← Book details Sanadin Boko Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 16

Sashe 16

Sanadin Boko Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100

Sanadin Boko 2-08
Posted by ANaM Dorayi on 11:28 PM, 19-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Domin sonka ya shigeni ne a lokacin da nake tunani na
ha'ka dogon rami na saka so a ciki na rufe shi, ina fatan
kowa ya mutu ya huta. Amma abin bakin ciki sai da ya
fito har ya zo ya kama ni, a bisa adalci Abubakar bai
cancanta na zam matarka ba, matsayinka na kamili, kada
ka so kaji dalili ko ka matsa min na fada maka." Na kifa
kaina a tsakanin cinyoyina ina kuka irin wanda yake sa
jiki motsi, gidan ya yi tsit, gidan shiru kamar ba
mutane.Abubakar ya ce, "Malama ki nutsu ki fiddamu
daga tunani." Hashim ya ce, "Baiwar Allah ki nutsu ki
mana bayanin komai, da kin san irin son da wannan
bawan na Allah yake miki hakika da baki masa haka ba,
ni abokinsa ne kuma dan'uwansa ne na jini, Mahaifina
wan Mahaifinsa ne, tare muka taso kamar 'yan 2, ya san
sirrina haka na san nashi, tunda muke da shi ban taba jin
ya ce yana son 'yan matan da suke nacin sonsa ba, na
kosa na ganki mai sa'a." Na dube shi na ce, "Ina son sa,
kuma ina matukar farin ciki ace na samu mutum kamar
Abubakar ya zama Uban 'ya'yana, amma kash!!!" "Amma
kash me?" Sagir ya ce, "Dan Allah ki daure ki fada mana
Insha Allahu za'a samu mafita."
Na mike tsaye, "Ba wai ka aureni ba, da zarar ka ji
matsalar, sirri ne zan fada muku." Na yi shiru, na yi ajiyar
zuciya cikin kudurin gaya musu, "Amma ina so na gaya
maka Abubakar ina sonka, kuma duk lokacin da ka tuno
da ni ka tuna cewar na soka, zan ci gaba da sonka har
karshen rayuwata."
Na kalli Hashim na ce, "Za ka so dan'uwanka ya auri
karuwa? Wadda ta bar gidan iyayenta saboda cikin
shegen da tayi? Ta shiga duniya tana zaman kanta?"
Abubakar ya mike zumbur ya ce, "Cikin in, in, wa? Wa
kenan kina nufin ke karuwa ce? Cikin shege kika yi kika
haifi Shaddad?" Na ce, "Kwarai kuwa, ciki nayi."
Ban ankara ba naji saukar mari wanda idanuwana suka
daina gani na wucin gadi, ya ce, "Tur da haihuwarki, kin
cuceni da kika bar ni na fada son ki, Allah ya isa!" Ya
fice fuuu!!! Sagir da Hashim suka bishi.
Shadad ya farka a gigice sakamakon kukan da na fasa,
na zauna kasa ragwab, ya zo ya fado jikina muna kuka
tare da ina fadin "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.
Allahumma ajirni fi musibati wa'akhlifni khairan minha."
Mun yi kuka ya ishemu, amma har daga bisan Shadad ya
yi bacci, ni kuwa tuni zazzabi ya rufeni hakanan hawayen
idanuna bai kafe ba, abin da nake tsoro kenan rabuwa da
Abubakar gashi nan kuwa, Ya Allah! Ya ma aka yi na
fada masa zancen a baibai?
Kafin safe ko motsi na kasa yi don zazzabi da ciwon kai,
Ga fuskata ta kumbura sumtum saboda marin da
Abubakar yayi min, ga kuma kukan da nayi, haka muka
kawan gidan ko sakata ban iya samu na sa ba saboda
azabar ciwo.
Da asuba da kyar na iya tashi nai alwala, a zaune na yi
Sallah, Shadad ma Sallah kawai yayi dan ba zan iya yi
masa wanka ba, har 8 ina kudundune ban san me zai
biyo baya ba.
Shin Abubakar zai iya rabuwa da Hafsat? Ko Munnir yana
sane da cikin da yayiwa Hafsay? Baba fa da bangaren
Inna kuwa suna ganin Hafsa?
Duk amsar tambayoyin nan
Sae kun biyo mu a littafi na 3
Godiya gareku

Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100
Chapter 16 · 0% Book details