← Book details Sanadin Boko Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 16

Sashe 11

Sanadin Boko Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanadin Boko 2-6 Posted by ANaM Dorayi on 11:25 PM, 19-Sep-15 Under: SANADIN BOKO "Ummi fa dole ta tsani auren Fadi, saboda ita bata da kirki, da ace ina da yanda zan yi to ba zan auri Fadin ba." Hashim ya ce, "Na kula ai da zaka yiwa Lamido musu ne, shiya sa nayi saurin amsawa." Haka suka yita hira har ya kaishi filin jirgi, yau dai da farin ciki ya nufi Kano, kuma baya jin zai samu matsala da Hafsat. Tunda bawan Allah nan ya tafi na kasa sukuni, ga rigimar Shadad yana Aunty Uncle fa? Tun ina cijewa har ta ni da kiran layin wayarsa, amma abin takaici ana fada min yana kashe. Daga bisani nayiwa kaina fada na watsar da lamarinsa. Shadad ya murmure ya koma makaranta nima na koma bakin aiki na. Na yi mamakin Manaja da bai ce min kala ba, su Ishak ma sai mamaki suke yi, na kuma ci gaba da zuwa makarantata. Tun mun horu da shan garin rogo, yanzun ma shi na jika ma a matsayin abincin dare. Na shimfida mana tabarma a tsakar gidan kasancewar lokacin zafi ne ga Kano akwai zafi. Muna cikin sha naji bugun gida, na tashi naje na tambaya wanene? Muryar da ban tsammace ta a lokacin ba ce. Ya ce ni ne Sadeek, jiki yana bari na bude, ta re da haska wayata, na ce "Sannu da zuwa, shigo." Ya shigo Shadad har yana faduwa garin gudu yana fadin "Uncle." Uncle ya daga shi sama, na kakkabe masa tabarma ya zauna.nakawo masa ruwa, nazauna ina cewa ina yini? Yace lfy, ya jikin shadad? Nace ya sami sauki. Don ya latsani yaji ko na damu dashi yace, shine tun da natafi ko flashig nace ai bakamin sallama ba,kuma wayar taka ai akashe take. Yayi murmushi, yau naga canji anty. Kina ta min fara‘a yau ba daure fuska ba harara, why? Nace ina sa ran zan sami lbr mutumin kirki a gurinka, wanda ya taimakeni tsawon lokaci da ya wuce, mutumin da ya fara gina karatuna, yace meyasa kike tsamanin samun lbr sa gurina? Nace, kun dibi kama, sannan kayi mun batun da yayi min a lokacin baya, wato na buga kudi, yace, fada mun yanda kukayi dashi, na kalmashe kafa. Na zaiyana mushi yanda mukayi da shi, yayi dariya. Banyi mamaki ba lokacin da yace, wai hafsat me na kara ne kika kasa ganeni. Alhalin ni kuwa tun lokacin da muka daukeki zuwa wajen buki rahama da sagir na ganeki, duk da da yarinyace kwarai kuma siririya, in kina yar gala-gala takar yar siririyar kafar ta karye. Nace dama kaine? Sunanka abubakar sadeek? Nce wallahi ban ganeka ba, idanunka dai in nakala sai inga kamar na taba ganinka, kai gaskiya fa tunda muka hadu kake taimako na, na gode Allah ya saka maka da mafificin Alkairi. Sannan ina so ka yafemun rashin kunya da rainin da nayi ta maka bisa rashin sani. Yace, nifa bakiyi min komai ba, asalima burgeni kikayi, ya kali kofin gari bance ki daina shan gari ba? Nace shi muke dashi, yace ina indomie da na sai muku? Ace ba ajiya ka bani ba? In zan kwana ban ci ba ba zan taba abin wani ba, yace naku ne fa, banaso muyi jayaya yasa nace maki nawa ne. shadad yace uncle bakace ka daina guduwa ka barni ba? Yace, tafiyar gaugawa ce ta sameni. Ya dube ni yace wannan zuwan na musan man dan ke, duk da zuwan da na dun gayi abaya suma dan kene, ki shirya gobe zamu tauna muhimmin zantuka zan shigo, nace to. Ya mike ki dafa ma shadad indomie, zakaci ko? Shadad yace eh, yace to ni zan tafi kada kayi rigima, zan zo da safe in kaika school. Yace, to uncle, suka rakashi bakin kofa sannan suka rufe gidan suka dawo. Tun da na kwanta bayan nayi shafa‘i da wuturi na kasa bacci. Tunanina wacce irin magana zamuyi? Nasani ba zaya wuce zai yi mun batun bayan rabuwa ba, domin nasan zaya iya cewa zai mai dani gida. Niko anawa ganin lokacin komawata gida baiyi ba, duk da ina ceke da son kannena, da yaya umar, harma da shi babanmu. Inna kuwa ita nafi son gani, ina so kafin na hadu da ita sai na zama wani abu a SANADIN BOKO. Zan wanke laifina zanyi abun da na kasa a baya, a fili nace banyiwa inna adalci ba, Allah kada ka dauki raina sai ka hadani da ita na roke ta gafara. Kuka ya kwace min, da dakina zaiyi magana da zaice yasani lokacin kuka na kenan.ringin din wayata ne ya ka tseni, na dauka ina kalon numbobin, nayi mamakin yanda na hadace numbobin shi aranar da na fara ganin shi. Nayi salama muryarsa kasa-kasa bani son ya fahimci nayi kuka, ya amsa kin soma baci ko? Nace a a yanzunan na gama shafa‘i da wutiri, yace shadad fa? Nace yayi bacci shi tuni. duk mukayi shiru har saida na duba naga wayar na kunne, nace kana jina? Yace ina jin ki, muryarki nake son ji ki min