← Book details Sanadin Boko Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 16

Sashe 14

Sanadin Boko Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanadin Boko 2-7 Posted by ANaM Dorayi on 11:27 PM, 19-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Munir ya dubi mahaifiyar shi, fuskar shi babu walwala. Ta ce ya akayi? Ya mika mata takardar hannun shi, sakamako ne na gwaji ya amso, da sauri ta mike tsaye HIV? Subhanallah! Muje wani asibitin, ya ce Momy tun daga Dubai suka fada min ban yarda ba, sai da nazo nan na sake yi har kashi biyu, ta dauki waya jiki na bari ta kira Dady a waya. Kuka ta saka masa tana fadin Munir yana da kanjamau. Shima Munir din kuka ya saka, a sukwane Dady ya baro ofishinsa zuwa gida, ganin su cikin halin damuwa harda kannan shi, sai hankalin Dady ya kara tashi. Ya ce ku kwantar da Hankalin ku zan shirya mana zuwa America za a duba shi." Momy ta ce, zan fi son haka. Shi kadai ne ya rage min yanzun tunda yayanshi suka yi fada suka kashe kansu a Maleshiya, yanzun kuma a ce shima yana da kanjamau?" Cikin kankanin lokaci suka shrya suka tafi. Sai dai kash! Can ma sun tabbatar yana dauke da ita. Sai dai sun basu wasu maganguna cewa ya dinga sha, sannan idan sun zo nan ma ya dinga shansu. Jiki babu kwari suka dawo. Sannu a hankali ya hakura ya cigaba da zuwa aikin sa, yana shan magani. Sai dai koda yaushe yana zargin mahaifansa sune suka ja masa wannan halin, SANADIN BOKO. Da sun bari yayi aure ya tabbata baza ya zama daya daga cikin masu neman mata ba, gashi yayyanshi sun mutu su biyu. Shi kuma ga halin da yake ciki. Ya hadu da wata yarinya 'yar mutunci, Usataziyya a rufe cikin hijabi da nikabi, ya ce yana sonta. Tuni ya fara zuwa shira. Yarinya mai suna Nanah A'isha ta amince dashi, sam bai fada mata yana da ciwo ba, kuma ya gama sheke ayarshi, kuma yanzun 'yar mutunci yake son ya aura don cuta. Iyayenshi ma basu nuna masa abinda zaiyi bai dace ba, sai ma suka shiga lamarin suka yi dumu dumu suka yi ta barin kudi aka sa bikin. Wani daga cikin abokan Munir yayi mata text ta waya wai Munir yana da kanjamau, ko ya fada mata? In kuma bai fada mata ba to ta sani yanzun. In kuma tana musu to ta gayyace shi suje ayi gwajin jini. Nanah ta firgita kuma ta sanar da mahaifanta. Sune suka nemi Munir da ya zo suje ayi gwaji, nan da nan ya zuke daga nan kuma sai ya samu Nanah yana borin kunya, wai ya fasa tunda iyaynta basu yarda dashi ba. Ta ce to menene don sunce muyi gwaji, ai ba sai ta mummunar hanya ba ake dauka, ko malamai sunce ba laifi bane don anyi gwaji. Ya ce shi ya hakura, ta ce Allah ya hada kowa da rabonsa. Gida uku yana neman aure amma ana dagaoshi, bakin cikinsa ya karu. Dole ya koma wajen tsohuwar budurwarshi wadda suke rigima suna zargin junan su. A nashi tunanin ita ce ta sak mishi, ita ma tana tunani shi ya saka mata. Ya ce mata suyi aure kawai tunda suna shan magani, ta amince nan dai iyayen su suka shiga barin kudi tunda duk suna dashi. A yawon amarcin su ne suka je America aka duba su in da Likita ya tabbatar masu zasu iya zama indai suna shan magani, sai dai yana gani da wuya su sami haihuwa. Su basu damu ba, amma da suka zo gida Momy ta damu. Ta fadawa Dady cewa ita yanzun ba za ta samu jika ba a wurin yaranta maza? Ya ce kada ta damu, tunda ga 'ya'yanta mata. Haka suka ci gaba da zama shi da matar shi a unguwar Kinkinau. Sai dai kullum yana cike da bakin cikin ciwonshi, wanda yake danganta shi da iyayenshi duk SANADIN BOKO. *************** Baba ya dubi Umar ya ce, "Tunda ka yi aure ka kwashe kannanka baka son zuwa duba ni, gashi bani da lafiyar da zan fita nema. Ya ce "wallahi Baba bana son zuwa ne in ban sami dan abinda zan riko muku ba, yaran nan kuwa na kwashe su ne dan kuji saukin kudin haya. Nima can kasan buga buga ce kawai. Bus din tawa kwanan nan kudi kawai take ci kullum sai nayi gyara, Allah ya taimaka. Umar ya ciro dubu daya ya bashi tare da cewa "Ga wannan sannan ga doya nan" ya ce na gode Allah ya saka da alkhairi" Baba ta shigo ta ce, "Mun gode Umar Allah ya ba da lada." Har ya mike zai fita, ya ce Umar zomana" Ya dawo ya zauna. Baba ya yukura, Babah ta kama shi ta sa mishi filo a bango ya jingina. Ya dube shi dakyau. "Umar wai har yanzun babu labarinHafsatu ne?" Umar ya daure fuska, shi kam in karatune wannan tambayar to ya jima da haddace ta. Babah ta ce "Malam kai ne fa da kanka ka kore su, ba dole suyi nisan kiwo ba? Gara ma innar su sunsan inda take, amma Hafsa yanzun wayamasan tana mace ko