Sashe 9
Sanadin Boko Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ban so na fada ba) A lokacin in zaka tuna ina karami amma raina yayi matukar baci kwarai, da muka je Makaranta nake fadawa Hashim sai ya ce Ai shi jiya ya ji Dadarsu tana fadawa Abbansu zaman hakuri kawai take yi da Abbansu, don ita ba shi take so ba, daga lokacin na kudurce a raina bazan taba aure ba, sai wadda nake so take sona. Ina son iyayena ku taimake ni, ku duba hujjojina, in kunki ni zan hakura in yi biyayya amma har abada ba zanyi farin ciki ba. Duk jikinsu yayi sanyi, kuma sun tabbata kowannensu yanada shigen wanan matsalar ko shi bai son matar ko ita bata son shi, amma wanda suka hada kansu su suna zaune lfy. Baffa sa‘adu yace, ina rokon lamido yayi mashi izini yatafi, mukuma munyi shawara. Lamido yace, ya iya tafiya. Abubakar ya mike cike da kwarin guiwa ya fita. yasan adu‘a bata faduwa, don tashi yake tun 2 dare ko 3 yana fadawa Allah matsalar shi. Lamido ya dubesu daya-bayan-daya, kuna nufin kun amince da batun sa? Baffa jume yace, a a sai yanda kace. Baffa sa‘adu yace, da zai yuwu hujjojinsa sun isa a duba lamarin, koda a gaban kotu ne. Amma in zancena ya bata ran lamodo aimun afuwa. Lamido yace ban gamsu ba har yanzun, biyayya muke bukata kuma kuje kuci gaba da shirin biki duk suka watse, kowa zuciya cike da nazari. Da dare ya sake zuwa gidan Baffa sa'adu don ya lura shi mai saukin kaine, kuma zai iya taimaka masa har yaga ya ci nasaram ya ce Baba na zo ne naji ko kun gamsu da bayanin bayan tafiyata? Baffa ya ce, Lamido bazai taba amincewa ba, ni kaina na cutu da wannan hadin da ake yi tsahon lokaci, sai da na sake Aure sannan na sami nutsuwa. Dalilin musgunawar da mai dakina take min duk dan ranta baya son auren mu. Aure na da Bilki ita ma 'yar dangi ce amma ni na ganta na ce ina sonta, ta yarda. Daga kanta ne na gane aure kina so ina so shine aure, in mace tana sonka tana kaunarka da ka sami matsala zata fara tausayinka, zata yi komai don ta faranta ranka. Amma in mace bata kaunarka, Abubakar akwai matsala babba. Ni yanzun shawara daya zan baka, ka gwada. Kaje ka sami Limamin Masallacin Juma'a kasan aminin Lamido ne ko?" Abubakar ya ce eh, ya ce to kaje ka same shi kayi masa bayani da neman tainakonsa, kila a dace. Kasan mu 'ya'yansa ne bamu da wani karfin tankwara shi, ga rikicin tsufa. Muna son mu lallaba shi ne har mu rabu lafiya. Abubakar ya ce za shi. Sai da kafa ta dauke sannan ya shiga gida. Don yana tsoron haduwar shi da mahaifinshi. Yana maida kofa ana turowa, sai da gaban shi ya fadi, zaton shi Dada ce, amma ai yaga Ummi ranta a bace. Ya matsa ta shiga, ya dubi agogo sha biyu ta gota, ya ce Ummi kina menene baki bacci ba? Ta zauna "Hamma ka janye auren kan nan mana, Dada ta yini kuka, hawayenta ba sauki bane a wajenka." Ta zamo ta durkusa, "ka dubi Allah kayi hakuri ka yarda cewa haka Allah ya so ganin zuri'armu. Ya kama ta, "Tashi Ummi Dada da Abba zasu fahimce ni da zarar komai ya daidaita, kije