← Book details Sanadin Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 17

Sashe 1

Sanadin Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Root Entry
WordDocument
0Table
Data
Normal
Default Paragraph Font
Normal Table
No List
0Header Char_1221a602-2082-4623-919d-d9da668ff92d
header
0Footer Char_a2b558c4-b015-41a4-a4e2-f0a91cd3812d
footer
Hyperlink
SANADIN KENAN!
1
Littafin
SUMAYYAH ABDULKADIR
HYPERLINK "mailto:[email protected]"
[email protected]
HYPERLINK "mailto:[email protected]"
[email protected]
SADAUKARWA
Littafin AMINA sadaukarwa ne ga duk makaranta littattafan TAKORI. Wadanda na sani da wadanda bansani ba. Ina son ku, ina alfahari daku. Allah ya kara zumunci.
GARGADI
a yarda a karanta ko a rubuta littafin nan a kowacce kafar sadarwa ba, gidan radio da sauransu ba tareda izinin marubuciyar sa ba. Yin hakan zai jawo gurfana a karkashin shari
a insha Allahu.
TUNASARWA
Ba labarin wani ko wata nawa bane, kirkirarren labari ne don fadakarwa da nishadantar da mai karatu. A guji zargin cewa anyi ne don wani ko wata. AMINA kirkirarren labari ne.
SHIMFIDAR LABARIN
Yayi missing flight dinsa ne mai zuwa Abuja ba da son ransa ba.
Ashe da rabon zai ga bacin ran da bai taba shiga kwatankwacin sa ba.
Ta danna madannin kararrawar dake jikin bango ta kiran ma
aikatan gidan, nan da nan mutum biyu suka zo, samari ne guda biyu masu share-share da goge-gogen gidan, ba wanda bai wuce shekaru ashirin a cikinsu ba.
Ku dauketa ku kaita
toilet
kuyi mata wanka, ku cire mata
pampers
dinnan tun dakin bai soma wari ba
Matasan biyu suka dubi juna kamar masu yin shawara, ta galla musu harara
ko bazaku yi bane?
Da sauri suka ciccibo yarinyar, daya ya riko kai daya ya riko kafafunta sukayi bandaki da ita, suka tube ta suka cire
pampers
zasu soma wanke ta.
Kamar wanda aka jefo ya shigo babu zato babu tsammani. Yana so ya gaya mata jirgin ya tashi ya barshi sakamakon wasu muhimman baki da yayi suka tsaida shi. Saidai ya jira na yamma insha Allah.
Idonsa bai sauka akan komai ba sai kartin maza kabilu rike da Amina sun tube ta, idanunsa suka kada sukayi jawur, zuciyarsa ta rika wani irin tafarfasa, hakan bai sa yayi magana cikin fada ko bacin rai ba, a sanyaye ya zuba mata ido na
yan dakiku kafin ya soma magana.
Maza balagaggu kika sa suka tsiraita
ya ta haka?
Yar tawa kwalli daya Lailah?? Ban yi zaton ko auren kiyayya kika yi dani ba Lailah bazaki iya taimakawa mara lafiya marainiya ba!
Kina nufin su sanya hannu a (private part) din diya ta? Ban taba dukan mace ba, bana fata in fara a kanki, kije duniya ce, kuma in gaya miki wannan yarinyar ta fi mun duk abinda na mallaka da rayuwar baki dayanta. Kisa a ranki kema mace ce, kuma zaki haifa, baki san yaya kaddara zatayi da abinda kika haifa ba kina raye ko bakya raye
Kallo daya ya yiwa ma
aikatan suka saki
pampers
din da suke cirewa suka yi waje. Cike da addu
a a zukatansu, kada Allah yasa wannan ya zamo sanadin hanyar abincinsu. Suma sun ji umarnin da aikin da aka sanya sun
to amma meye laifinsu? Salin-Alin suka fice.
Da sauri ya wanke Amina da kansa yayi mata wanka da soso da sabulu mai kamshi, ya nado ta cikin shawul ya fito da ita. Ya shafe ta da vaseline ya sanya mata sabuwar
pampers
da sababbin riga da siket masu kyau. Sannan yayi waya kicin a kawo masa
da
pancake
Da kansa ya rinka baiwa Amina a baki wani na shiga wani na dawowa yana goge mata har ta koshi ta ture. Jiki ba kwari Laila ta wuce don ganin yadda yayi kamar babu ita a dakin. Bata taba tsammanin zai dawo a yau ba sai bayan kwana uku kamar yadda ya ce. Ta kulla a zuciyar ta ko
cangal
bazata yiwa yarinyar ba har ya dawo.
Maganganun da ya gaya mata ba su ta zata ba, tafi zaton dan banzan duka daga gareshi yadda ta lura yana son yarinyar tasa. Kafafunta ba kwari ta nufi dakinta.
Ya sumbaci Amina a goshinta ya mayar da ita ya kwantar ya gyara mata pillow, ya fito falo ya jibgu a kujera mai tsananin taushi. Ya kai hannun damansa ya dafe kz
ansa dake tsananin sarawa. Ji yake dan son da ya fara yiwa Lailar na
decreasing gradually........(raguwa a hankali). Zufa ta shiga karyo masa, da ya tuna kalami na karshe na uwar Amina.....
Ka kara kula da Amina, ba don na raina kulawarka gareta ba, she will need extra more...
Yess! Tana bukatar karin kulawa, kuma zata samu insha Allah in har ina raye kuma kudi suna da amfani zata samu kulawa. Da gaske kula da
ya mace sai mace. Na lura matar nan son kashe min Amina tayi ko abinci bata bata ba har karfe biyu na rana. Kuma tasa maza su tozarta ta ba don Allah ya dawo dani ba.
Ya san muddin ya gayawa Hajiyarsa wannan abun cewa zatayi zata dawo ta kula da jikarta. Bayan yanzu ta fara samun nutsuwa a gidan mijinta da nata koshin lafiyan, hankalinta ya tsaya waje guda. Zaiyi
finding solution (nemo mafita) da kansa.
Babu wanda ya fado masa a rai sai tsohon abokinsa Dr. Usman Turaki. Consultant a asibitin koyarwa na Tafawa Balewa teaching hospital.
Tare sukayi sakandire, sun shaqu sosai a wancan lokacin, yanayin karatu a gaba ya raba su, kowa da jami
ar da ya wuce da fannin da ya zaba.
A take ya zakulo lambar Dr. Turaki, ta jima tana kara kafin matarsa ta daga. Abinda tace shine
Doctor is on call. A gida ya bar wayarsa
ok. Please da ya dawo kice ya kira ni da wannan no.din. Ma
arouf Ji-qas ne
Insha Allah zan gaya masa
Chapter 1 · 0% Book details