← Book details Sanadin Boko Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 16

Sashe 5

Sanadin Boko Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

so yanzun nan ka shiga cikin 'yan matan nan yanzu ka fitar da mata ka, nasa ranar auren ka wata biyar daya ga watan. In kayi lissafi zai zama wata hudu da kwana goma sha biyar kenan, kafin lokacin kun fahimci juna." Nan da nan dangi suka sheda suka shiga murna, shi kuwa gurin zaman shi ya koma. Hashim yace tashi mu duba, yace dan Allah ka bar ni ka ji." Haka taron ya tashi ba tare da Abubakar ya zabi mata ba, hakan ya kona ran mahaifansa da Lamido, daga bisani kakarsa Gogwal kodai bashi da lafiya ne? A bincike shi, sun tsare shi ya ce shi kam lafiyar shi lau, amma bai samu kawai mai irin halayen da yake so bane. Cikin bacin rai Lamido ya ce sun zura masa ido amma ya sani rana baza a daga ba ko ya sami mata ko bai samu ba, in lokacin yayi zasu daura aure da duk wadda suka ga dama. Abubakar kuwa ko a jikinsa, cikin hakan ne bikin abokinsa Sagir ya taso a Kano, yaje yayi arba da yarinyar da ya santa a Kaduna lokacin da yaje (Bautar Kasa), tana talla mai yawan wasa, kusa shekaru goma baya. Yana son sanin abubuwa game da yarinyar kuma yana jin wani abu a ranshi game da ita, sai dai abin tambaya ta tara halayen da yake so matar shi ta kasance? Ya iso gida daga gida Hashim, gaban iyayan nashi ya zauna a kasa, Abban ya dube shi yau in ni na haife ka ina son ka fada min nufin ka damu. Dada tace dazun su Yafendon shi da suka zo dukan su kowa na cewa yazo ya sasanta da 'yar gidanta, na ce masu dai kun sanshi in ya yarda shike nan, amma fa ni bazan maku alkwarin ko ya yarda ba. Don haka ka fitar da mata kada ka hada ni da 'yan uwana, Abba yace yama fada mana nufin shi kawai, in yana da wata matsala ne sai ya kawo uzurin sa muji, in ko lafiyar shi lau to raini ne da walakanci, baka jin kunya kannan ka duk sunyi aure cikin dangi ko ina lbarinka ake, fada min nufinka." Ya danyi dim don yasan abinda zai fada yanzu zaya girgiza su. Dada kayi magana mana. Ya dan numfasa yace, naga wadda nake so." Abba yace, ko kai fa, fada min wacece yanzu na sanar da Lamido ta waya." Yace tana Kano." Suka hada baki gurin cewa, Kano? 'Yar gidan Goggonka Furera?" Ya ce a'a ba dangin mu bace. Suna hada baki gurin cewa, ba dangi ba? Eh, ya dago ya dube su, ba zato sai yaji saukar mari gefe da gefe, sannan ta rufe shi da duka. Sunkuyar da kai kawai yayi tayi ta dukan shi. Abban su kuwa sunkuyar da kai yayi ba tare da yace Dada ta daina dukansa ba, har sai da ta bar shi don kanta. Cikin tashin hankali take cewa ba zaka jawo mim abin fada a cikin dangi ba, kai ne mutum na farko da zai kawo matsala a zuri'ar mu? Tur! Ba dani za a yi ba, ta fice daga falon rai bace, yana nan zaune Abba yace kasan dai kazo da abin da bazai yuwu ba ko? to ka cire wannan tunanin a ranka in dai kana so kaci gaba da zama danmu. ya mike shima ya fita dàga falon, Abubakar yana zaune cikin halin da baza yace gashi ba, yafi awa daya saññañ ya fito ya tafi dakinsa. washe gari sam iyayen basu amsa gaisuwar sa ba, wannan lamari ne mai girma. Ya zama dole ya faranta ran iyayan sa, yasan idan tasu ne zai iya shawo kan su, tsoron lamido da sauran dangi suke yi. Shi kuma yana so ya kawo karshen wanan auran, domin wasu na cutuwa, an hada su da wadanda basu so. Sannan ko mai mace zatayi wa namiji ko shi yayi mata babu rabuwa, yasan ba wai haramun bane auran zumuncin, to amma yanda zuri‘arsu suka dauke shi tamkar ibada, shine yake son su gane auren bare ma ba haramun bane. Akan gadon shi yake ta juyi tare da neman