← Book details Sanadin Boko Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 16

Sashe 6

Sanadin Boko Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaharaddeen Shomar
whatsapp. 08168575100

Sanadin Boko 2-3
Posted by ANaM Dorayi on 07:34 AM, 19-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Abubakar yayi shuru, yayin da jikinshi yayi sanyi lakwas.
Al‘amarin mai girma ne, yace dada kada ki damu, zanje
gurin lamido amma ina so ku daina fushi dani. Tace to
mu dama fushin mu don kaki bin abin da muke so ne, da
kabi shi kenan mun huce. Yace to zanyi duk me kuke so.
Har zuciyar shi ya san ya amsa ne kawai, amma ba dan
zai je wajen lamido da batun a zaba mashi mata ba, zai
jene da batun wanda yake so amma sai yaje kano ya
dawo. Tun dare ya shaida wa mahaifan nasa cewa zai
shiga lagos a gobe, don tau taunawa da wasu abokan
kasuwan cin sa a bisa wata cinikayya da zasu yi. Sukayi
masa adu‘a da safe karfe 9 ya hau jirgin kano. Sai da ya
huta a masaukin shi sannan ya daga waya ya kira layin
sagir yace yana kamo don Allah ya kawo masa mota.
******* ******* *****
Tun dare zazzabin shi ya tsananta, kwana mukayi babu
bacci, gashi bani da ko parasitamol bani da kudin saya
cikin yan satitikan tsananin babu ta dameni, jiya ko girki
banyi ba. Da dadare garin rogo muka sha muka kwanta,
jikin sa ya tsanata sosai da safe har da safe har ta kai
numfashin sa na futa dai dai. Nace ka bari dai in watsa
ruwa sai mutafi asibiti tunda kan da kati, ko da bani da
na mota, ina saka hijab na lura ya mike idanun sa sun
kafe hakoransa suna datsewa, dukda ban san suma ba
tabbas suma ne wannan. Cikin matsanancin tsoro da
firgici na sunkuce shi da gudu nayi waje ina fadin
innalilahi wa inna ilaihir raju‘un! Kamar daga sama na
ganshi tsaye jikin mota, da gudu na nufeshi ina cewa, ya
mutu! Ya mutu!! Da sauri ya karbe shi yasa a mota bai
jirani ba ya figi mota kamar dama abinda yake jira
kenan. Na koma cikin gida ina zagaya ina kai kawo,
kusan awa 3 sannan naji tsayiwar mota da gudu na fita,
shi kadai ne ya fita fiskar shi mur tuk, ko bai fada ba
nasan shadad ya cika.da gudu na juya cikin gida ina
kuka, hakika nayi rashi. Na zube kan katifa nayi kuka na
gode Allah, sai nace Allah yasa mai cetona ne. Ina
fitowa sai nagan shi jingine a bango, na daure nace ka
daukosh bari naje na fadawa su maman rahama. Yace ki
ce musu me? Ya rasu mana, yace inji wa? Na kara
matsawa kusa dashi me kake nufi? Yace ya far fado
nazo ne in kaiki gurin shi. Likita yace typort ne ya
kamashi da kyau. So, yanzu in kin gama kukan ki shirya
ki dauki duk wani abu da zaku bukata a can. Yan kayan
shi kawai na diba, sai nawa guda 2, da daudumar sallah
da alkur‘ani. Na fito yace kin dauki komai? Na ce eh.
Amma kafin muwuce bari na sanar da maman rahama,
kada suji shuru. Yace to ina jiranki a mota. Sai da na
kule gida sannan naje. Asibitin kudi ne mai tsari dakin
mu kadai ne har da kayan kalo ga na‘ura mai sanyaya
daki da taruwa. Na kafe shadad da idanu, duk ya rame
yanata bacci. Hawaye sai sauka suke a idanuna, yace
min yana zuwa. Bayan fitarshi likita yazo muka gaisa, ya
tambayi mai jiki nace da sauki, yace bai tashi ba ko?