hira. Nace wace irin hira? Yace ko wace, ina jinki. Me kakeso mu tautana gobe? Yace wannan sai gani gaki, nace to Allah ya kaimu, yace amin. Yauwa, ummi tace in gaisheki, bansam me yasa naji faduwar gaba ba, nace wacece haka? Yace kanwata, itace autarmu. Nace to ina amsawa. Ya akayi ta sanni? Yace, duk dangina sun sanki, labarina ka basu? Yace, eh, to me kace masu? Yace, zan fada maki shi gobe. Nace, to wai meyasa ka damu da ni tun farkon ganina ina yariya kake ta taimako na? Yace kila Allah yayi nine kawai don in taimakonki, kila watarana kayi min gori, shiyasa bana karbar taimakon maza, ko kasa in saka maka da wani abu wanda bani da izini a kansa. Yace, me kike nufi? Yaci gaba, kada ki damu kanki, ni bakince rance nake baki ba, zaki biya ni, nace dame zan biyaka? Naci gaba da cewa, kai baka cikin wadanda zasu cuceni, kai na daukeka yayana ciki 1. Yace a a kada ki dora min dutsin da zai shiga tsakanin halas da halas, nace kamar yaya? Yace sai dai nazo gobe, yace kiyi bacci dani a ranki zakiyi mafarki innazo kifada min, goog night. Ya kashe wayar. Nayi shuru ina so in tono abubuwan da mika tau tauna, amma na kasa, illa kalmarshi ta karshe da yace kada nashiga tsakanin halas da halas, dan kawai nace shi yaya nane na daukeshi uwa daya uba daya? Kamar yanda na saba duk bayan sallah asubahi sainayi azakar, haka da magariba. Yanzuma na gama namike na cika bokiti daruwa na nufi wanka. Da nafito nazo na tashi shadad, yana bude ido nace mashi adu‘ar tashi daga bacci kada ka manta. Nan take ya karanta. Na sunkuce shi sai bayi, nai masa wanka nasashi yayi alwala, na zura mashi jallabiyar sa mai gajran hannu wanda na sai masadon yin sallah. Nace to maza yi sallah kuma kayi adu‘a yace to. Na koma na dauko sabulun da mukayi wanka dama na wankine nazo na wanke muna kayanmu, cikin raina ina mitar kayan shadad duk sun kode inna sami kudi zan sai mai wasu. Tsaf na shiryashi cikin kayan makaranta na dafa mashi indomie, na share ko ina gyara. 7 da rabi na gama komai, sai kurum naji bugun gida, nazaci dan a daidaitana ne sai da na bude naga Abubakar tsaf cikin riga da wando blue jeans, riga baka. Takalminshi sau ciki bakake, sumarshi tanata sheki baka wuluk. Kamshin turaren jikin shi ya cika gurin, ya shigo shadad ya kwaso da gudu ya nufo shi. Sama ya dagashi yana cewa, serious student, har ka shirya? Nace, bari nayi maka shin fida. Yace a a zo mu kaishi tukunna. Na saka hijabi muka fita, muna direshi a makaranta yace min shifa yunwa yakeji, nace to yanzu yaya za‘ayi? Mukoma gida inmaka indomie. Yace an ta cin abu 1 kenan? Muje gurin abinci nikam yau masa zanci, nace nifa bana son abin siya, nafi son komai inyishi da kaina, yace zakiyi min masa? Muje kasiya lokaci ya kure.a zatona in yasiya gidanmu zamuwuce, sai naga mutum ya nufi wata hanyar, masaukin sa ya kaimu na dube shi gaskiya sadeek ba zan shiga hotel ba, babu mutunci gareni matsawar aka gani cikin nan. Yace nafiki kishin hakan, ba dan dani bane zamu shiga nan ba zan aminbe ki shiga ba. Muka shiga daki tamkar a gidanka. Ya zauna wai muci waina, nace a a ba zanci ba. Yayi nace ni bana cin masa, nama karya fa. Yace ban yarda ba kice dai kina jin kunyata, nace nifa na kosa inji maganar da zamuyi, inada kagara. Yace, bari in gama. Sai da ya koshi ya dora da ruwan shayi da yasa aka kawo masa, sannan yace to kafin inyi maganata, zanyi maki tambaya 1 rak! Nace to, kina da aure? Nace a a, yace to gaskiyar magana ba wata kwana ko dogon turanci, ina sonki zan aureki nan da yan watannin da basufi 2 ba....da sauri na mike saboda zantukan da naji suna yawo a kwanyata, na nuna shi, kana sona? Ni kake so? Na bubuga kirjina, yace com down my hafsy, ki tsaya mu fahimci juna. Jikina ya soma bari, jin ya ambaceni da hafsy, sunan da munnir ke kirana dashi, da ina son sunan aman yanzun in da sunan da na tsana to shine. Nace, nina sani, dole dawainiyar da kayi ka nemi ka fanshe, to karya ne kakeyi ba kai bane wannan bawan Allah mai tai mako don Allah, kaima cutata kake sonyi. Da gudu na nufi hanyar fita ban san ya akayi ba kawai na tsince shi gaba na yayi key din kofar. Yace, ki saurare ni, bana nufinki da komai sai Alkairi, nace bana so. Jikina kake bukata. Tsaki yaja ya koma ya zauna yana kallona, na jingina da kofar ina kuka, har na gama bai hanani ba. Yanata dan ne dannen wayar shi, nagaji nace ka bude mun kofa, yace in kinga kin fita anan to kin saurare ni, kuma amsar cewa kina sona zaki aure ni, nace bana sonka. Yayi murmushi, karya kike kina sona, haushi ya kara kamani, nace ni bana sonka, Allah ka
Chapter 11 · 0% Book details