← Book details Sanadin Boko Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 16

Sashe 2

Sanadin Boko Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

lafiya. Babar ta dubeshi da murmushi tare da mikewa tsaye dan girmama shi. Hamma sannu. Yace rukayya sannu da gida, ina dada tana ciki? Suka ce eh, tana ciki tare da baki. Ya nufi dakin shi, ummi tana rike da hahhun shi. Ya zauna bakin gado ya dubeta. Me kuka dafa? Tace tuwon semo da miyar kubewa danye. Je ki kawo mun shi kuma ya tube ya dan watsa ruwa ya tasa tuwon agabanshi amma ya kasa ci, tun lokacin da yaga hafsat ya ganeta daga muryarta duk da girman da tayi, bai sa ya kasa ganeta ba. Yana son sanin mai ya faru bayan da ya barta. Ina su innarta? Ina babanta? Me yasa ta canja daga mai tsananin wasa zuwa ma fadaciya? Me yasa ta canja daga mai son mutane zuwa me kin mutane? Mai yasa ta canja daga mai son tai mako zuwa mai kin tai mako? wata zuciyar tace ita kadaice zata baka wanan amsar. Tunanin ya katse lokacin lokacin da yaji hannun ummi a bayan shi, yasani ita ce dan suna mayukar shiri da ita. A hankali ya dago kai ya dubeta, ta tsura wa fiskarshi ido, tana da kishin yaransu kamar yanda aka san fulanin adamawa da yola nayi, da wuya kaji sunayin wani yare in ba nasu ba. Shi kuma abubakar ya fi mai da musu da turanci, haka ma abban su. Tace hamma me ya faru ne?Baka ci tuwonba kuma gashi kana ta tunani. Yayi dan murmushi tare da cewa ummi, me kika gani ne? Tace baka ci towon ba kuma gashi kana ta tunani. Yayi murmushi tare da cewa ummi kenan! Gajiya nayi yau, shiyasa kika ganni haka ya janyo tire ga banshi tare da cewa, zauna muci. Tace nikam na koshi, kaci sai in fitar da kayan, kuma bakin dada suntafi ta fito. Yace to. Ya dan tsa tsakala ya ture, ummi tace hmma ni sai nake kallon kamar ba gajiya bace, in mutun ya gaji in yayi wanka yana cin abin ci sosai, kafin yayi bacci gajiyar ta tafi. Ya dubeta ko? Tace, eh, yayi murmushi. To me ke damuna? Tace, ina kallon kamar tunani kakeyi ko? Yayi murmushi har dan sauti yafita, san nan yace to tunanin me? Ta juya hannunta tare da cewa oho. Ya lumshe ido. Ummi tana burgeshi yarinyar tana saurin fahimta shi yasa suke shiri yarinyar tana sonshi fiye da sauran yan uwanta shi ma yana yana son yarinyar, ta katse shi gashi kana sake yin wani tunanin? Yace tunaninki nake ummi, tace tunanina? To me nayi? Yace saurin fahimtar ki, tayi murmushi, to na gane cewa kana tunani kenan? Yace eh tace to tunanin me kakeyi? Ya mike zan fada maki amma yanzu muje wajen dada. Mahaifiyar tasu tana kokarin kashe TV din da rukayya ke kallo tare da yin fada cikin harshen fillanci. Na fada maki bana son yawan kallon nan, in kin gama rubutun to kije kicin kiyi min wanke-wanke. Zatayi magana sai ta fasa, saboda ganin hamma. Ta mike ta nufi kicin din. Da girmamawa ya gaida dadar su, ummi tace su ya findo sun tafi? Yace dama sune kuka ce min baki? Da na shiga mun gaisa ai, tace sune kuma saboda kaine suka zo. Anjuma zamu zauna da kai in babanku ya dawo. Ya dan ware ido, gurina? Ta nufi daki tana cewa in mun zauna zakaji, nima na gaji. Ummi ta dube shi, hamma ka zabi mata? Yace in na zaba kece zaki fara sani, ta ce zaku fara fada da dada kamar yanda kukeyi da abba. Nasani dada zatayi maka zancen aure ne, don lamido ya tarasu da baka nan kaje kano bikin abokin ka ya mai da hankali sosai gurin ta, suwa ya tara? Tace su faffa dukansu, harda fafa na abuja da abba da su gogo dukansu. Ya danyi di, tabbas ya kure kakan nasu, yau kwana 3 da dawowar shi amma ba wanda yace mashi komai? Yayi a jiyar xuciya me suka ce? Tace abba ya fada dada amma bata fada mana komai va, amma dai lalai saboda kai lamido ya hada taron, yace shi yasa tun da na dawo abba da dada suke daure min fuska har nayi zaton da na dade a kano ne musalin 9 wayar shi tayi kuka, yadaga ya duba afili yace abba. Tare da kalon hashim. Nawa zan tafi, abba na kira na. Ya dauki wayar cikin fillanci abba ke fada mashi yana jiransa, yace to gani nan. Yace nikam na boni hashim gara ka bonin, in kuma baka da lfy ne ka fada mana. Abubakar yayi dariya, kaima ka daina goyon baya na? Yace eh, na daina tunda har da iskanci, ace kaf dangi baka ga matar aure ba? Kowacce kace baka so mugashi har