Sashe 12
Sanadin Boko Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bude mun kofa in tafi abina.Maimakon amsa da naga ya mike ya nufi gadonsa ya cire rigarsa da farar singileti, ya hau gadon ya kwanta, kauda kaina nayi ina tura baki, ina cewa indai sai nace ina son ka sai dai mu shekara a haka. Wasa wasa har lokacin sallah yayi, ina kallon shi lokacin na gaji da tsayuwana tsuguna, yayo alwalar shi ya tada sallah. Nazo kan gadon na dinga neman key har ya idar ban gani ba, na koma inda nake, ya kira wayar Sagir wai don Allah ya fadawa Rahma karfe biyu taje makarantar su Shadad ta dauko shi ta tafi dashi gidansu, mu munyi tafiya. Ya dube ni, ki shiga kiyi sallah, na ce in naki fa? Ya ce ki gamu da Allah. Ya fada kan gadon shi ya ci gaba da bacci. Ina ta neman makullin ina sanda, amma Allah baibani ikon ganin sa ba, don haka naje nayo alwala nayi sallah. Ina zaune ina tunanin anya kuwa wannan dan tahalikin cutata zaiyi? Amma bari ya tashi na gwada yi masa dabara duk da naga shima kar yake kallo na, amma da macucci ne da tuni ya aika abinda zuciyarsa take so. Daf da la'asar ya farka, ya shiga bayin nake zaton ruwa ya watso da naga ya jima kuma ya shiga da wasu kayan, ya fito yayi sallah, sannan ya ce nifa ina jin yunwa. Na hada rai na ce to ni ina ruwana, ya ce ke mijinki yana jin yunwa zaki ce ina ruwanki? Na ce ni dai ka bude ni in tafi. Ya kira waya wai a kawo masa jalof din shinkafa da farfesun koda. Ya dube ni me zaki ci? Na ce nidai burin in bar nan, ya share ni. A raina na kudurce ana kawo masa abincin zan fice koda tsiya, amma ana danna kararrawar kofar sai naga ya zuge gilas din window yayima ma'aikacin magana ya amsa, ya zauna yana ci yana waya da Hashim cikin fillanci jifa jifa yakan sako hausa, anan ne na gane zancena yake yi, lokacin da yake cewa Allah Hashin in zamu shekara anan sai randa ta saurare ni zata fita, ya sake juyowa ya ci gaba da fillanci. Ni kuwa nayi zugum kamar wacce take neman gafara, ganin yamma tana kara yi bansan abinda zai biyo baya ba idan dare yayi, don haka na ce bari na saurare shi, kafi sannan bari na gwada dabarata ko da lalata yake sona. Sai da ya gama wayar na ce to naji zan saurare ka, amma banda yau. Don yau ina azumi ne, in ma jiki na kake so ka bari gobe zan baka. Ya dube ni da sauri, jikinki? Ina jikin kin yake? Ya ja tsaki banga jiki anan ba, ni ke nake so, zatinki na ke so ba jikin ki ba, kin tsaya kina zabga min karya wai kina azumi. Ki tsaya muyi magana shine mafita, amma har wani jiki kike dashi? Na ce in ba jikina ba me kake so? Ya ce halayenki da ke kanki nake so, inna sauraroka, yi batunka. Ya ce tashi ki matso nan dan bazan iya daga murya ba kamar fada. Na dan matsa ya ce bana bukatar sai kince kina sona, na riga naga sona a idon ki, fada min inda su Baba suke in tura magabata na, nayi shiru, tunani nake ga garin zuwa amma babu zanin daurawa, lallai zanso haka sai dai nasa in Abubakar yaji labarina bazai aure ni ba. Sannan in shi ya yarda iyayen shi baza su yarda ba. To ni da na shigo duniya ma yaya za'ayi mutum mai mutunci ya aure ni? Yanzun ma ina zan san inda iyaye na suke? Tunda nasan ba gidan kanshi yake ba, gidan haya ne kila yanzun ya tashi... "Ba ki bani amsa ba." Ya katse ni. Na ce ni fa kaga ka kyale ni, bazan aure ka ba, ya ce nasan kina tunanin ki fada min kin taba aure kada in ce bana son bazawara, to kin min kuma zan aure ki a haka. Shike nan? Takaici ya sa wasu hawaye zubo min, nace a raina da na taba aure me zai hana ni fada?" Ya ce ki fada min damuwarki bana son kuka. Na ce, ina rokon wata alfarma a gurinka, don Allah ka zauna a matsayin yayana, mai bani shawara in bukatar hakan ta taso, ka zam mai min fada a duk lokacin da nayi ba daidai ba, na dube shi in nayi abin duka ma ka doke ni....." Na fashe da kuka tare da sa kaina cikin hajabi. Ya zo ya tsuguna a gabana, ban sani ba sai da naji muryarsa dab dani. Abin zaifi armashi idan kika amince na zama mijinki majibancin lamuranki, mai saki cikin farn ciki, mai kare lafiyarki da mutuncinki, hanyar shiga aljannar ki. Hafsat ina so da kaunarki, ki amince. Wallahi nasha