mafita, ya kalli agogo 11 a fili ya furta Allah yasa hashim bai yi bacci ba, ya daga wayar sa yasa a kunne, bayan ya laluba num hashim din. Tayi kuka har ta katse ba‘a dauka ba, don haka ya ajiye wayar yana miyar hashim har yayi bacci sai kace mace. Kusan minti 30 wayarshi ta soma ruri, ganin sunan hashim ya daga da wuri,ya soma korafi ka cika baci kamar mace. Hashim yace ina tare da iyalina ban san tayi ringin ba, duk da tana kusa dani in ka fahimce ni ka kira lokacin ina duniyar ma‘aurata, bana tare da ku. Abubkar yace ban tam bayeka ba, sannan Allah dai ya tsine ma mai tona asirin iyalansa, don haka sai kai hattara. Kasanan dalilin kiran da nayi maka? Hashim yace sai ka fada? Abubakar ya gyara kwanciya sannan yace, kila kaji mamakin cewa wadda nake so ba a cikin zuri‘armu take ba ko? me kake son fada mun? Hashim ya mike ya nufi falo dan kada matarshi shatu taji abin da zasu tau tauna. Kada kace zaka shugo da bidi‘a cikin zuru‘ar anan, kasan hakan zai jamaka matsala kai da mahaifin ka? Abubakar yace haba hashim kai fa ba jahili bane, abinda kake kira bidi‘a ba haramun bane. To auren zumunci sunna ne? Ka fada mun a matan monzon Allah wacece yar uwarsa ko a kwai bata wuce guda 1 ba, kuma duk matansa yan kabilar sa ne?Dashi fa muke koyi, don haka matar da aura ina nufin ba haushiya ce, ina zoton ma ba zawara ce, kaga kenan zanyi sunna. Hashim yayi tsaki, wannan karan bana tare da kai, matsawar baka canja tunani ba. Me hausa sukafi yaren mu na fulani? Kyau ko asali? Abubakar yace look! Hashim ka fahim ceni sosai, ba al‘ada ce a gabana ba, addini nake son awa agabana, yarenmu suna da kyau da asali da kuma tarbiyya, amma ban ga wadda tatara irin halin da nake so ba. Ok inji hashim. Ita wannan ta tara duk abin da kakeso? Abubakar ya tashi zaune, ba zan saniba sai dai na ga 1 daga ciki, saura sai ta bani dama mun zanta. Hashin yace kana nufin baku taba zantawa ba? Abubakar yace ni ke sonta, ita bata san inayi ba, domin bata so in kusanto ta, na dai taba sanin ta da. Hashim dan Allah ka natsu, ina so ka taimaka mun yanda zan shawo kanta, zanfi tsayuwa kan ra‘ayi na inna tuna wanda nakeyi dan ita, ta san ina yi. Hashim yace, abinda zai fi kaje ka fada mata nufinka, ka ce mata kana sonta kuma zaka aure ta, na san zata girmama zan cenka don matan da suka san abin da suke yi, suna girmama zancen aure. In dai ba wani ya riga ba. Abubakar yace ta tsani maza, ina zaton namiji yayi mata laifi. Hashim yace kaje, in baku sasanta ba ka sanar da ni, sai mu koma tare. Kai dai kasan yan da zakayi mahaifanka kada su shiga fushin lamido. Yace zan ga me zanyi. Sukayi sallama. Arana ta 3 ce daada ta shigo dakin shi, da wowarshi kenan daga office, tace ka sauya ra‘ayin ka ne ko kanan kan bakanka? Ya kwantar da murya. Dada kiyi hakuri, wlh wace nake son aura musulma ce mai tarbiyya. Tace amsa kawai zaka bani, ba. Tace amsa kawai zaka bani, bana son dogon turanci, ya ce to duk yanda kuke so haka zanyi, tace uhm! Isa da kai kaje ka cire mata a dangi, ta tausasa murya, da zakaji tawa ma, ka sami lamido ka fada mashi ya zabo maka. Na tabbata zaka wanke lefukan da kowa ke ganin ka dashi. Muma zaka ciremu a zargin da lamido ke mana, na san baka sami lbr mitin din da lamido ya kira su abban kuba ko? Ya dube ta, na sami labari sai dai ban san abun da aka tau tau na ba, duk da nasan dan ni akayi shi. Tace to ya tara yayan shi maza ya sanar dasu cewa bai yafe ba duk wanda ya bari dan sa ya kawo bakon lamari a cikin zuri‘armu ba, yace za‘a yanke mumunan mataki a kanshi da yayan ta hanyan yanke zumunci da su
Chapter 5 · 0% Book details