← Book details Sanadin Boko Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 16

Sashe 8

Sanadin Boko Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanadin Boko 2-5 Posted by ANaM Dorayi on 03:15 PM, 19-Sep-15 Under: SANADIN BOKO "Amma wanda ya bada wannan shawara ya kyauta, dan kai da Fadi kun dace, kuma ina zaton tana da wasu irin halaye da kake so." Ya ce, "Na rasa dalilinku na cewa mun dacen." Ya ce, "Ya kake son nayi da Hafsatu?" Hashim ya ce, "Kun daidaita?" Abubakar ya ce, "Akwai alamun nasara. Abba ne ya sani na dawo da gaggawa, saboda wasu takardu. Sati na sama zan koma ko da kwana daya ne, daga nan in mun daidaita zan kai ka ka ganta. Amma ka shirya anjima zamu je gurin Lamido." Hashi ya ce, "In dai kan yarinyar da zaka shigo da ita cikin zuri'armu ne zaka masa to ka tafi kai daya ba zan je ba." Abubakar ya ce, "Na rasa me yasa kuke tsoron Lamido haka, shi ba dodo ba ba komai ba, ni Allah kadai nake tsoron na sabawa ba mutum ba, zan je kuma zaka ji sakamako." Har ya fita Hashim ya ce, "To yaushe zamu je wajen Fadin?" Tsaki Abubakar yayi sannan ya yi gaba. Lamido ya tarbe shi cikin fara'a, ya ce, "Ubana ka iya zabe, domin ko da ni ka bari to da wuya na zaba maka irin wannan Babban kamu, lallai kun dace." Abubakar ya sunkuyar da kai cikin daure fuska ya ce, "Ni fa ba nine na ce ina son Fadi ba." Ya ce, "Duk wanda ya hada ku yayi maka gata." Abubakar ya ce, "Ni wadda na zaba daban, bana son Fadi." Ya ce, "To kila ka gaji takwaranka Mahaifina kenan, tarihi ya nuna mana duk cikin zuri'ar nan shine mutun daya taba auren mata 2 lokaci daya. Fada min wadda ka zaba ita ma yau akai mintinta, rana daya duk a sa su a lalle." Abubakar ya yi shiru, Lamido ya ce, "Duba, taso ka matso nan, ka fada min wadda kake so." Abubakar ya matso, ya dubi Lamido, "Wata yarinya ce a Kano, sunanta Hafsatu, bata daya daga cikin zuri'armu....." Wani wawan mari Lamido ya sakar masa da bayan hannu, ya mike tsaye cikin fada mai tsanani yana cewa, "Tir da kai, ba zaka surka mana Zuri'a ba, tunda muka taso zumunci iyayenmu suke yi, don haka muma ba zamu daina ba har bayanmu, don kana takama da boko, bokon banzanka, na yi tunanin shine yasa kake zagaye-zagaye, kana juyamu kamar waina (masa), to kaje da Iyayenka zan yi, don ina girmamaka saboda sunan Ubana, zan ajiye uban a gefe in kamata inci mutuncinka, baka wuce duka ba a gurina, FITA!!!!! Abubakar ya tashi ya fita. Kafin wani lokaci ya kira dukkan manyan 'ya'yanshi ta waya ya fada musu yana nemansu gobe da safe. Abban Abubakar yana jin kiran ya sha jinin jikinshi kan batun Hamma ne, domin Dada ta fada masa komai game da abin da Abubakar ya ce. Ummi ta shigo dakin yana ta sintirin kai kawo, ta ce, "Hamma!!!" Ya dubeta ta ce, "Ka ja surutu cikin dangi, ko a Makaranta surutunka 'yan uwa suke yi, wai ka canja hali yanzu baka da biyayya, ni kam ka yarda da Fadin mana." Abubakar ya kama hannun Ummi ya rike kam, "Tun farko ina rokon Allah ya bani macen da nake so, zuciyata ta san da Fadima, amma ta kama son Hafsa ranar