ki kwanta, fata na daya ki taya ni fada ma Allah shine kadai mai maganin matsalata. Baffa Sa'adu ya bani dama ta karshe, idan har na gwada bata yi ba, na dauki alkawarin cewa na hakura." Ta ce "zanci gaba da yi maka addu'a," Ta fita. daga sallah asubahi bai dawo ba saboda tsoron haduwa da mahaifansa, gidan Hashim ya karya duk da ruwan tea ne ya sha. Yayi wa hashim bayani, hashim yace, sannu namiji. Kayi kokari, zan rakaka gurin liman. Bayan la‘asar suka sami liman agida, sun gaisheshi sannan suka gabatar da kansu, yayi murna da jin jikokin amininshi ne, daga nan suka kora mashi jawabin komai. Liman yace, to zan ganshi in Allah yaso zamu tautauna batun, in kuma ya sausauta ra‘ayinsa to akan nada kyau, don nasha yunkurin in fada mashi wanan al‘adar tayi tsuri, musanman in yana bani lbr matsalar gidan yayansa ko wasu daga jikoki wadanda basa zaune lfy. Amma nakan fasa in na tuna yanda ya dauki lamarin. To yanzu tunda dama tasamu zanyi kokari in nusar dashi. Sukayi godiya sannan suka tafi. Duk aranarce dai liman yayi tattaki zuwa gurin lamido, sunyi murna da ganin juna, duk da cewa ko yaushe suna haduwa. Sun gaisa sannan liman ya soma da cewa, aminina gurinka nazo da batu mai matukar muhinmanci, duk dacewa batun nawa ba zaiyi maka dadi ba. Amma inaso kakali lamarin ta fiska 2, addini da kuma zamani. Ni da kai dukanmu musulmai ne, muna koyi ne da manzon tsira (s a w) addini ya amince muzabawa yayanmu maza na kwarai amma bai yarda muyi musu auran dole ba. Idan muka dubi fiskar zamani zamuga cewa, mubar yayanmu suyi auren so da kauna, zaifi bamu kwanciyar hankali. Lamido yace, oho! Abubakar ya kawo maka karata kenan? Liman yace a a yazone yanemi da in rokyaka ka amince, yayi aure da wada yake so, wai shin ma wane dalili yasa ku rike wanan al‘adar sai kace bauta? Lamido ya ce iyaye da kakaninmu suna gudun hada iri da wani ne saboda kada mu gauraya da mugun iri. Liman yayi dariya sannan ya ce, da kai dani da bature da balarabe da igbo da hausa da duk wani yare daga mutum daya muke shine Annabi Adamu Alaihissalan. Sannan Manzon Rahma ya fada mana Musulmi 'yan uwan Musulmi ne. Lamido ya ce, amma nasha ji daga bakin ka kana cewa mai yanke zumunci ba zaya shiga Aljanna ba, wata rana kace ba mai shiga Aljanna sai mai sada Zumunta. Liman ya ce to ai ba ana nufin ka kamo wannan ka ce sai sunyi aure ne zumunta ba. Abinda ake nufi shine Ziyara, kwana biyu ka dade baka ga dan uwanka ba, shirya kaje ku gaisa kuyi zumunci, wannan shine sada zumunta. Yanke zumunta kuwa shine kace wane baya zuwa, don haka nima na gaji da binshi bazan je ba, kowa ya zauna a inda yake. Shine yanke zumunta, don haka ka sassauta ra'ayinka ka tafi dashi daidai da zamani. Sannan daidai da turbar addinin Musulunci, cewa aka yi in zaku yi aure ku nema wa 'ya'yanku Uwa ta gari. Sannan ana auren mace saboda abubuwa guda hudu, asalinta, kyawunta, kudinta da Addininta, Manzo SAW ya ce na hore ku da ma'abociayar Addini, don haka shawara