Nace eh yace to idan ya tashi ki bashi abinci ko da
ruwan tea ne, sai ki bashi magungunan shi an siyo?
Nace banga ta kardar maganin ba ai, yace tana hannun
baban shi, yace dan Allah kada kiyi masa wasa da
magani, nace to. Yana fita na soma tinanin ina zan sami
kudi? Gashi ko abincin da zan bashi bani dashi in ya
tashi. Nace oh Allah na gode maka a wanan hali da kasa
ni, Allah ina mai naiman sauki a gareka. na dauki wayata
na kira Rahama na fada mata muna asibiti an kwantar da
shadad, tace taji gurin Abubakar, gasu nan zuwa dashi
da sagir ma. Kusan minti 25 da yin maganar mu sai
gasu. Rahama ce gaba dauke da katon kwando da
kulolin abinci da filas na ruwa zafi, Abubakar da Sagir
suka shigo da ledoji. Ya nufi yar durowan da ke gefen
gadon ya jera kalolin jus ne da ruwa. Sannan sai magun
gunan shadad ne ya zuba su a wani kwando dake jikin
gadon, kila an tanade shi ne dan zuba maganin dama.
Sagir ya koma ya shiga da dadduma mai girma, ya
shinfida ta can gefe suna fiskantar gadon, rahama ta
dauko kwandon ta zuba musu da fadukan shinkafa da
kayan lambu, sai farfesun kifi. Ta zo ta daukar musu
ruwa tana cewa bari na sashi a fridge saboda naji babu
sanyi. Ni dai sai bisu nayi da idanu. Rahama ta dube ni,
bari in sa mana, nace zuba dai dai cikin ki. Abubakar
wanda ya zauna saiti na da na dago fiska sai mu hada
ido, na daure fiska Rahama ta sani ni magana 1 nake yi
shiyasa bata matsa min ba, ta zuba nata ta juyo kujera
kusa dani, ina bakin gado ne ta soma ci. Ya kurbi ruwa
me yasa ba zaki ciba? Na dan tsuke fuska, sannan na
dube shi haka kawai. Ya kali kofar shigowa, kamar mai
nazari. Can ya sake duba na, amma ba don kin karya ba,
kuma ba don baki jin yunwa ba?ban karya ba kuma ni
bance bana jin yunwa ba. Rahama ta ce, Alhaji abubakar
dama ka barta, domin duk abinda tace tana nufin hakan.
Abubakar ya dubi Rahama, yace kina nufin bata
karyawa? Rahama tace a a ina nufin duk maganar da ta
fada ba zata canja ba, shi ne dalilin da yasa kaga da
tace ba zata ci ba, ban matsa mata ba. Ya ce ok. Duk
kamshi ya cika dakin sagir da Abubakar kasa kasa suke
hirarsu. Wayata ta shiga ruri, nayi tsam tare da son in
tashi taro da son inhasashi ko wanene, ina dubawa sai
naga number super markert din mu. Gabana ya fadi, sam
na manta da wani aiki. Ida nuna suka kai kan Abubakar,
ya kafe ni da ido da alama yana so yasan wanene ya
kirani? Nikam a zatona manaja ne, na daga da sanyin
jiki. Ba muryar shi ba ce, nace ishak ne ko musa? Yace
ishaq ne yace munjiki shuru ne kuma manaja yace baki
ce bazaki zo da yanma ba, tun dazu yace kina zuwa ki
sameshi ofis. Ya numfasa yace ranshi fa ya baci, wai shi
kin soma isarsa. Nace ishaq don Allah kace yayi min
uziri, yaro nane ba lafiya duk na rudene shiyasa ban tuna
da aikin ba, yanzu haka muna asibitin anbashi gado.