munyi yara. Abubakar yace, in nayi aure yan bibiyu zan haifa kaga sai in kamo ku. Ya daga murya yana cewa, shatu na tafi. Yace to ka gaida gida. Abubakar lamido shi ne da na farko a gurin ma haifiyar shi, hajiya fatima wada suke kira da (dada) da alhaji ibirahim lamido wanda suke kira abba. Duk wanda yake garin yola yasan lamido abubakar (family) saboda dukiyarsu da kuma akidarsu ta kin auran bare. Suna da yawa matuka, sam basa son su bada yayan su waje kokuma dan su ya auro, basu taba ba tun kaka da kakanni, haka suke har yau. Lamido yana da yaya kusan 30 da yankai, maza da mata. Matan sa 4 ne, kuma dukansu dangin shi ne alhaji ibrahim shi ne da na 3 gurin mahaifiyar su gogwal, wace itace matar farko, haka shine wanda ya fara yin kudi fiye da mahaifin su kafin kanansa su biyo baya. Lamido abubakar sarkine a wancan lokacin, mai fada aji, kafin ya sauka ya ba baban danshi sa‘a du maifin hashim. Lamido yanada tsutsuran ra‘ayi a kan auren waje, duk yayanshi maza saidai yace shirya kaje wajen wance yar baffanka ko yar gogonka, inko macece sai dai yace wane zai zo ki shirya ko jikokinsa haka ne abbukar su 7 ne gurin mahaifinsu,usman ke bin sa, sai umar, sai aiyu sai kasim, sanna rukayya sai auta hauwa'u, sunan gogwal ta ci suna ce mata ummi. shi ko abbukar sunan mahaifin lamido yaci, kakan babanshi kenan, shi yasa lamido ke san shi duk cikin jikokinsa yafi son baban shi abbukar kaf family hammam suke kiran abbukar don girmamawa. yana da wani irin kwarjini mai ban mamaki ga farin jini kowa na son shi, bugu da kari ya taso hannun shi sake, ma'ana yana da yawan kyauta. ya sanka bai sanka ba in yana da shi xa ya baka, shi yasa kawunan shi da goggonin sa su yafendon sa har su baffan shi kowa na son hama ya auri yarsa. su kan su yanmatan cikin family suna son sa, wasu har sun yi masa maganar, wasu sun aiko amma baice ma kowa kala ba. abbukar mutum ne da yake tsayiwa kan ra'ayinsa, a tsarinsa baya sha'awar macen da xata ce tana son shi, yafi son yaga mace da kansa yace yana sonta, matsalar shi duk cikar family bai ga wadda ta mishi ba, duk kuwa da kyawun yanmatan yana cikin maxan da kyau baya tsarin shi. a yanxu haka yana da (mastets digree) a fannin kasuwanci, yana jan kamfanonin abban su ne yayin da abban ke hutawa, tun kusan shekaru 7 bay, lamido ke zaba mishi yanmata yana cewa sai yayi master xaya yi aure. a tarihin gidan su shi ne da na farko wanda ya karya dokar lamido, ya ki yi aure a lokacin da ya bukata, bayan ya kammala karatu ya soma aiki.lamido ya kira shi yace mishi abbana, ina son ka shiga da kanka gidan baffanninka da ggonninka ka duba mata, in ma da xan zaba maka da kaina sai in ce kaje gidan baffanka na abj yaransa suna da kyau. Abubakar ya dubi kakansa, lamido nifa ba mai kyau nake so ba, kaikam sakarai ne saikace ba dan boko ba? Kowa yana son mace mai kyau, yace ban da ni, akwai wasu halaye danake son matata ta kasance dasu, a dan bani dama in tantance. Lamido yace to ubana, na baka wata 2 lokaci ishashe ya isheka kayi duk bin cikenka, abubakar yace na gode. Wata 2 har da saty 2 lanido yaji abubakar shuru, dan haka sai yasake aikowa ayi mashi kinran abubakar, wanda ya kasance cikin wanan kiran a kowanne lokacin. Abin da ya kudirta shine ba za ta taba kai kanshi gurin lamido ba, har sai lokacin da ya kirashi. Ba yan salan isha‘i ne ya sami lamido a gidan shi, cikin falonshi mai tsari irin na masu kudin da, duk da haryanzu a kwai kudin bai damu da canja tsarin falon ba, don ya masa. Ya zauna tare da gaida lamido, sannan ya sunkuyar da kai, lamido yace cikin yar tsokana, abba na nasan kana da kara ko da ka zaba mace ba zaka iya zuwa gabana ka fada ba. To dan matso ka fada mun gidan wa kaga matarka? Wacece tayi sa‘ar samun namijin duniya kamarka? Abubakar ya lumshe ido sanan ya sunkuyar da kai yace, gaskiya lamido saboda aiyuka bansamu zuwa ko ina ba. Fuskar lamido ya canja daga fara‘a zuwa daurewa. Sannan yace duk tsawon lokacin nan bakaje ka aiwatar da abinda muka zanta da kai ba, don baka dauki abun da muhim manci ba? Yace, a a yanayin aiki ne. Lamido yace yayi kyau yau wace rana? Abubakar yace alhamis, yace to gobe in an taso sallar juma‘a ka kira hashimu kuzo ina nemanku.
Chapter 2 · 0% Book details