a raye oho. Umar ya mike tare da cewa, "In da rabon ganawa za a gana." Baba ya ce, "Umar ina cike da nadamar abinda na aikata. Hakika ina zaton nine na yiwa Hafsa baki har kaddara ta fada mata, da ina mata addu'a da bata shiga wannan halin ba, ko dai zaka sa cigiya ne? Umar dai gani yau Baba yafi kullum rudewa akan batun Hafsat, sai ya lallaba shi da cewa. "To Baba, za a cigita kada ka damu" ya ce to Umar, a cigita. Allah yasa a dace." Tabbas tun bayan rabuwar shi da innar su Hafsat yaga matsaloli kala kala, ga ciwo ya sa shi a gaba, wai suga ya kwanta a asibiti har sau biyu. Umar ne ke ta fama dashi, don ma Allah ya taimaka Innar su ta sa shi ya saida mashin din ta cika masa ya sai Bus ya diban lodin kasuwa daga Rigasa. na dama ta shige shi yanzu tun da ya rasa matar shi fatansa ya samu yar. Cikin haka ne umar yaga yar uwar inna mai suna murja a wata ziyara da ya kai munanfashi. Yace yana sonta itama ta amince, nan aka kare komai inda aka sha buki,tare da dan madaidai cin gidan da ya kama mai daki 3 don haka ya kawo kannan shi zuwa gidan. Tun baba yana dan fita har ta kai baya iya fita din ma, ga ka‘idojin abinci, gashi ba kudi. Yanzu baba bashi da burin da ya wuce yaga hafsat, shikam umar ya kance bai san inda zaije yaga hafsat ba, domin yayi bakin cikin abin da ya faru. Kuma hafsat itace silar rabuwar iyayen su, shi sam bai ga laifin baba ba, tun da dai dai gwargwadon ilimi ta samu, sun dage sai tayi jami‘a, to ga abinda ya biyo baya yanzun. ************** Haka inna anata ban garen tana zaune lafiya gidan mijinta, da yayan taguda 2. Kuma duk sanda umar yazo takan tambaye shi ko ya sami labarin hafsat. Yace, inna ki daina batun hafsat, babu inda za‘aje nemanta. Ita tasan inda muke, inda muna ranta kamar yanda take ranmu da tuni tazo koda zamu kashetane. Kum inna ya kamata ki sauwaka ma kanki batun ta, dubi yanda tabaki kunya, ta zubar da kimanki ta kashe aurenki, dan kawai kin tsaya mata ta sami gishirin zamani, wato ilimi. Ta miki sakamako da haka. Inna tace, ina zaton kadarace ta fadawa hafsat, yanzu da tatafi ba asaniba ko tana raye ko tana a ma ce, kilama ta mutu gurin haihuwa. Umar yace, to muyi adu‘a kawai Allah ya yafe mata. Inna tace, amin. Amma nafi dora laifin kaina. Don da lokacin da mahaifinku yace bayaso tayi boko da na hakura da yanxu ban bar yaya na ba. Da yanzu bata gudu ba. Umar yace duk mu bar wanan ga kadara, Allah shine mafi sanin da lilin da hakan ta faru,tsakaninta da mijinta akwai mutiny's juna, haka nan ya yansa ta hada da nata yayan ta sunguma. ********* Abubakar ya dawo gida cike da rashin kwarin gwiwa. Cikin kwanakin duk ya canja ba kwanciyar hankali. Ummi ita ce ta fara gano haka acikin gidan su, ta dunga matsa mashi da son jin matsalar shi. Yace, kinyi kan kanta da in fahimtar dake halin da nake ciki. Tace zan gane hmma. Yace nida hafsat muna son juna, sai dai a kwai wani dalilin da take ganin zai hana mu aure wanda ban san dalilin ba. Kiyi shuru da bakinki kada wani a gidan nan yaji wannan zancen. Ummi tace, hmma ina tunanin zaka iya shawo kan kowace matsala da zata hanaka auren anty hafsa. Tunda ka iya shawo kan lamido ya yarda ka aure ta. Abinda ko iyayenmu ba zasu iya kwatanta hakan ba. Kai sadauki ne, kana da nasara a kan duk abinda kasa a gaba.ina ji ajikina zaka auri anty hafsa. Dadin kalaman ummi sun karfafa mishi gwiwa sosai, har ya bata kyautar wayar da take ta nacin ya bata. Da yace sai ta gama secondary. Amma yana bukatar ya kara natsuwa kafin yagane ta in da zai shawo kan matsalar. Ko da ya fada ma Hashim cewa hafsat taki, tace ba zata aure shi ba saboda wasu dalilai nata. Hashim yace, kada ka damu zamuje tare kuma zata yarda. Amma yanzu abinda nafi so ka nutsu, iyayanmu su san ka karbi fadi. Dan haka yau dadadare zamuje zance. Daga ofis super market ya wuce inda ya siyo kayan shafe-shafe da tande-tande dan suyi tsaraba. Lokacin da fadi ta nufo su abubakar, ya zuba mata ido. Gaskiya tana da kyau, sai dai baya jinta a rai kamar hafsa. Ta zauna suka gaisa, tace ya dawo lfy? Yace lafiya lau. Hashim yace, mun zone dama mu dan gaisa. Amma yanzu bari in matsa ku zanta ke da yallabai. Abubakar yace kaje ina, kamar dai zamu shekara? Bai saurari Abubakar ba, ya fita. Fadi tace, don baka sona shi ne zaka ce wai sai kace zaku shekara? Ni to ina son ka. Ya dube ta kin ji abakina cewa bana sonki? Tace, banji ba, amma naji yanda kaita kokarin doje ma aurana. Ni kam ko wane lokaci nayi sallah ina fada
Chapter 14 · 0% Book details