da na fara ganinta, nasan kema zaki so ta Ummi." Ummi ta ce, "Hamma ina son duk abinda kaima kake so, sai dai bana son matsalar dangi, zaka yi kallon halin da su Dada zasu shiga, tunda kace Lamido yana nemansu." Ya ce, "Ki taya ni addu'a, so baya barin mutum ya ji tsoro, ni da kaina na fadawa Lamido batun Hafsa, jikina yana bani zan yi nasara, kullum cikin mafarkin Hafsa nake." Ummi ta ce, "Allah ya amsa." Lamido ya mike yana kai kawo a tsakanin 'ya'yansa wadanda suke zaune akan kafet. Dukkansu manyan mutane ne masu fada aji, domin wannan yana wane wannan ne a kudi. Ya dubi Mahaifin Abubakar ya ce, "Ibrahim dauki wayarka ka kira min danka Abubakar." Nan take Abba ya aikata haka, shima Abubakar nan take ya bar komai ya nufi gidan Lamido. Abubakar gabansa ya fadi ganin daya yiwa Iyayanshi kamar masu neman gafara. Dakin yayi tsit sai karar agogo, jiki a sanyaye shima ya zube tare da sunkuyar da kai, sai dai duk da haka bai ji a zuciyarshi cewa zai canja daga batun son Hafsa ba. Lamido ya ce, "Abubakar!!!" Cikin zafin rai ya ambaci sunan. Abubakar ya dago da kai ya dube shi, Lamido ya nuna su ya ce, "Su waye wadannan?" Abubakar ya kalle su ya ce, "Iyayena ne." Ya ce, "Da kyau." Ya ce, "To ina son ka fada musu abinda ka fada min jiya." Abubakar ya sake dubansu gabanshi na faduwa, musamman da suka hada ido da Baffa Magaji, Lamido ya ce, "Ka fada musu nace." Abubakar ya kasa magana. Ya ce, "OHO!!! ni ka raina kenan da ka zo ka same ni kafada min saboda ba nine na haifeka ba?" Baffa Magaji ya ce, "Ka yi magana mana, wane ne sa'anka a nan?" Abubakar ya ce, "Dama kan batun yarinyar da nake so ne, wadda ba 'yar cikin zuri'armu ba." Dukkansu suka hada baki gurin tambayarshi, "Me ka ce?" Illa Babanshi da ya sunkuyar da kai cikin matsanancin takaici. Baffa Magaji ya ce, "Kai ko Shaidanin yaro ne, zaka kawo mana sabon al'amari cikin zuri'a." Lamido ya daga ma Baffa Magaji hannu, sannan ya ce, "Ban taraku kwanakin baya ba na gaya muku cewar kar wani daga cikin 'ya'yayenku ya kawo mana wani sabon al'amari a cikin zuri'armu ba?" Duk suka ce hakane. Ya ce, "To lokacin ina zargin Abubakar zai aikata haka, gashi zatona ya zama gaskiya. Don haka yanzu kai Ibrahim tunda ka kasa tankwasa danka ba ka iya bashi tarbiyya ba, ina son ta bakin ka kafin kuji ta bakina." Abba ya nisa ya ce, "Lamido Allah ya huci zuciyarka, na jima ina fama da Abubakar akan wannan matsalar, sam ya ki bin umurnina, don haka ina son 'yan uwa da suke zaune ku zama shaida, daga yau na cire shi daga cikin 'ya'yana. Ina son Lamido ya cire shi daga cikin zuri'armu don girman Allah. Baffa Sa'adu ya ce, "Ina rokon alfarma gurin Lamido, da ya ba Abubakar dama muji uzurinsa kafin a yanke masa hukunci." Lamido ya ce, "Gashi ga ku." Baffa Sa'adu mai rike da sarauta a yanzun wato Mahaifin Hashim ya dubi Abubakar ya ce, "Dana fada mana dalilinka na son ka saki layin da ka same mu a kai?" Cikin karfin hali ya ce, "Baffa duk ciki ban samu mace mai irin halayen da kamannin da nake so ba." Abba ya ce, "Ka ji