Sashe 8
Sanadin Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mahaifinta ba su damu da su ba, sun watsar da su, tun rasuwarsa wani nasa bai taba tako gidansu ba, amma Goggo ba ta yi zuciya ba, jefi-jefi tana tura Aminan. A cewarta, Naka sai naka ko ta ina aka juya sune iyayenta, ita ba wani abu ta ke so su ba su ba, a ah zumuncin Allah, wanda Allah subhanahu wata ala ya yi umarni da a yi shi, Ya nesanta da mai yanke shi, Allah ka sa mu dace amin. Ita kadai ta ke wadannan tunane-tunanen, har aka zo garin Shira. Ta dauko ledojin tsarabarta ta doshi gidan kawunnin nata. Gidan su mahaifin Amina malam Mas udu babban gida ne irin na Gandu, kowa an ware masa sassansa da iyalinsa. Bangaren Kawu Bilya daban, na Baffa Tasi u daban, shi ma Kawu Sule yana da bangare cikin gidan inda yake sauka da iyalinsa idan ya zo. ya da jikoki rututu don Bilya matansa hudu, Tasi u mata uku, akalla kowannensu yana da yan da suka haura goma, kuma babu wata tartibiyar sana a bayan noma, ita ma sai shekara-shekara, don haka duka matan kowacce da sana arta don mazan ba wani abin kirki suke iya yi musu ba, karfin ciyarwa a wuyansu yake. Uwargidan Kawu Bilya, wato Asabe sana ar man kuli-kuli ta ke yi, ta biyun Sahura dinki ta ke yi, ta uku sakar huluna na maza, ta hudu Ramma danwaken sayarwa ta ke yi, ya kuwa ga su nan ba adadi don kowacce tana da kusan goma. Bangaren Baffa Tasi u shi da dan dama-dama, yana kokari a kan iyalinsa, duk ya kwashi yansa ya sanya a makarantar boko, babu wanda yake bari ya zauna a gida yana jiran a gama dahuwar abinci, sannan matansa akwai tsafta daidai misali, bai hana su yin sana a ba shi ma kamar Bilya, sai dai yana wadata su da abinci, kuma suna zaman lafiya sabanin matan Bilya da kullum kamar su cinye kansu wajen tarewa ya fada. Amina ta yi sallama ta shigo sassan kawu Bilya ta fara shiga. Ramma ce ta fara ganinta, ta dago da mamaki a fuska da muryarta ta ce, Wa nake gani kamar Amina? Ta yi dan murmushi, Ni ce Goggo Ramma Ta tsuguna ta gaishe ta kafin ta bi sauran matan daki-daki su ma ta gaishe su, ta dawo dakin Ramma don duk ta fi su kirki, suka dan taba hira ta tambayi jikin kawun Ramma ta ce, Babu sauki wai ciwon arne, mu je ki ganshi Ramma ta yi mata jagora suka yi sallama a turakarsa, kallo daya Amina ta yi masa zuciyarta ta buga don sai ta ga kamanninsa da mahaifinta sun fito sosai. Yana kwance duk ya kare, sai tari yake yi. Amina ta gaishe shi, da kyar ya samu ya amsa sakamakon tarin da ke turnike shi. Ya yafito Amina alamar ta zo gare shi, Amina ta matsa kusa, ya kama hannunta ya ce, Ki yafe min uwata, na kasa zama kaka a gare ki saboda son zuciya irin tawa. Ba irin kyautatawar da mahaifinki bai min ba, amma na bi ta kai na take saboda son zuciya irin nawa. Ki yafe min ko Allah ya sassauta min zunubin yin wasarere da zumunci da maraicinki, ki kuma roka min mahaifiyarki yafiya don Allah Hawaye suka cicciko a idon Amina, Wallahi Kawu, Goggona ba ta taba rike ka a zuciyarta ba, ita ta umarce ni da in zo in duba ka, an gaya mata ba ka da lafiya. Ga wannan ma ta ce in kawo maka Ta dire masa ledar da ta riko, ta ci gaba da cewa, A nawa bangaren ni ma na yafe maka, Allah ya yafe mana bakidaya, Ya tashi kafadunka Ya dumtse hannun Amina cikin nasa, ya dinga sanya mata albarka, da kyar ya cika ta sakamakon wani tarin da ya turnuko shi. Amina ta tambayi Ramma ko an kai kawun asibiti? Ramma ta ce, Yo halin Sule wanne ne ba ki sani ba? Ana ta yi masa aike ya zo ya kai shi asibitin ya ki zuwa, tarin fuka ke damunsa in ji malamin asibitin da Tasi u ya dauko, ya yi masa allurai ya ba da magunguna yana ta sha, amma ga shi nan kullum sai abin da ya yi gaba. Amina ta ce, Zan gaya wa Goggona mu zo da taxi gobe a kai shi asibiti Ta yi sallama da su ta shiga sassan Baffa Tasi u kowa a gidan yana lale maraba da ita har shi Baffan. Ta kawo tsarabar Goggo ta ba shi, shi kuma ya danka wa uwargidansa Azumi ta hau rabo, suna hira yana ba ta labarin ciwon yayan nasa, ya ce shi ya yi duk iya kokarinsa, ya dauko malamin kyamis ya duba shi ya yi masa allurai, bai san ya zai yi ya fitar da shi asibitin maraya ba, karfin nasa bai kai nan ba. Sule ne dama ya kamata ya kai shin, to an yi aiken duniya ya ki zuwa Amina ta ce, A kyale shi Baffa, gobe za mu zo