Yace to kikirashi ki fada mishi, dan kada ya gane nine na
kiraki. Nace to na gode. Na dafe goshi na, Rahama tace
ya akayi? Kin san cewa na manta da batun aiki? Shine
Ishak ya kirani. Na shiga dan na wayata ina son in duba
account dina, duk da nasan bani da kudi, ko ina ziro ziro,
nashi gshi bani da kudin ma da zan kira manaja sai in na
sa.
Rahama ta ce ga wayata ki kira shi, na harare ta kina
hauka ne, zan kira wani namiji da wayar ki, bayan kinyi
aure? Ta ce to menene, ba da nima Ogana ne ba? Nace
sam, da kika ce, ki tuna mijinki har canza maki layi yayi
don kada mutane su dinga kiranki, kuma hakan yayi
daidai, don ya nuna kishin ki.
Yanzu sai na kira Manaja? Alhalin yanzu baki da wata
alaka dashi?, tace to naji. Sagir wanda bansan suna jina
ba, yace a to fada mata gaskiya. Na dube su, idanun
Abubakar su suka sa na sunkuyar da kaina.Yace, "ga
wayata ki kira, na girgiza kai, ka barshi na gode, ya shiga
danna lambobi, ban sani ba sai naji yana cewa Manaja
yarinyar nan Hafsa tana da uzuri, don haka bazata samin
zuwa aiki ba sai bayan wani lokaci da bazata iya cewa
gashi ba, don haka tana son uzuri.Na tsura masa ido, a
raina ina cewa ji mutum zaya balgace min aiki na, bayan
dan shiru kadan da yayi sai yace, to shike nan. Ya dube
ni "menene na zare min ido? Ya yarda, nace na gode.
Amma ba haka ya kamata ka tambaya ba saboda
shugabanane a gun aiki. Ya ce yanzun nayi laifi kenan,
na girgiza kai alamar a'a, sannan nakai dubana ga
Shadad.Sai bayan munyi Azahar sannan ya farka, naba
bashi tea. Abubakar ya bashi magani, naji dadin yanda
ya bashi don ni idan na bashi kuka da su amai yake yi,
amma shikam ya bashi cikin lallashi kuma yasha. Amma
sai yace masa Uncle bazaka kara guduwa kabarni ba, ya
ce eh amma sai kasha magani.
Cikin rawar jiki yasha, na kanyi al'ajabin irin son da
Shadad yake yiwa Abubakar, domin ba shine mutum na
farko da ya fara masa magana ba, bai taba zuwa gurin
kowa ba sai shi.Sun fita sai ni da Rahama na kasa rike
abin da ke ciki na nace, Rahama wai me wannan abokin
mijin naki yake nufi da ni ne? Ta ce baki tambaye shi
ba? Na harare ta in ya bani amsa zan zo ina tambayarki
ne? Na jima ina tambayar sa bai bani amsa ba nifa
gaskiya bana son shishigin nan ki fada masa.
Ta ce ke me ya hana ki fada masa, ta gyra zama Hafsat
ki nutsu da kyau ki lura. Abubakar yana nemanki da
alkhairi ne, koda bai fada min ba nasan kila sonki yake.
Na dubeta da wani irin kallo cike da masifa nace sona?
Don Allah ki daina wannan sabon, in har yayi kuskuren
furta min kalmar so ai sai yayi nadamar yin hakan.Tace
maida wukar, tambayar ki zanyi. Cikin harara nace, ina
jinki, ta ce kina nufin laifin Munir ya shfi sauran maza?
Tsakani da Allah zaki bani amsa, na ce kusan haka ne, ta
ce kina dai da ilimin addinin musulunci, ance laifin wani
yana shafar wani? Na ce baya shafa amma na dade ina ji
a bakin iyaye na cewa maza ba yan goyo bane maza
rigar kaya ne, maza basu da tabbas, maza mugun ice da
dai sauran sunayen da ake kiran su da su, da ban yarda
ba sai gashi namijin yayi min, don haka ni layi guda na
ajiye su.
Chapter 6 · 0% Book details