ko? In ba rainin wayo ba ace duk zuri'armu masu kyau da ilmi da tarbiyya amma ace ya rasa matar aure? Sai ya je yayo mana rore-rore?" Baffa Magaji ya ce, "Muna jin shi ai, ya fada mana irin matar da yake so muji dame yake takama." Abubakar ya ce da su Baffa, "Bana son macen da an kalleta za'a san kyakykyawa ce, nafi son baka kuma zuri'armu kusan duk kyawawa ne farare, game da batun halaye kuma, nafi son mace da bata cika wayewa ba, sai wadda bata cika buri ba, mai ilmi duka 2, mai tarbiyya da hankali da natsuwa, sannan kuma 'yar talakawa wadda za taji magana ta, ta girmama Iyayena da duk wani nawa, mai tsoron Allah a duk inda take, mai hangen na kasa da ita ba na sama da ita ba, wadda bata da rawar kai. Baffa kada ku yi zaton na raina tarbiyyar 'yan matan zuri'armu, ko ba za'a samu mai irin wannan hali a cikinsu ba, a'a za'a samu matsalar daya ce, ina son na auri wadda nake so kuma take so na, ba wacce take sona ni kuma bana sonta ba, Manzon Rahama ya hana auren dole, don yana da illoli, bana son a cikin zuri'armu akwai dayawa wadanda zaman hakuri da biyayya kawai suke yi, alhali babu biyayya ga abokin zamansu, hatta dan sabawa mahalicci." Baffa Magaji ya taso ya ce, "Wato auren zumuncin ne sabawa Mahalicci? To sarkin iya magana fada mana inda aka ce ya haramta?" Abubakar ya gyara zama, "Aure bautar Ubangiji ne, a duk lokacin da aka hada Ma'aurata dan dole ba so da kauna, to ba zasu yi wannan bautar ba yadda Ubangiji ya ce, maimakon lada sai kaga zunubi ya samu. Mu dauki misali da gidan Yaya Saleh, duk family ba wanda bai san tashin hankalin da suke ciki kullum ba, banda kuma sauran dangi da ba'a sani ba." Baffa Magaji ya ce, "Lallai Abubakar, boko ya sa ka fitsare idanunka, kana rigima damu saboda aurenka." Abba ya ce, "Duk wannan zantukan naka basu isa su zama hujja ba, tunda ba littafin da yai hani ga auren zumunci." Lamido ya ce, "Ikon Allah!!! Ashe tun ina da rai zan samu wani a zuri'armu da zaya kalubatanceni akan al'adarmu? Dole ne na dauki mataki, in ko ba haka ba in na mutu zumuncinmu rushewa zai yi." Abubakar ya ce, "Ku yafe ni, ba zan zama sanadiyyar rushe zumuncinmu ba, haske na zo mana da shi cikin zuri'a, ku kwatanta dani zaku gane nufina nan gaba. Ma'ana ku barni na auri bare." Baffa Sa'idu ya ce, "Abubakar mene ne dalilinka na cewa ba zaka auri mace mai kyau ba? Alhalin shine burin duk wani namiji." Ya kalli Abba, "Da ban san yin wannan batun ba, amma yanzu ya zama dole na fada, dalilai 2 ne suka sa nace ba zan auri mace dan kyau ba. Na 1 Yaya Mansur in baku manta ba lokacin da aka ce ya nemi Waslia bai ki ba, ya ce ko ba komai ai tana da kyau, da suka yi hadari fuskarta ta lalace, har yau ba wanda bai san irin wulakancin da yake mata ba. Abu na 2, lokaci mai tsawo daya gabata. (Abba ka yafe min abinda zan fada, ina dan yaro lokacin kun dan samu hargitsi da Dada, na ji kace mata abu 2 ne suka sa kake zaune da ita, na farko biyayya ga Lamido, na 2 dan kyanta da take da shi. Ta yiwu ka manta, kayi min afuwa
Chapter 8 · 0% Book details