alwashin zama dake har karshen rayuwata, bazan sake ki ba yanda mijinki na baya yayi, zan rike danki tamkar ni na haife shi." Na dago ina kallon shi, shi zatonshi na taba aure mijina ne ya sake ni, ina ma ace haka ne? Da tuni nayi magana. Na ce kayi hakuri duk ba wannan bane, don Allah ka kyale ni kawai yanda ka ganni." Shima shiru yayi. Can ya ce. "To naji, yanzun ki fada min inda mahaifanki suke kawai." Na ce ban sani ba, wallahi ban san inda suke ba. Ya ce to shike nan share hawayen naki in maida ke gida. A cikin mota ni dashi kowa tunanin shi daban. Motar tsit kamar babu kowa a ciki. Shi a tunaninshi kila bayan nayi aure baban Shadad ya sake ni nabar gida, kila Iyayena suna son in koma gidan mijina ni kuma naki. Ni kuma tunani na shine zanso matuka Abubakar ya zama mijina, don wannan gata ne Allah yayi min in dai na same shi a matsayin miji. Amma nasan da wahala in zai ji labarina ya aure ni. Ya tsaya kofar gidan mu jikin sa sanyaye, ya kifa kanshi a sitiyarin mota. Na bude kofar motar tare da cewa sai anjima. Ya zaro wayata daga aljihunsa na baya ya mika minn ni na manta ma ina da wata waya, na karba jiki babu kwari na shiga gidan sukuku, nayi sallolina na zauna cikin tagumi , Allah nake roko ya zaba min mafi alkhairi. Misalin karfe takwas suka shigo shi da Shadad, yau har cikin dakina ya shigo, Shadad ya zauna a jikina shi kuma ya tsaya da leda a hannun shi. Ya ajiye min ledar. "Kici wani abu zan kira wayarki anjima. Gobe da safe zan wuce kila na biyo." Sai naji har raina bana son tafiyar tashi, sai dai bani da izinin hana shi. Na bude ledar kaza ce da madara mai sanyi, rabona da cin kaza tun lokacin Hajiya Hindu Likita, Allah ka yafe mata har in gushe bazan daina mata addu'a ba. Na ci na koshi, Shadad dama da guntun baccin shi ya shigo, yana zuwa yayi bacci. Nayi shafa'I da wuturi na kwanta. Sam bana jin bacci zuciyata ce ma take ta azazzala ta tare da fada min bazata juri Abubakar ya subuce mata ba gara ma in san abin yi. Na kosa ya kira ni, sai gurin sha daya da rabi lokacin na debe tsammani da kiran sai ga wayata na ruri. Na daga da sauri don marmarin jin muryarshi. A tare muka yi sallama, sannan muka kara hada baki gurin amsawa. Ya ce kin fara bacci ne? Na ce a'a" ya ce ki fada min tsakani da Allah ki kasa bacci saboda menene?" Na ce bazan iya ce maka ga dalili ba." Yayi shiru, can yace sona ne ya hanaki bacci kamar yanda sonki ya hana ni. Muna son juna mezai hana ki bani hadin kai muyi aure? Duk abinda kike so zan maki Don Allah ki tainake ni Hafsat." Muryata can kasa, jikina yayi lukwi nayi juyi zuwa ruf da ciki. Sannan na ce in nace ba jin wani abu mai kama da so a tare dakai, hakika nayi karya. Sai dai in na saki jiki zuciyata tazame da sonka, a karshe zan sha wahala, duk ranar da kasan who I am. Ya ce ki fada min komai, bazan taba gudar ki ba, don kin sami wata matsala ko kina da matsala da iyayenki zan fahimce ki sosai. Na ce zan fi so in kabar batun aurena, ya ce in yi yaya da sonki to?" Na ce hakuri mana, nima hakuri zanyi." Ya ce amma da gaske kina sona? In na duba wasu abubuwa zan iya yarda cewa ina sonka, kai kadai ne kasa ni in manta alkawarin da na dauka na cin mutuncin duk wani namiji da yayi min kallo fiye da daya. Kaine kake sani inyi abinda ban niya ba. Ya ce har kin sani naji sanyi a zuciyata, don Allah ki taimaka muyi aure. Gidan mu an matsa min in fito da mata, yanzun haka an bani lokaci." Na ce dama baka da mata? Ya ce ina da mata, na ce to bazan taba auren ka ba don na san wata rana zata yi min gori. Da saure ya ce bani da mata wasa nake maki. Na ce duk da haka kayi auren ka ni bazan iya aurar ka ba, hirar mu daga jayayya sai zance soyayya, tare da magiya. Abin al'ajabi sai na jiyo kiran sallar farko. Na ce, "Sadeek kaji abinda naji kuwa? Ya ce me? Na ce, kiran Sallah fa." Ya dubi agogo yanzun nan fa muka fara magana, na ce shi ne nima na gani, to zaka shigo kafin ka tafi? Ya ce bazan shigo ba, kuma bazan sake zuwa kano ba tunda kince baza ki aure ni ba, kin kuma ki fada min dalili. Bance komai ba har lokacin da yace min sai wata rana, ya kuma kashe wayar shi.