da mota ni da Goggo mu kai shi asibitin Baffan ya yi ta sa mata albarka. Ba ta jima ba ta yi sallar la asar ta kamo hanya, kafin magriba tana gida. Ta kwashe komai ta gaya wa Goggo. Goggo ta ce, Allah ya kai mu goben, kin ga ai gara da ki ka je, da haka za su barshi a gida ciwo ya ci ya cinye shi, ai fuka ba ta da kyau, mugun ciwo ce, Allah ya ba shi lafiya Washegari Ilya ne ya samo motar, aka tsadance zuwa da dawowa da wucewa asibiti, Goggo ta biya suka kama hanya. Da yake ba tsaye-tsaye ko jiran fasinja, nan da nan suka iso Shira. Da ma tun kamin su iso Ramma ta kintsa mijinta cikin yan kayansa masu haske, Ilya da babban dansa Hamza suka sanya shi a motar. Kai tsaye ATBU Teaching Hospital suka wuce da shi. Likitoci sun karbi kawu Bilya, aka soma ba shi taimako bayan an ba shi gado. A binciken da suka yi ma bayan tarin fuka, akwai sugar tare da shi da hawan jini. Duk abin da suka nema Goggon Amina ta biya, suka ci gaba da ba shi kulawar da ta dace. Dansa Hamza ne yake kwana da shi, Amina na hidimar kawo abinci safe, rana, da kuma dare. Kwanansa uku ya soma murmurewa, sai kuma kunyar Hauwa u ta hana shi sukuni. Da ya ganta sai hawaye da rokon gafara, yau bakuwar haure ita ta ceto shi daga cututtukan da suka kusa hallaka shi. Jininsa Sule ko oho! Balle yan cikinsa. Kwanansa bakwai ya yi garau, likitoci sun kafa masa sharadi kan cimar da zai rinka ci ya ce, duk ya ji ya amince. Goggo ta sake biyan kudin mota Hamza da Ilya suka maida shi Shira. Tun daga wannan abu da ya faru, Amina da Goggonta suka zamo shalele wajen dangin Amina na kauye. Kowa Amina- Amina, gidan Kawu Sule ma taje bata tarar da shi ba, wai yayi tafiya kasar Togo. Zuwan da Amina ta yi da na sanin yinsa. Tunda Hafiz babban dan kawu Sule ya ganta ya rikice wa uwarsa Atika shi fa ya ga mata. A washegari sai ga shi gidan su Amina gidan da bai taba taka kafarsa ba tunda aka haife shi. In ran Amina ya yi dubu, to ya baci. Ta fashe wa Goggo da kuka tana fadin, ta shiga tsakaninsu, ba ta son maganganun da yake mata. Goggo ta ce, An taba shiga tsakanin yan uwa ne Aminatu? Ki bi shi a hankali, ba wanda ya isa ya yi miki auren dole muddin ina raye Hafiz fa da gaske yake, ya makalewa gidan Goggo, abincin ranarsa a gidan yake ci in ya taso aiki, ma aikacin MTN ne. goggo ba ta taba nuna masa rashin goyon bayanta ba ko a fuska, Allah ta ke gaya wa cikin sallolinta Ya zaba wa Aminanta miji na gari, mai addini, wanda zai rike ta da maraicinta amana. Amina da ta gane lokacin zuwan Yaya Hafiz gidan, da zarar lokacin ya kusa za ta sulale ta bar gidan zuwa gidan su Ilya wajen Goggo Zulai, tana taya ta gyaran zogale da dahuwarsa, sana ar Zulai din ke nan, in ya tafi Ilyan Goggo zai zo ya gaya mata. Haka za ta koma gida tana yi wa Goggo mitar ita ta sakar masa har ya maida gidansu wajen zuwa. Ita fa ko maza sun kare a duniya ba abin da za ta yi da dan kawu Sule, balle ma mijinta ba a haife shi ba. Goggo murmushi kawai ta ke yi, ba ta cewa komai. Da gaske Amina ta kullaci kawu Sule, duk da yadda ta ke nusar da ita. Kuma ba ta son kalaman Amina masu nuna ba ta da niyyar aure a rayuwarta. A haka hutunsu ya kare, Amina ta koma makaranta. Atika har gida ta zo ta tadda Goggo da kashedinta, cewa ta yi gaggawar kwance asirin da ta kulla wa Hafiz ta tura Amina gidansu da shi, domin ko mata sun kare ba abin da Hafiz zai ci da Amina, su ba su gaji fatara da talauci ba. Don haka a kiyaye tun Babansa bai ji ba. Goggo ba ta ce mata komai ba har ta yi bambaminta ta gama, ta fita. Ta girgiza kai, a fili ta ce, Rayuwa ke nan Hafiz bai fasa zuwa gidan ba ko bayan da Amina ta koma makaranta, ita kuma Goggo ba ta fasa ba shi abinci ba in ya nema, sannan ba ta gaya masa mahaifiyarsa ta zo ta yi musu cin mutunci ba, ta bar komai a hannun Allah. Cikin dumi irin na Hafiz yake gayawa Goggo babansa yake jira ya dawo daga Tokyo ya gaya masa zancensa da Amina, ya ce, Goggo na san zai yi farin ciki, zumuncin da ya gurgunce zai mike. Don Allah Goggo ki dinga nuna wa Amina na rasa gane kanta, ni dan uwanta ne, jininta. Zan fi kowa rike aurenta da daraja Goggo kan yi murmushi, Hafiz gata ne ya yi masa yawa shi ya sa yake ganin komai yake so zai same shi da sauki. A ranta cewa ta ke, ashe kun san kuna da yan uwan na jini da ma?