummah. Inna Luba ta dade da shafa mata lafiya. Au! Ka gani na manta, dazu aka kawo maka wai daga (post-office) Ya karba yana juya ambulan din mai dauke da tambarin kamfanin Lange&Grant , ya ciro ya bude yana karantawa. Bai san sanda ya mike tsaye ba, Aisha, alheri zai same mu, kirana ake yi intabiyu. Na dade da neman aikin wajen shekara guda ke nan. Sai dai ga bikin zuwa babu zanin daurawa Ta ce, Kamar ya ya? Eh, toh!. Sai na je Lagos. Ga shi babu kudin mota. Wata ya zo karshe, kuma gobe-gobe ake so in shiga Lagos jibi in shiga intabiyu din Aisha ta mike ta shiga dakinta, ta jawo abu daga kasan gadonta. Sai ganinta ya yi ta fito da bankin kasa, ta tika shi da kasa, sai ga kudi fululu. Da mamaki yake kallonta, Wannan fa? Naka ne Kamar ya ya nawa? To an ce da kai haka ake ba wa iyali kudin cefane kamar ma aikata? Ko an ce maka maigida ba zai dinga adana komai ba a kudin cefane yake karewa? Ko kuwa mu hudu ka ajiye da ka ke ba ni tsabar kudin da ka ke ba ni kullum? Karbi ka shirya ka tafi Shi dai ya kasa magana, sai binta yake da kallon kauna. Ba zan karba ba sai kin yarda rance za ki ba ni Da ta ga zai bata mata lokaci wajen ja-in-ja, ta ce, Na yarda Sannan ne ya soma kirga kudin. Za su kai shi har karshen Nigeria su dawo da shi Bauchi lafiya. A daren ta hada masa kayan da zai bukata, sun shirya da asuba zai fita. Ya yi sallama da Baba tun a daren ranar ya ce suna fitowa daga masallaci zai nufi tasha. Baba ya yi masa addu a sosai. Ya gamu da wahalhalu irin na matafiyi, har Allah ya kai shi garin Ikko lafiya. Ofishin Lange&Grant na nan a 53 Akanbi Onitiri, Eric Moore Road a Surulere cikin jihar Lagos. Bai sha wuya ba ya riski kamfanin kasancewar yana da adireshin a rubuce. Su suka ba shi masauki, washegari suka yi masa intabiyu da (screening) din takardunsa. A take suka dauke shi cikin manyan ma aikatansu, saboda kyawun takardunsa. Sun ba shi sati daya ya koma gida ya shirya ya dawo ya shiga office. LANGE AND GRANT kamfani ne mai zaman kansa da ke karbar kwangilar gine-gine (construction company) na abubuwa da dama, sannan suna daukar nauyin ma aikatansu da tura su kwasa-kwasai kasashen da suka ci gaba, babban ofishinsu yana nan a jihar Lagos. Samuwar aikin nan ga Ma arouf ba karamar sa a ba ce a gare shi, da duk wani mai kaunarsa. Ya dawo gida cike da farin ciki, ya sunkuci Aisharsa yana juyi da ita a tsakar daki. You are a blessing Aisha. Tunda na aure ki nake cin karo da farin ciki iri-iri, da ci gaba ta kowane fanni. I really love you. Pack our belongies (harhada mana kayayyakinmu). Mun zama yan Lange&Grant Murmushi kawai Aisha ta ke yi. Ita ba za ta iya gaya masa adadin kaunar da ta ke masa ba, kuma ba za ta gaya masa kullum ta yi sallah addu ar ci gaban rayuwa da gamawa da duniya lafiya ta ke masa ba. Baba ma ya yi farin ciki. Ya sa Aisha ta shirya ta je ta yi wa mahaifinta sallama. Har matan baban ta gaisar ta yi musu sallama, ta gaya musu za su koma jihar Lagos da zama. Ba wadda ta damu da me ta ke ciki, don haka suka bi ta da a dawo lafiya Tare da Baba suka tafi Lagos ya je ya gano muhallinsu. Madaidaicin gida mai dakuna uku da falo. Komai na bukatar rayuwa akwai shi a gidan daidai bukatar kowanne dan Adam. *** *** *** Shi kansa shugaban Lange & Grant , Mr. Timothy Emmanuel na mamakin (talent) irin na Ma arouf, kullum cikin kawo musu sababbin discoveries da ideas yake. Tunda ya zo bangarensa na ginin titunan mota da jiragen kasa kara inganta yake, sai samun abokan ciniki suke. Ma arouf ne ya sa suka yi kokarin da suka soma karbar kwangila daga (Federal Government), hakan ba abu ne mai sauki a gare su ba a da (before), amma da zuwan Ma arouf sai ya maida shi mai saukin. Suka soma samun kwangila daga gwamnatin tarayya. Cikin shekaru biyu da shigowar Ma arouf kamfanin, ya samu ci gaba a dukkan bangarorinsa, don haka shi ma ogansu Mr. Timothy ya kara masa promotion, da daraktansu ya yi (retire) ya dora ma arouf a kujerarsa. Ya zamo daya daga cikin (board of directors) na kamfanin, da tafiya ta yi gaba ya zama mataimakin Mr. Timothy. Abin da ke bai wa Mr. Timothy mamaki da Ma arouf ya ki zuwa kowanne (course) da suke tura shi Amurka, bai yi shiru ba, kuma ya yi masa bayani, ra ayinsa ne, tsarin rayuwar da ya yi wa kansa ne ba shi ba fita waje. Shi ma sai ya kyale shi, sai dai ya ga abokan aikinsa na fita, su kuma hakan na musu dadi. Saboda suna kishin daukakar da ogan ke masa a kansu, shi da ya zo a bayan-bayansu, amma har ya isa kololuwa. Zuwa wannan lokacin duk wani rufin asirin rayuwa da dan Adam mai ilimi ke nema, Ma arouf Habibu Ji-qas ya same shi. Falla-fallan motocin hawa har guda biyu, ya gina (smart mansion) dinsa a Fati Mu azu Links cikin Bauchi, ya bige gidansu ya yi wa Baba ginin da ya ja hankali a unguwarsu, ya doke na Baban Aisha. A kauyen Ji-qas ya yi wa mahaifiyarsa da mijinta gida na gani a fada, wanda duk kauyen babu kamarsa. Haka yake dauko ta ya kawo ta Lagos ta yi kwanaki ta huta tare da Aisha. Suna son juna ita da Aisha suna girmama juna, suna kiyaye mutuncin juna.