anan sai ku duba, suwaye iyayenta? Kuma wanne irin hali gareta? In mai Addini ce shike nan. Ku hakure ku cebakomai saikuga ci gaba, ku cire 'yar wani dangin kusa ta cikin naku shine karuwa, shine zumunci dangin ku sun zama 'yan uwa da danginta, kuma ko bayan ranta zaku yi ta zumunci da danginta. Liman ya dinga bashi misalai tare da Hadisai zuwa Ayoyi, har jiki Lamido yayi sanyi, ya ce to zai gana da 'ya'yanshi, in yaso za a bincika aji asallinta. Amma fa sai dai in ya yarda ya hada mata biyu, domin baza a fasa Fadi ba. Liman ya ce, "Wannan ba laifi ba ne." Lamido ya kuma tara 'ya'yansa ya gaya musu cewa, sakamakon zuwan da Liman ya yi yayi masa bayanai da dama akan wannan lamari, dan haka ya nada Baffa sa'adu da su binciko masa 'yar wane ne? Sannan ya ce da Abba in yaje gida ya turo masa Abubakar. Ko da Abba ya dawo gida bai samu Abubakar ba, sannan duk wayoyinsa a kashe suke, ya kira Hashim yake gaya masa in ya ga Abubakar ya fada masa Lamido yana neman sa. Tare suka je gurin Lamido ya ce, "Hakika kana da sa'a, zan amince da auren in naji cewa Iyayenta masu mutunci ne, itama 'yar mutunci ce. Sannan kuma in ka yarda ka hadasu 2 ka auri Fadi itama. Sannan ita yarinyar tunda bakuwa ce anan gida na zaka kawota mu zauna da ita muga irin nata dabi'un." Har zai ce wani abu sai Hashim ya zungure shi, sannan ya ce ya amince. Lamido ya ce, "Shi bashi da baki ne sai kai?" Sannan Abubakar ya ce, "Na amince." Lamido ya ce, "To sai kuje, in mun shawarta lokacin da za'a je zaka ji."Farin ciki gurin Abubakar baya misaltuwa, ya isa gidansu da karfin gwiwa. Dada tana zaune suna hirarsu da Rukayya, ya zube gabanta yana neman gafararta, sun ji komai daga bakin Abba, sai dai ta ce, "Shawara daya zan baka, kada ka yi rawar jiki akan bakuwar da zaka kawo cikinmu, ka nuna kamar kafi son 'yar uwarka a kanta, ka tashi mun yafe maka. Ka samu Abba ka bashi hakuri, sannan ka samu Hashim ku je gurin Fadi." Ya ce, "To." Ummi cikin murna ta ce, "Ni kam in zaka Kano zan bika muje na ga Hafsat." Ya ce, "To, Amma sai na fara zuwa in na dawo sai muje tare."shi da Hashim suka nufi gidan Goggo Jami, sun jero ita da Fadi zasu fita, hannun Fadi rike da makullin mota, sai ga Abubakar. Suka tsaya Goggo da fara'a ta ce su shiga. Fadi ta musu sannu da zuwa, suka gaisa sannan Goggo ta koma ciki tasa a kawo musu abin sha duk da cewa da safe ne. Fadi ta gaishe su, Hashim ne ya ce, "To Fadima, kin san dai dalilin zuwanmu tunda magana ta yi nisa, yanzun ma yana kan hanyar tafiya ne muka biyo. In ya dawo zamu zo zuwa na musamman." Ta ce, "OH, zashi gurin KISHIYATA ko? In kaje ka gaidata." Ta mike, "Nima zan je office ne." Suka mike suma, Abubakar bai yi magana ba, Hashim ne ma ya mata sallama. Suna hanya inda Hashim zaya kai shi filin jirgi don zuwa Kano. Ya ce, "Kuna ta fadin Fadi nada mutunci, dubi irin tarbar da tayi mana." Hashim ya ce, "Kishi ne, taga kowa a family ita daya ake aure, amma ita su 2, dole ta damu." Abubakar ya ce, ....